RABI'ATU

720 34 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
      *RABI'ATU*

STORY&WRITTEN BY BILLYLOSH❤



® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com



Follow me on wattpad @ Billylosh1



*HAPPY BIRTHDAY SULTAN AGE WIT GRACE🎂🍾🎂🍾🎂🎉🛍🛍🛍🎁🎈*

     _*AUNTY SIS💞*_



9⃣

"Allah yasa"inji Inna. Nan suka ta hirar su har lokacin sallah yayi sannan suka tashi domin gabatarwa suna idarwa Inna ta tashi ta bud'e wardrobe d'inta ta ciro wasu had'add'un lace guda biyar atamfofi guda uku da mayafai uku sannan ta juyo tace "Rabi'a ya kamata nima na d'inka wad'annan kayan tunda na kwana biyu banyi d'inki ba ko"?  "Eh  gaskiya kam inna ga wasu sark'oki ma ki zab'a"  "kai Raba'a kinaji da Innar ki toh mik'o su na gani". Wasu jeweries ta d'auko masu kyau  Inna ta zab'a kala uku ba tare da sunsan Gold bane.

   "Yanzu Rabi'a sai ki bani kud'in d'inki da na siyan takalmi" toh tace sannan ta nufi bedside drower ta d'auko  ragowar kud'in da aka ciro mata ta fara irgawa, da sauri Inna ta fizge kud'in tace yaza ayi ki irga kuma haba 'yarlele ta, ay kud'in da ky'ar  ma su isheni.
     "Yawwa bama wannan ba so nake ki k'ara min wasu kud'ad'en akan wanchan da kika bayar saboda wannan ginin da muka fara nakeso a cigaba saboda a gama da wuri.
   Washe rinannun hakoranta Rabi'a tayi sannan tace "kinyi gaskiya Inna,yanzu bari in d'auki mayafi na sai muje na baki ko"? Inna ce tace "sannu 'yar albarka muje saboda kar yamma tayimin kinsan samun mota akwai wuya, ya kamata ma ki siyamin mota" Rabi'a ta ce kedai bari nan bada dad'ewa ba".

     Nan suka ta hirar su sannan suka fito compound. "Raba'a ina direban"? "Direba kuma"? "Eh mana, toh a k'afa zamuje"?  "Nifa Inna kinsani sarai bana fita da wani gardi na gwammace in fita in hau Taxi"  Inna tace "shashasha kawai. kina matar mai kud'i sannan ki ringa raina kanki kina fita titi ki tsari motar haya"? Ko me ta tuna ta juyo tace wa Rabi'a "kinyi daidai karki yarda direba yana fita dake kinji ni ko" tohm.

Divya tana zaune sai ga mijinta Abdulmalik tare da Dr.Halima wacce tayi mishi rakiya da sauri ta taso tayi hugging dinshi tare ta fara wani sabon kukan tana why why why all this? Rarrashinta ya shiga yi ba tare da yasan kukan menene ba domin Dr. Bata mishi bayanin komai ba.
     fita tayi ta basu wuri, zaunar da Divya yayi a gefen gadon da Zarah ke kwance ya ce calm down please and tell what's the crying about, and this little baby? Shiru tayi tare da fuskantarshi tace Habiby Zarah ce  wannan, yace "Zarah? Zarah kuma?"  "Eh Habiby Zarah" "toh me ya sameta"? Nan take gaya mishi komai da ke tattare da ita, " Lahau'la walak'uwata illa billahil'alimun azim", maganganu ya farayi ba tare da yasan abubuwan da ke fitowa daga bakin shi ba, "wannan wacce irin uwa ce anya Zarah 'yar Rabi'a ce? ina mahaifinta? Ko bata da uba ne"?
 
    "Wannan wacce irin azaba ce take azabtar da Zarah wannan wani irin Jahilci ne anya Divya bazan kai k'arar Rabi'a ba kuwa" ?

      
        Divya da kuka ya ci karfin ta tace "a'a Habiby baza'ayi haka ba ka barta duniya ce taza koya mata hankali in Sha Allah, Allah bazai barta ba ta tuna 'ya'ya fa amana ce Allah ya bamu kuma Allah ranar gobe k'iyama zai tambaye mu akan amanar daya bamu it will be too late for her to cry".

     Kudin masu yawa Rabi'a ta cire ta bawa Inna sannan ta dawo gida.

   Missed calls din Abdulra'uf babu adadi a wayar Rabi'a amma sam tak'i bi ta kansu ballantana tayi tunanin kira. A haka suka d'inga  rayuwa ba tare da chanji ba Divya ita ke rainon Zarah a asibiti, har suka d'iba sati uku Divya duk tayi bak'i ga rama kullum cikin kuka takeyi.
     Malam sani kwana biyar ya d'iba yana zuwa asibiti karshe ma ce mishi sukayi sun sallamesu yana dawowa gida ya sanar da Abdulra'uf  a waya ba k'aramin dad'i yaji ba duk da halin kunci da yake ciki na rashin daukar wayar da Rabi'a batayi, yayi godiya yace in Sha Allah shima nan da 2weeks zai dawo.

BILKISU ARDO CE❤


❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now