RABI'ATU

945 32 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤


® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

Follow me on wattpad @ Billylosh1









   *AUNTY SIS💞*


1⃣4⃣➡1⃣6⃣



       Jirgin su Abdoulra'uf ne ya fara hayak'i kafin su ankara saman ya fara ci da wuta duk inda hankalin kowa yake ya tashi masu addu'a sunayi masu ihu suna yi wuta sai k'aruwa yake, su kansu pilots din hankalin su a tashe yake saboda sun kasa controlling jirgin basu ankara ba suka ga........

  
   Dr. Halima Hankalin ta atashe  tabar gidan  Rabi'a bata zarce ko'ina ba sai katafaren gidan ta.

    Tana shiga bedroom dinta ta nufa ta ajiye handbag dinta da veil sannan ta kwanta akan sofa bed dinta tare da d'ora hannun ta akai tana tunani kalakala acikin ranta, dama akwai mutane irin Rabi'a acikin duniyar nan 'ya ba *'YAR ZINA* (littafin maryam pinky) ba amma ake gudunta 'yar sunnah, wannan wacce irin rayuwa ce haka.

    Kwalla ce ta taru a idonta, mikewa tayi tare da sharce kwallar sannan ta shiga toilet ta dauro Alwala ta tada sallar la'asar....

   Rabi'a kuwa tana komawa parlour sai taji horn din mota dasauri ta lek'o, Aww ashe wata yayi( duk wata ake juye mata kayan abinci da duk wani abin buk'ata everything is available but its of no use, gwangwanayen madarar Zarah kuwa kusa guda 20 ake kawo wa amma ba'a taba bata ba ). Bata bari drivern motan ya fito ba tazo inda yake tace mishi " ka juya da motar ka tafi kauyen innata ka kai mata kayan dukka" sake baki yayi galala yana kallonta ba tare da yace komai, tace " kai bakaji mai nace ba ne?" D'ago kai yayi yace "toh Hajiya ba matsala" "ah ka ce ma da matsala mana" reverse yayi da motar sannan ya dauki hanyar kauyen *NAMORA*.

   Har ta juya zata koma parlour ta sai ga malam sani ya gaisheta cikin girmamawa duk da a haife ya haife ta dan sai dai tayi sa'a da yar'sa ta uku dan bata wuce shekaru 23 ba a duniya  yace "Hajiya ya ko jikin Zarah?" tabe baki tayi hade da yatsina fuska tace "da sauki" bata jira mai zai ce ba taja sod'add'en silifas dinta da tazo dashi daga kauye tashige parlour ta barshi a gurin..

   Dr. Halima tana idarwa ta sauko main parlour ta zauna tare da kiran baba delu, da sauri ta fito tare da rankwafa wa ta ce " gani hajiya" Dr. Halima juyowa tayi tace "haba baba delu me kikeyi haka? Dan Allah daga ah daga kibar rankwafa min, ki kawomin abinci na"  toh tace sannan ta fice, batafi 2min ba ta kawo mata abincin ta bubbude mata sannan ta tashi .

    Saukowa tayi k'asa ta fara cin abinci. Ci takeyi amma da sanyin jiki kamar bataso saboda damuwar makomar Zarah, bata wani ci da yawa ba ta kira aka kwashe kwanukan.

   Kukan zarah ta faraji ba tare da tasan tana dakin k'asa ba, da sauri ta mike ta dauko ta tana jijjigata har tayi shiru. Cereals aka hada mata ta fara sha, da sauri-da sauri take sha tashanye tasa kuka hakan yasa aka k'ara hado mata wani tas ta shanye sannan ta koma barci, ta tafi da ita dakinta ta kwantar da ita akan gado tana shafar kanta tare da mata addu'a sannan ta shiga study room dinta dake cikin bedroom din  tana karatu ko me ta tuno dasauri naga ta tashi tafito ta dauki veil da bag ta fito main parlour baba delu tashiga kira da sauri ta fito tace "gani hajiya", "baba Dan Allah ga Zarah nan acikin d'aki na tana barci ki ringa dubata karta tashi tayi ta kuka ni zan fita "  ba tareda ta jira me zatace ba ta wuce saboda saurin da takeyi.

   Kofar gidan Rabi'a naga tayi parking, fitowa tayi cikin nutsuwa ta buga gate sai ga  malam habu mai gadi ya bude yana ganin itace ya fito waje tare da babbake wa a kofar saboda kashedin da Rabi'a tayi mishi d'azu yace "Baiwar Allah lafia?" Dr. Halima taja numfashi sannan tace "Dan Allah idan bazaka damuba inason kabani  lokacin ka kadan saboda in maka wasu y'an tambayoyi" gam ya rike kofar gidan sannan yace "ina jinki"  tace "toh mud'an k'arasa gurin mota" kallon banyarda dake ba yayi mata murmushi tayi irin nasu na manyan mata tace " toh ba komai naga kamar kanaji tsoro"   gyara tsayuwa yayi sannan yace "ashe kingane" nan  tasoma magana  "shin  aina iyayen Rabi'atu suke da zama? Shin mijinta yana da rai ko ya rasu? in yanada rai yana ina? Shin mijin yanada y'an uwa ko bashida? Y'ay'an Rabi'atu nawa? " jin tambayoyin yayi kamar saukar aradu.......


Jirgin su Abdulra'uf ne ya farayin k'asa at thesame time gudunsa bai ragu ba, Abdulra'uf wanda tun lokacin da hakan ya fara faruwa ya rufe ido yanata karanto kalmar shahada ba tare da tsoro ya bayyana a fuskar shi ba , wasu kuwa tuntuni suka suma,





BILKISU ARDO CE❤



❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now