RABI'ATU

494 20 0
                                    

❤💕❤💕❤💕❤
       *RABI'ATU*



STORY & WRITTEN BY BILLYLOSH❤






® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


(ฬє ๔๏ภ't ๏ภly єภtєгtคเภ คภ๔ є๔ยςคtє,๒ยt ฬє t๏ยςђ tђє ђєคгt ❤๏モ гєค๔єг'ร 📚)_





#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/
PML_-Writers-
FANS-4525671123035
#http://maryamsbello.blogspot.com




Follow me on wattpad @ Billylosh1




*AUNTY SIS💞*




2⃣4⃣➡2⃣6⃣





     Within 10mins jirgin su ya d'aga zuwa Abuja, daga nan suka wuce gidan su dake maitama sule mai gadi ya bud'e musu gate suka shiga

   "WOW"

   Shine abinda Dr. Halima ta furta da ganin 3D building tsararre wanda yasha adon flowers wanda ya k'ara k'ayatar da gidan. Direct main door suka nufa Abdoulmalik ya danna password k'ofar ta bud'e suka shige.


Relaxing sukayi akan kujera Divya ta musu ordering abinci, kowa ya tashi yayi wanka yayi sallah sannan suka fito suka ci abinci suna gamawa suka d'an tab'a hira la'asar nayi sukayi sallah suka fito raka Dr. Halima airport saboda zuwa magrib jirginsu zai d'aga zuwa Eygpt, suna shiga Abduolra'uf yana fitowa da luggages dinsa mistakely Abdoulra'uf ya bige handbag din Divya ya juyo yace

    "Sorry ma"

Tare da zubawa Zarah ido saboda yanda tayi mishi kyau Divya tace

    "Bakomai"

Sannan suka k'arasa ciki, jirginsu na tashi suka juyo gidansu na maitama sule......

    Abdoulra'uf Hotel yaje ya kama a Abuja zuwa gobe, yana shiga yayi wanka yayi Alwala yayi sallah aka kawo mishi dinner da yake ba gwanin cin abinci bane sosae Fruit cocktail ne sai pineapple milkshake.      

      Yana gama sha yayi sallah isha sannan ya dauki wayarsa ya fara dialing number uwar gayya Mrs.Abdoulrauf wato Rabi'atu, yayi harya kat'se bata answers ba.

B'angaren Rabi'a kuwa tana kwance ta hangame baki tana  bacci hankalinta k'wance wayarta kuwa tana cikin toilet ta barta tunkafin ta k'wanta data shiga da wayar ta manta bata d'auko taba. Abdoulra'uf harya gaji da kira ya hak'ura.

   Kwanciya yayi akan gado yayi rigingine yana kallon sama da tunani iri-iri aranshi yace

    "bayan shekara 2 yau na dawo,  wani irin tarba matata Rabi'a zatayimin ya zanga 'yata, Rabi'a tayi missing d'ina?"

   " Ko dayake ai dama ba so na take ba babu wani missing d'ina dazatayi, dukda ba santa nakeyi ba amma nayi missing uwar 'yata Zarah i feel like flying just to see my cutest Daughter Zarah ohhh i know she resemble me".......


  Da irin wannan taught d'in  barci b'arawo ya sace shi.
  Asubar fari yayi sallah yayi wanka. aka kawo mishi breakfast yaci sannan ya fito saboda 8am flight d'inshi. Rabi'a kuwa karfe 8am as usual ta tashi tayi sallah kamar kar taje makaranta saboda Zazzabin data tashi dashi sai wuraren tara da 'yan mintuna sannan ta isa makaranta...

    Malam Habu mai gad'i na gani yanata firfito da  kayayyakinsa yana had'asu a Ghana must go ya shirya tsaf sannan ya fito daga d'akinshi ya rufe yasa kwad'o ya juyo yace

"Toh malam sani Allah ya k'ara hakurin zama"

   Malam sani da duk abun bai yi mishi dad'i ba tun d'azu yake bashi hakuri amma fir yak'i hak'ura hakan yasa ya k'yaleshi yana binshi da ido.

  Bud'e k'aramar kofar sa keda wuya sai ya hangi Dr. Abdoulra'uf murmushi yayi mishi tare da k'arasa bude mishi k'ofar gidan ya shigo kayayyakinsa suka shigo dasu har k'asa suka t'sugunna suka gaishe shi ya amsa tare da yi musu hani cewa su daina t'sugunna mishi.
   kallon Mal.Habu yayi ganinshi da jaka yace

 
    "lafia naganka da kaya nik'inik'i? Ko wani abune ya samu iyalinka"?

  Shiru malam Habu yayi sai malam sani ne yace

    "Ranka ya dade dama ya bar aiki ne jiya ya gayawa Hajiya tace yayi ta tafiya".

  D'aga kai yayi ya kalli gidan ya ganshi a bushe ciyawa sun tsitsiro flowers basa samun kula a gyara su. yace

    "Kayi hakuri zuwa anjima zamuyi magana"

Nan yayi gaba suna biye da kayansa yana bud'e k'ofar parlour wani gigitaccen wari ya bugesa saida yayi baya yana haki, ganin akwai mutane a bayanshi karsu d'auka wani abune (tunda shi mutum ne mai boye sirrinsa da kuma damuwarsa )

Yace musu "ku bar kayan anan zan shiga dasu ciki"

   Kallon juna sukayi tare da ajiye kayan suka juya shiga yayi da bismillah har t'sakiyar parlour yana kallon sama yana duk yayi wa saman rumfa ga k'ananan k'wari a mak'ale a jiki ga kuma gizogizo duk yayi sak'a.  ba tare da ya lura ba yayi tuntube da k'wanuka nan kallo ya koma k'asa idanuwa ya zazzaro ganin tuk'wane akan white leather seat din dake zagayi da parlour kujerun duk sunyi bak'i labulayen parlour da suka kasance farare suma sun koma bak'i saboda  idan Rabi'a  taci abinci ajiki take gogewa, carpets din kuwa i don't have to explain you already know it has turn to coffee brown.

   D'akin Rabi'a ya bude saida ya gwammace da bai bud'e ba saboda azabar wari. Wanki yaci karo dashi kashi-kashi gadon nan kuwa duk ya cika da kaya ga tarkacen tsummokaranta baza ka taba gane d'akin ba saboda ada maroon&orange ne colour d'akin yanzu kuwa is something else, nan ya zarce toilet lahaula wala k'uwata illabillahil aleemun azeem.................

  









*BILKISU ARDO CE❤*




❤💕❤💕❤💕❤

RABI'ATUWhere stories live. Discover now