ZR-01

9.8K 613 41
                                    


©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye

This book is  free from beginning to end.

***    ***     ***

A hankali ya bude idonsa sai kuma ya maida idon ya rufe har sai da wayar ta sake ringing. Wannan karon yayi saurin bude idon ya sauka daga kan gadon yana kallon kyakkyawar mace dake gefensa tana bachi, hannu ya kai kamar zai shafa fuskarta sai kuma ya fasa sakamakon wayarsa da tai ringing. Kallon kwayar yai kamin yabkai hannu ya dauka.

“Sadam kai kadai muke jira fa”

“On my way Dad”

Ya fada yana shafa sumar kansa, sannan ya aje wayar yana hamma, da alama bachin be isashe ba a haka ya tashi ya nufi bathroom, a gaggauce yai wanka ya fito sanye da bathrobe ya nufi gaban madubi. Cikin kankan lokaci ya shirya ya feshe jikinsa da expensive perfume, wani bangare ya nufa na bedroom, hannu ya kai ya danna wani dan karamin maballi dake gefensa gurin sai ga wata katuwar kofa mai cushion ta rabu biyu, ciki ya shiga ya sai gashi cikin wani dan madaidacin dakin mai dauke da kayan ado na zama kama daga kan tufafi, agogo, takalma, hulluna, glasses and so on.

Cikin kananna kaya ya shirya dark blue T-shirt and white jean, takalmin dake kafarsa ma dark blue ne kamar yadda facing cap dinsa take, fito yai daga dakin yana kokarin saka ma hannunsa agogon, gaban madubi ya zo ya tsaya yana kallon kansa. He look so cute and adorable, so cool and calm. Tufafin jikinsa sun karbeshi sosai. A cikin madubin yake kallon mace data taso daure da zanen gado ta nufo inda yake tsaye.

“Don't touch me”

Ya fursa fuskarsa a hade. Ko da wasa bata tai gigin kai hannunta ta taba shi ba, sai kawai ta bata fuska. Barin gaban madubi yai ya koma dan karamin dakin sai gashi ya fito rike da da bandir din yan dari dubu ya jefa mata, sannan ya juya ya danna maballin dazun dakin ya rufe. Gaban madubi yaje ya dauki makullinsa da atm dinsa ya saka aljihu.

“Zan shigo da Friends dina anjima karki yarda na tararda ke a cikin dakin nan”

Yana fadar hakan ya nufi kofar fita sai kamshin turare yake, gaban tinting windows ya nufa ya kai hannu ya daga curtains din yana hango wani dan karamin gida, hankali ya maida sosai yana kallon wata matashiyar yarinya da ke zaune saman kujerar tsakar gida irin ta mata, hannunta rike da bulala ta hade rai sosai tana kallon kananan yara dake gabanta. Baya iya jiyo abunda take cewa amman ga dukan alamu horo take musu, hannayensu suka taro tana dukansu a hannun daya bayan daya, mahaifiyarta ce ta fito daga dakin dake kusa da su rike da av ta zabga mata a gadon baya, wani irin tsalle ta daka ta tashi tsaye ta shige dakin da gudu tana dariya.
Murmushi yai ya saki curtains ya juyo fuskarsa da annuri ya nufi wani dakin sai gashi ya fito rike da wata yar karamar jaka mai dauke da kayan wasan tennis.
Main door ya nufa ya bude ya fito daga falon, da dan sauri yake taka katon stairs din yana saukowa kasa. Tun kamin ya karaso ya danna key din hannunsa bakar motar mai bakin gilashi tai tsuwa, front seat ya fara budewa ya saka jakar sannan ya zagayo ya shiga driver side ya tashi motar.

***  ****  ***

Tana ta murza gurin da Umma tai mata bulalar kamar tai kuka.

“Gaskiya Umma kina min cin fuska haka kawai a gaban yara za ki dake ni”

“Ai shine daidai da ke, haka kawai dan zalunci za ki tara yara cikin rana kina musu hoto, kamar haihuwarsu ki kai”

Ta kalli wanda ya fada mata haka ta murguda masa baki.

“Wai kai Ya Nabeel ba Abbah yace ka daina shiga sabbagata ba, bari ya dawo Wallahi sai na fada masa”

“Mtsssss”

Yaja tsaki tare da tashi hannunsa rike da rike da tecno spark 3 ya fice. Ta yi kwafa

“Ba Nabeel ba Nabila”

Ta fada tana kara murguda baki kamar yana gabanta, ta sake murza gurin da Umma tai mata bulalar tana bata fuska kamar wata karamar yarinya.

“Zinneera”

“Na'am”

Ta amsa kiran da Umma tai mata da fushi ita a ala dole an daketa.

“Zo ga wayarki tana ringing”

Da gudu ta fita daga dakin ta nufi inda ta bar wayar ta dauka tana rawa kamar ba ita ce take fushi ba.

“Assalamu Alaikum”

Ya kara wayar a kunne tare da sallama sannan ta shige daki. Saman gado ta fada tana murmushi.

“Na yi marmarin muryar nan, yau duk ban ji Sahibata ba”

Ta dan bata rai.

“Bana ce ka daina ce min Sahiba ba”

Yayi dariya.

“Yi hakuri Sahiba ba zan kara ba”

“Wallahi zan kashe wayar”

“Yi hakuri na daina, yanzu dai fada min me da me Babyna tai yau?”

Ta yi murmushi tana mai jin sonsa har cikin zuciyarta.

“Taje makaranta, bayan ta dawo ta ci abinci sannan tai wanke wanke, sai kuma ta dawo tsakar gida tana yi ma yara horo”

“Au ba zaki daina wahalar da yaran mama ba ko?”

“Ee din, ai basa jin magana”

“Ke jin magana kike yi? Shiyasa kullum Nabeel yake zaneki”

“Ai Abbah yace duk ya sake shiga saggata sai ya sa kafar wando daya da shi”

“Amman Abbah be kyauta ba, ai ke sai da horo”

“Au haka ma za ka ma zaka ce?”

“Yi hakuri Babyna, fada min me kike son na zo miki da shi anjima”

“Zuciyarka, ka cireta daga kirjinka ka saka ta a hannunka ka zo min da ita yau ita na ke so”

“Consider it done, I love you”

“I love you more Little Boy”

“What...!”

Ya amsa da karfi sai tai saurin kashe wayar tana dariya....

____________________________________________

How are about this journey?
😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍😍

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now