49

1.6K 232 11
                                    

BAYAN KWANA BIYU.

Babu asibitin da ke cikin garin Sokoto ta manyan mutane Sadam be kai Zinneera ba but the same result yake badawa cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba. Hakan yasa hankalin kowa ya tashi ciki kuwa har na Nabeel da Abbah abunda kowa yake fada shine azubar da cikin idan ta samu lafiya sai ta sake dauka wani amman ta ki yarda.

“Amman Zinneera ba zan iya hakurin rashinki ba, kuma za mu iya samun wata haihuwa idan kin samu lafiya”

Sadam ya fada yana rike da hannunta yayinda suke cikin mota zauna a kofar gidansu misalin karfe goma da rabi na dare.

“Allah shine mai kashewa ya raya Sadam idan ya ga dama zai iya raya ni, idan kuma ya ga dama ya ga dama zai iya kasheni ba tare da komai ba ma, ya kamata kai imani da hakan”

“Na yi imani amman ina ta jin tsoro i wanna loose you”

Ya fada yana kai hannunsa a kirjinsa.

“Likitan sun fada min cewar Matukar zan kwantar da hankali hawan jini ba zai kamani ba, idan kuma be kama ni ba, zan a iya min theater cikin sauki a cire abunda yake cikina lafiya kuma ni na tashi lafiya kalau, iyakar kokarin da nake na kwanciyar hankalina ne, ba ni da wata damuwa a yanzu wancce ta wuce kai kuma ina tare da kai to mi xai tashi hankalina a yanzu?”

Yai mata murmushi yana kara matse hannunsa a cikin na shi cike da kaunarta.

“Mu shiga ciki kar Abbah yai ta jiranmu”

Ta bude motar kamar yadda ya bude ya fita shima suka shiga cikin gidan tare. Aleeya ce ta fara yi amsa musu sallama tana dauke kai daga kallon Sadam wanda ke sanye da farar shadda sai kyalli take. Jiki na rawa Umma ta shimfida musu tabarma tana musu sannu da zuwa. A saman tabarma suka zauna Zinneera ta fara gaisheta sannan Sadam ya biyo da tashi gaisuwar bayan ta Zinneera Umma ta tashi da kanta ta kawo musu ruwa duk da tasan Sadam ba sha zai yi, Zinneera ta dauki ruwan ta sha ganin hakan yasa Sadam shi ma ya sha kadan yana kallon Abbah wanda ya fito daga daki rike da touch light kasancewar babu wutar nepa a lokacin.

“Sannunku da zuwa”

“Yauwa Abbah ya gidan?”

“Lafiya kalau ya aiki”

“Alhamdulillah, Abbah Daddy ya turo mu ni da Zinneera ya ce mu zo mu nemi yafiyarka akan abunda ya faru”

Sadam ya fada kamar yadda Daddy ya umarce shi duk da kasancewar Daddy san Abbah baya fushi da Zinneera har yanzu amman da kyau ta nemi yafiyarsa tunda ubanta ne. Abbah yai murmushi yana gyara zamansa.

“Babu komai ai ya wuce, daman ba saboda komai na ke fushi da Zinneera ba sai dan mutuwar auren nan kuma tunda an shirya to ni miye nawana fushi kuma? Kuma daman can na dauka hakanan kawai ta gudu ta je gurin Hajiya Karima shiyasa raina ya kara baci, amman jin cewar ta gudu ne saboda kar Safiya ta zubar mata da ciki ni sai ta burgeni ma kuma tabbatar tana da hankali da tunani”

“Haka ne daman can Abbah ai Zinneera tana da hankali kawai dai wani lokacin aikin zuciya ne”

Umma ta karbi zancen.

“Wallahi kuwa Zuciya mai kai mutum ga halaka”

Sadam ya tashi yana ajewa Abbah kudi mai yawa ya ce ya siye goro.

“Ni zan jirata a mota sai ku kara gaisawa, In-Sha-Allah ranar Saturday zata zo nan ta wuni na san ta yi marmarin gida sosai”

“Haka ne an gode sosai da hidima Allah kara rufa asiri”

Umma ta fada baki har kunne. Sai da ya fice sannan Zinneera ta kalli Abbah ta ce.

“Dan Allah Abbah ka yafe min abunda ya faru, In-Sha-Allah hakan ba zai sake faruwa ba”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now