33

1.7K 256 39
                                    

Bayan awa daya da yan mintuna ya soma motsawa, kansa yaji yayi masa mugun nauyi kamar an dora masa dutse a kai da zugi, daker ya bude idonsa sai Ummi ta leki fuskarsa da sauri.

“Sannu”

Dishedishe ya fara gani kamin ya ganta daidai, ganin bakuwar fuska yasa shi kura nata ido yana kallonta, can kuma ya dauke idon yana kallon ceiling, sai kuma ya sake maida dubansa gurin hannunsa dake da bandeji kokarin tuna abunda ya faru yake, yasan ya fito daga gida rike da waya yana neman inda zaije saboda bacin rai da damuwa, sai kawai motar data shigo kwanar da gudu ta kadeshi.

“Ni na kade ka ni ce, amman ba da gangan ba, kuma yaje kiran mamanka wayar ta mutu”

Ta nuna kanta.

“Ina wayar take?”

“Gata nan a jakata, naje gida na kwana da safe na zo na tararda wata yarinya tana kuka ban san ko wacece ba”

“Wace yarinya?”

“Nima ban santa ba, fara ce haka mai tsaye bata da jiki sosai”

Shiru yai yana tunani.

“Wa kike kira da wayata?”

“Ban kira kowa ba amman dai lokacin dana kadeka naji kana kiran sunan Zinneera waccece ita?”

“Ina ruwanki bani wayata”

Ya fada kamar da fada.

“Wayarka ta mutu ba charji, kuma idan baka fada min wacece ita ba, ba zan fada maka abunda yarinyar nan tace ba kuma ba zan baka wayar ba”

Wani kallo ya watsa mata.

“Me tace maye sunanta?”

“Ba zan fada ba sai ka fada min ko wacece Zinneera”

“Daga ganinki baki da hankali shiyasa kika kadeni”

“Eh daman ai bana da hankali, mahaukaci yana saurin gane dan'uwansa shiyasa ka gane cewar ba ni da hankali”

Ta fada tana dora kafa daya saman daya.

“Ki bani wayata nace miki!”

A tsawace.

“Ba zan bayar ba sai ka fada min ko wacece ita, matarka ce? Ko kanwarka ce? Ko kuma mahaifiyarka ce? Da kake kiran sunanta?”

Tsayawa yai kallonta ba tai kamada mahaukata ba balle yace bata da hankali amman abunda take kamar ba na masu hankali ba. Ya zata kade shi jiya yau kuma yana cikin wannan halin tace sai ya fada mata ko wacece Zinneera, ina ruwanta da rayuwarsa?
 
“Mama ta zan kira ko baki san darajar mahaifiya ba?”

Ta kalleshi a sanyaye ta ce

“na sani”

Sai ta saka hannunta a jaka ta dauko wayarta ta mika masa.

“Wayarka ba charji amman zaka iya kiranta da wayata”

Ya dade yana kallon wayar sannan ya karba ya saka number Mama ya kirata, ya sanar da ita ya mayar mata da wayarta. Be sake kallon inda take ba itama bata sake ce masa komai ba. Ba ayi minti talatin ba sai ga Mama ta sake kiran wayar tana neman inda suke, wannan karon Ummi ce tai mata kwatancen, sai gata ta shigo dakin hankalinta a tashe. Da sauri Ummi ta mike tsaye ta bata kujerar.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Sadiq garin ya haka ya faru”

“Ni ce na kade shi amman ba da gangan ba”

Ummi ta amsa tana matsa hannayenta.

“Allah ne ya kawo, kaddarorine kin san ba a wuce musu”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now