ZR-09

2.8K 328 39
                                    

A jikin kofar shiga part din Daddy ya tsaya ya daidaita natsuwarsa, sannan yai knocking kofar. Yayi tsayuwar minti biyar zuwa uku kamin kofar ta bude masa. Sai da ya jira cover shoes din da ke kafarsa sannan ya karasa cikin falon da sallama.

“Wa'alaikussalam”

Daddy ya amsa masa ba tare daya dago ya kalleshi, hannunsa rike da kofin lemu, dayan hannunsa nata aikin bude magazine din dake saman center table idanuwansa sanye da farin gilashi.
Kusa da shi Sadam ya zauna a yadda suka jera sai ka rantse wa da kane ne, sam ba zaka ce Daddy yana da babban da kamar Sadam ba saboda kyaun jikinsa da kuma jindadin da yake ciki. Kamaninsa ne kawai suka banbanta da na Daddy domin fuskar Mommy ce shimfide a fuskar Sadam babu inda ya ragota da komai.

“Daddy barka da rana”

Ya fada cikin tsantsar ladabi yana kai idonsa gurin magazine din da Daddy ke kallo. Sai a lokacin Daddy ya dago ya kalleshi fuskarsa dauke da murmushi.

“Barka dai Mr Kazaure”

Sadam yai murmushin daya bayyana hakoransa jin Daddy ya kirashi da family name dinsu. Daddy ya dauki magazine din dake gabansa ya mika masa. *Kazaure Limitless company*  Shine rubuce a fuskar magazine din cikin manyan harufa, sai kuma hoton kamfani da akai ado da shi a gaban magazine din, daga can kasa kuma an raba hotunan kashi hudu dayan hoton ya kumshi abubuwan da suke cikin kamfanin ne dayan kuma hoton Sadam ne an rubuta Mr Kazaure, hoto na biyu da na uku kuma suna dauke da abubuwan da kamfanin yake siyarwa ne. Wadanda suka hada da sarkar gol da kuma yan kunne diamond. Cike da mamaki ya kalli  Daddy.

“What this?”

“Open and see”

A take ya bude magazine din ya soma dubawa, yana cikin dubawa Daddy ya ce

“Kamfaninka ne da zamu bude next month”

Sadam ya lumshe ido alamar be jidadi ba.

“Daddy maganar kamfanin dai...? I thought mun gama maganar nan tun muna waje”

“Not yet, ba zan hana aikin gwanati ba kamar yadda kake so, amman for now zaka kula da wannan kamfanin ne kamin aikin ya zo, and ko bayan aikin ya fito ba zaka bar kamfanin ba”

“Dad please...”

“No Sadam na gina reshen kamfanin nan ne a nan Sokoto saboda kai, so ba zaka bani kunya ba”

“Yes Dad.... Sure.. ”

Ya aje magazine din tare da tashi yana sauke ajiyar zuciya, yanayinsa na nuna rashin jindadin da yake ciki, zumudin daya zo da shi na zancen zuwa gidansu Zinneera sai ya nemi zumudin ya rasa, maganar bude kanfanin nan ta shafe komai.
Cikin rashin walwala da sakewa ya dawo part din Mommy, be sameta a falo ba, kai tsaye ya wuce dakinta, tana zaune saman kasaitaccen royal bed dinta Suraiya na zaune kusa da ita suna kyalkyalar dariya, da alama fira take ma Mommy,  kallo daya Mommy tai masa ta karanci damuwa a tare da shi.

“Favorite miya faru?”

Zaunawa yai saman kujerar dake facing din gadonta yana kara bayyana mata damuwarsa tare da shafa kansa. Suraiya ta tashi ta koma kusa da dan'uwanta ta zauna tana kallon yanayinsa.

“Mommy's Favorite miya faru?”

Sai da ya busar da iskar bakinsa sannan ya kalli Mahaifiyarsa wacce hankalinta ya gama tashi ganin danta cikin damuwa.

“Mommy na ɗauka mun gama maganar kamfanin nan tun ina waje, and now Daddy ya dawo da issues din, wai by next week za'a bude kamfani kuma ni zai barwa ragamar imagining...”

Lumshe ido Mommy tai tana murmushin tare da sauke ajiyar zuciya jin dalilin bacin rai mai sauki ne, Suraiya kuma ya rumgume shi tana ihu.

“O My god, Mommy's Favorite so that's mean Daddy kai ya ginawa kamfanin nan congratulations”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now