ZR-05

2.6K 324 36
                                    

Tun da tai kwaliyar take ta faman fifita a fuskarta, wai kar tai gumi duk iskan fankar dake dakin be wadatar da ita ba. Ita dai kar tai gumi kwalliyarta ta goge Abubakar (Sadiq) be zo ya gani ba, ta yi jiran kiran wayarsa har ta gaji be kira ba, Nabeel sai dariya yake mata shi da Aleeya. Ita kuma ta cika kamar ta fashe dan takaici, baro musu dakin tai ta nufo gurin icen guava ta zauna ta soma kiran Abubakar a wayarta ganin har tara na kokarin wuce bata be zo ba. Ringing daya ya dauka.

"Hello Baby"

"Mai sunan Baba miya han ka zuwa yau?"

"Wallahi Baby ba ni da lafiya, Fever ya rufeni yanzu haka kwance nake sanyi na ke ji"

"Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, Subhanallahi ka sha magani?"

"Ee na sha"

"Ko na zo na duba ka?"

"Aa ba sai kin zo ba, ki yi zamanki anjima kadan na san zai sauka"

"Allah ya sauwake"

Ta aje wayar ba dan ta gamsu da sauki ba, a take ta soma jin kamar ita ce bata da lafiyar, hankalinta duk ya bi ya tashi. Ji tai bata da natsuwa indai bata je ta duba lafiyarta ba. Amman kuma bata da kudin mashi kuma ta san dare ne yanzu gata da tsoron dare. Tashi tai ta nufi dakin dakin Umma, agogon dakin ta fara kallo tara da yan mintuna ya nuna mata, daman ta san indai Abbah ya wuce tara to ba zai dawo ba sai sha daya ko sha biyu wani lokacin ma har karshe daya yana kaiwa idan ya dauki passengers na nesa. Jikin kofar ta tsaya tana ma Umma magana kamar wata munafuka.

"Umma wai Abubakar ya ce na siya mishi kwai da kwai (awara) kamin ya zo"

Umma ta jiyo ta kalleta.

"Abubakar din ne ya ce a siya masa awara?"

"Ee"

"Zo bude aljihun gado ki dauko naira dari ki siyo masa"

Cike da jindadi ta karasa gurin da Umma ke ake kudi ta bude ta dauki naira dari kamar yadda ta fada mata sai ta dawo dakinsu ta dauki katon Hijab dinta ta saka, ta zura talkamin roba ta fice da sauri. Bakin titi ta fito ta tari mai Napep wandabke dauke da mutum biyu.

"Alu quarters zaka kai ni"

"Dari biyu"

"Kai Wallahi dari ne, dan Allah ka taimaka ko babakin Titi ne ka aje ni sai na karasa da kafa, dan Girman Allah ka taimaka min"

Girman Allah data hada shi da shi ne yasa ya ce ta shigo, suka kama hanyar daman mace daya a can za a sauketa dayar kuma a Badoo. Idonta ta mayar gurin titi amman hankalinta na can gurin Abubakar zuciyarta nata raya mata irin halin da yake ciki. A kusa da gidansa aka ajeta kasancewar gidansa na kusa da titin ne.

"Na gode"

Sannan ta cire takalminta ta zura da gudu saboda duhun da ke gurin, @360 ta isa bakin kofar gidansa. Ta shiga buga masa da karfi kamar wacce tai sata aka biyo bayanta, sam hankalin be bata ta kira shi a waya a sanar masa tana waje ba. Kamin ya bude mata har ta fara kuka, dan har ga Allah gani take wani zai zo ya mata wani abun ne a nan. Sai da ya bude haskem falonsa ya hasko waje, be gama tantance ita din ce ko bata ita ba har sai da yaga ta shigo da sauri tana haki.

"Baby mi ya kawo nan?"

Ya tambaya bayan ya maida kofar ya rufe. Sai ta soma sosa kai.

"Ba ka ce baka da lafiya ba"

"Amman ai na ce karki zo, ya akayi ma Umma ta barki kika zo?"

"Bata san na zo ba, karya nai mata"

"To kin koma yanzu tun da kin ganni, idan wani ya ga shigowarki a unguwar nan ma ai sai yai mana wani zargi"

"Amman ai ba komai zamu yi ba, mu ba yan iska ba ne"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now