Mysteries

1.7K 273 38
                                    

ZINNEERA POV.

Hajiya Karima tai murmushi ta kara matsowa kusa da Zinneera ta kai hannu ta rika fuskarka idonta cike da kwalla.

“Ba zan sake yarda na aikata wani kuskuren ba, na gudu saboda talauci ina neman kudi na barku, yanzu kuma na siye zuciyarki da kudi, bana son ki min so mai dalili, idan har zan biyaki ki so ni to kiyayata zatai ta karuwa ne kawai a zuciyarki, so nake ki so ni so marar dalili da yadda ke kanki sai kin yi mamaki yadda zuciyarki take son mahaifiyarki, ba zan siya son ki da kudi ba ba dan kuma ya min tsada ba, sai dan yayi min arha da yawan da ba zan ci ribarsa nan gaba ba, idan wani abun kike so ki fada na siya miki, amman ba ki tambaye irin wannan kudin kai tsaye ba”

“Saboda ba za ki taba iya cire kudi mai yawa ki yi ma yarki hidima ba ko? Daman can baki san zafinta shiyasa kika gudu kika barta ko?”

Zinneera ta fada kai tsaye, a take jikin Hajiya Karima yai sanyi sai ta janye hannunta daga fuskar Zinneera ta share kwalla da suka zubo mata.

“Zan iya yi miki komai Zinneera ciki har da baki kyautar raina idan da hali, ban gudu na barki ba na gudu na bar talaucin mahaifinku ne da kuma bakin halinsa, miyasa yake ta baki labarin kaina? Yana ta fada miki aibuna dan ki kini, wani be taba labarta miki cewar mahaifinki be yanka miki ragon sunan ba lokacin da aka haife ki? Zanen da dauke lokacin da aka haife ki mahaifinki be siya ba, babu abunda mahaifinki yai miki har na gudu na bar masa gidan ba kuma saboda babu kawai ba sai dan mutuwar zuciya irin tasa, tun da na haife ki Zinneera ban taba ci na koshi ba, saboda mahaifinki baya iya fita ya nemo, shi ala dole sai dai aikin yi ya tararda shi har saman gadonsa, bayan kuma be yi karatun da irin wannan arzikin zai same shi ba, kina da sati biyu a duniya mahaifinki yace min ban haife ki da arziki ba shiyasa ba be samu komai na haihuwarki daga yan'uwa da abokan arziki ba, shin duk be tabarta miki wannan ba? Sai aibuna yake ta fada miki saboda ya dasa miki kiyayyata a zuciyarsa, bayan kuma ba ni kadai ya kamata ki tsana ba har da shi!”

Ta karasa tana maganar da karfi kamar ba dare ba, hawaye masu zafi na sauko zuciyarta cike da bacin rai. Zinneera kam tsaye tai a gurin kamar an dasata kwalla na fitowa daga idonta.

“Tunda na tafi na barku kullum da ke nake kwana na tashi a raina, soyayyar ki tai ta azabbatar da ni, idan na tuna ku sai na kasa cin abinci, na samu wasu yayan amman hankalina be kwanta ba har sai da na dawo gareku saboda ku na dawo garin da babu uwata a ciki balle ubana, na baro aurona da sauran yayana na zo nan na zauna saboda ke da Nabeel, Zinneera”

Tana kaiwa ta share hawayenta ta rika hannun Ikram ta nufi Bedroom dinta. Zauna Zinneera tai a gurin still tana hawayen da bata san na minene ba, tsanar Hajiya Karima ko kuma Abbah? Shin da gaske Abbah yai mata haka ko kuwa Hajiya Karima tana kokarin kare kanta ne kawai. Da wannan tunanin tai bachi a saman tayil din duk kuwa da irin sanyin da ke gurin.
  Sai da Ikram tai bachi sannan Hajiya Karima ta fito idonta a kumbure ta nufo inda Zinneera take zaune, samman kujera ta zauna tana kallonta zancen miliyan talati da tai mata dazun ne ya tsaya mata a rai, har yaushe Zinneera tai wayon da zata tambayeta miliyan talati? Mi zatai da kudi masu yawa haka? Lallai akwai wani abun da take boye ko kuma take kokarin aikatawa, wanda ba zata so yarta ta sake shiga wani kunci ko halin matse na rayuwa ba. A hankali ta kai hannu ta tashe cikin da tausayinta, ita kuma tai zumut ta tashi zaune tana kallonta.

“Zo muje dakin ki kwanta”

Hajiya Karima ta kama hannunta ba tare data jira abunda zata fada mata ba, ita kuma ta bita kamar barawo da mai kaya har suka shiga hadadden bedroom din mai cike da kamshin turaren wuta irin na manyan hajiyoyin nan. Saman gadon ta kwantar da Zinneera sannan ta ja Bedsheet ta rufeta ruf kamar wata jaririya sannan ta kwanta bayanta, a bar Ikram a dayan dakin ita kadai tana bachinta.

SADAM POV.

  Ya dade be kwanta ba, ba dan kuma baya son bachinba sai dan bachin yaki zuwa masa kusa shi balle har ya rabe shi, sai daf da azuba ya samu yai bachi yan mintuna ya farka yai alwala yai sallah asuba sannan ya kara komawa bachin, be farka ba sai ta da rabi and he spend thirty minutes on bed kamin ya sauka ya shiga bathroom yai wanka ya tare da wanki baki ya fito.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now