ZR-02

4.3K 553 33
                                    

Gaban wani katon gate ya tsaya, sau daya ya danna horn, sai ga mai gadin da gudu ya zo ya bude masa gate din yana daga masa hannun duk kuwa da kasancewar gilashin motar tinting ne, na waje baya ganin na ciki sai dai shi na ciki yana gani na waje.

Komai a kebance yake a gidan, an tsara shi kamar wani karamin kamfani, gidane plate mai farin fenti sai dai an kawata ko ina da fulawoyi, a dayan bangaren kuma babu komai sai tarin motoci na alfarma, yamma da motocin wata yar karamar kofar garden ce. Yana faka motarsa wasu yara suka zo da gudu suka zagaye motar suna tsalle, murmushi yai ya bude motar ya fito ya zagayo inda suke tsaye.

“Hi kids”

Yasa hannunsa aljihu.

“Ohhh sorry na manta daga gida na ke ban zo muku da komai ba”

Ya fada yana bata fuska irin yadda yara suke yi, sai suka sa dariya sai daya daga cikin yaran ya ce.

“Amman zamu yi wasan tennis ko?”

“Yes boy ga kayana nan na zo da su, an gyara mana fili?”

Ya fada yana shafa kan yaron.

“Ee Daddy yasa an gyara mana bangare daya cikin Garden”

“Okay kuje ku buga kamin na zo”

Ya mikawa wacce ta fisu girma makullin motar, ta karba da sauri suka bita gurin bude motar suka dauka. Main door ya nufa wata katuwar kofa ce mai kyau da kyali wacce ta kara fitar da kyaun farin fentin kasancewarta baka, hannu ya kai ya tura ya shiga. Murmushi da annashuwar dake fuskar mahaifiyarsa ne suka fara masa lalle marhabun, kana kallonta kasan tana cikin jindadi da kulawa, domin jikinta da yanayin, gurin da take zaune tufafin jikinta sun nuna haka. Kusa da ita yaje yai side hugging dinta.

“Morning Sweetlove”

“How is my Favorite doing?”

Ya saketa yana masawa.

“Am doing fine”

“Ya yanayin garin? Kasan Nigeria akwai zafi ba kamar can ba, musamman sokoto nan”

Ya daga kafadunsa.

“Akwai zafi gaskiya, amman ba irin zafin da zai hanani zama ba, dama can ina kokarin koyon zama cikin zafin ai dan na san ba can zan daumma dole wata rana zan dawo gida, gashi kuma na dawo”

“Haka ne, ka yi breakfast?”

“Yeah ai kin san ni bana wasa da cikina, sai dai ace bana ci da yawa, tun takwas na safe nai breakfast”

“Good, ka shiga ciki mahaifinka yana da baki yana jiranka”

“Okay”

Ya nufi kofar fita, kasancewar part din mahaifinsa yana can yamma da wannan part din, duk da kasancewarta akwai hanyar da kan sada mutum da part din, shi be cika bi ba sai idan ta kama dole saboda dogon corridor ne shi kuma be cika son hanya haka ba.

Glass door ne a gurin, na waje na hango na ciki kamar yadda na ciki yake hango na waje amman idan an daga curtains. Door bell ya danna hakan a hankalto da Daddy ya dauki dan karamin remote din dake saman glass center table mai kamar na ac ya danna sai kofar ta bude. Nan kam sallama yai kamin ya shigo sai duk suka sam masa har Daddynsa.

“Good morning Dad”

Daddy yai masa wani kallo sai ya dan sosa kai.

“Sorry Ina kwana?”

“Kwallahiya zaka ce shine gaisuwar sakkwatawa”

Sai duk suka sa dariya har dattawan dake cikin falon. Yana kokarin zama Daddy ya nuna masa mutumen dake dama da shi.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now