ZR-07

2.6K 339 25
                                    

“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”

Shine abunda Umma ta fada ganin irin kwancin bulolin da ke bayan Nabeel.

“Miya same ka Nabeel?”

Umma ta tambaya idonta na cika da hawaye zuciyarta kuma cike da al'ajabi. Daga kwance da yake rub da ciki ya soma magana a wahalce.

“Wallahi Umma dukana akai jiya da dare har garin Allah ya waye”

“Waya dake ka?”

“Wallahi Umma ban sani ba, amman jiya ban yi bachi ba, dukana akaita yi har safe, kamin a dake ni din ma sai da akai ta kaini sama ana sakoni ina faduwa, ina ta ihu amman babu mai jina, daga baya kuma na gan ni cikin daji mai duhu ga kura da zaki sai sun zo kamar za su cinye ni sai na gan ni a dakin nan, sai kuma na kara ganina can sai kuma na gan ni a nan, babu kalar ihun da ban yi ba amman babu mai jina, daga baya kuma nai ta jin kamar an dannemin kirji na kasa tashi sai dagani ake sama ana jefowo da na fado kife shine akai ta dukana a baya har safe, Wallahi Umma jikina ko'ina ciwo yake ko motsi bana iya yi”

Ya fada hawaye na fito ta gefen idonsa. Umma ta zauna kusa da shi tana kallon bayansa.

“Kai ka cire rigar daman? Wannan abu ko gamo kai”

“Ni ina zan sani, ko Sallah asuba zan yi ba”

Ya amsa a wahale. Aleeya kallon tausayi take masa, a dayan bangaren kuma tana dariyar yadda yake raki rabon da ta ga hawaye a idonsa har ta manta, ta san halin yayan nata mugune na karshe indai aka ce dukansu zai yi ba ya musu da sauki, musamman idan aka ce Zinneera zai doka, amman yau gashi shi ma ya sha dukan ya ji yadda suke ji, wani karin abun dariya ma babba da shi amman an masa wannan dukan har da su hawaye lallai ta san ba karamin duka ya sha ba.

“Sannu Ya Nabeel, gaskiya ka ji jiki”

Umma ta rafka uban ta gumi tana fadin.

“Ina ganin gamo kai?”

“Ni na fi tunanin ko dan na da....”

Sallamar da akai ne ya hanashi karasa maganar. Daga cikin dakin Umma ta amsa Aleeya kuma ta fita tana amsawa.
  Wasu yan mata ne su uku dayar na sanye da abaya, sauran biyu kuma na sanye da gown din atamfa.

“Abubakar ne ya kawo mu, zamu gaisa da Zinneera ne, mu kanensa ne”

Dayar ta fada wacce ke sanye da bakin gilashi.

“Okay, amman Zinneera bata nan ta tafi makaranta sai dai idan ta dawo”

Umma ce ta fito tana musu lale martabun.

“Sannunku da zuwa, ku shigo daki mana”

Sai duk suka gaisheta. Wacce tai magana dazun ta sake cewa.

“Aa mun gode, Abubakar yana waje yana jiranmu, sai dai in mun dawo”

A tare suka juyo suka fito daga cikin gidan, sai suka samu Abubakar tsaye jikin motar yana jiran fitowarsu.

“Wai bata nan ta tafi makaranta”

“Kai amman Babyna tayi saurin zuwa gashi na kira wayarta kashe, muje na kai ku makarantar sai ku gaisa a can”

Ya bude motar ya shiga, sai suma suka shiga yai mata key, yana driving suna fira har suka isa State University. Department dinsu ya nufa ko da yaje ya samu ta shiga lacca hakan yasa ya dawo ya fada musu ta shiga class.

“Kun san yadda za ayi? Ku bari sai anjima na san lokacin ma ta koma gida sai muje can ku ganta”

“No Yaya ni zan bar garin nan 12, sai dai mu dawo ko zuwa goma ko sha daya, dan gaskiya ina son na ga matar nan ta mu, labarinta kawai muke sha ya kamata dai yau mu ganta face to face tunda mun zo garin”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now