Don't Rush Things

1.8K 317 128
                                    

ALEEYA POV.

A hankali ta kai hannu ta rufe bakinta gudun kar tai numfashi mai karfi Umma taji motsinta daga zauren da take boye, kunnuwanta su jiyo mata komai cewar Zinneera na son Sadam da kuma zancen Umma na cewa karta fadawa kowa ita ta san yadda zata bullowa lamarin. Kwalla ne suka cika idonta suka sauko mata tasan Zinneera ce zata samun Sadam baya ita kuma an sakata ta saka sonshi a ranta. Juyawa tai ta jingina da ginin zauren hawaye na mata zuba, da tasan abunda zata ji kenan da bata dawo daga islamiya daukar Fiqhu dinta ba, miya ma tun farko ta tsaya ta saurara? Miyasa lokacin data shigo zauren ta ji Umma na ambatar Sadam kike so, ta tsaya saurare? Wata kila da yanzu duk bata ji wannan ba.

Takawa ta fara yi a hankali har ta fita daga zauren gida tana hawayen da bata san suna zubo mata ba, sai a yanzu take kara jin kaunar Sadam a zuciyarta, idanuwanta sai yawo suke mata da fuskarsa, kashim turarensa yadda yake drees kalamansa da duk wani abu daya danganceshi.

‘Ba lallai ne ya so Zinneera tunda ni ya gani ya fara so’

Wani bangare na zuciyarta ya fada mata.

‘Aa zai so ta, Zinneera ta fini komai, Zinneera ta fini komai kyaun jiki, kyaun fuska, haske da komai ma, zai so ta’

Ita kadai take ta sakesakenta kamin taji an dafata.

“Aleeya”

Tai saurin juyowa ta kalli kawarta Nafisa.

“Lafiya kike kuka?”

“Kuka na ke yi?”

Ta kai hannu ta taba fuskarta sai ta jita a jike da ruwan hawaye. Saurin gogewa tai.

“Ban ma san sun zubo ba”

“Me ke damunki?”

“Ba komai”

Tai saurin yin gaba ta bar Nafisar a tsaye gudun karta sake yi mata wata tambayar. Kamar wacce ta rikice haka ta koma islamiya, karatun ma sai ta kasa yi har aka tashi, sannan ta kamo hanyar gida ita da Larai da Aliyu bata taba jinta cikin irin yanayin da taji yau ba, bata miye so ba sai yanzu da take jin Zinneera na son wanda take so. So silent haka ta isa gida, sallamarta ma can kasa kasa tai duk yadda tai kokarin ta boye damuwarta sai ta kasa sakamakon cika da idonta ke yi da kwalla. A gindin ice ta samu Umma tana gyaran shimkafa yar hausa, Larai da Aliyu suka nufi gurin da Umma take ita kuma ta nufi dakinsu, sai ta samu Zinneera kwance ta dunkule fuskarta da alama bachi take ko kuka, sai kawai ta aje jakar makarantar a gurin data saba ajewa ta juyo ta fito ta nufi dakin Umma, saman gadonta ta zauna ta bawa kofar dakin baya tana kuka. Umma na ganin yanayin data fito tai saurin tashi tabi bayanta.

A lokacin da taji motsin shigowar Umma sai tai kokarin boye kukanta, sai dai ta makara domin Umma taha hawayen nata.

“Lafiya me akai miki?”

“Kaina ke ciwo”

Ta bata amsa kai tsaye. Sai Umma ta zauna kusa da ita.

“Ko dai kinji Zinneera na son Sadam ne?”

Umma ta fada with lower voice tana kallonta. Kokarin yai tai kamar bata ji ba.

“Me tana son Sadam? Sadiq din fa?”

Tambayar take amman kwalla zuba suke kamar dazun. Umma tai shiru sai kallonta take sai tausayin yarta ya kamata.

“To idan ma naji me zai sa nai kuka ni kaina ne yake min mugun ciwo”

Ta fada tana kokarin tashi daga gurin, sai Umma ta riko hannunta.

“Saboda kina son shi... Bana bukatar ki fada min ko karki fada min wannan zubar hawayen na ki ya karantar da ni komai”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now