46

1.7K 317 43
                                    

Ganin Hajiya Karima yasa Sadam mikewa tsaye ya bata kujerar ta zauna, sai dai ba ta zauna a kujerar ba ta zauna kusa da yarta tana taba jikinta.

"Ya jikinki?"

"Alhamdulillah"

Suhail ya mikawa Sadam hannu suka gaisai.

"Sannu"

"Yauwa sannu"

"Zinneera ya jikin na ki?"

Suhail ya tambaya sai ta amsa masa tana murmushi.

"Na ji sauki"

"Allah kara lafiya"

Yasmin ta fada tana murmushi.

"Na yi miki sakwara da miyar agusi an sani ba ko kina ra'ayi"

Hajiya Karima ta fada tana kallon yanayinta idonta yai ja sosai ra rame kamar wacce ta shekara ba ta da lafiya.

"Yasmin ma ta dafa min veggitable kuma ta miki pepper soup"

Suhail ya fada mata jin ta yi shiru bata ce komai ba.

"Ina sha'awar shawarma"

Ta fada tana murza yatsun hannunta.

"Sauko muje na siyo miki"

Sadam ya tari numfashin Hajiya Karima wacce ta bude baki za tai magana. Kallonsa Zinneera tai sai kuma ta kalli Hajiya Karima ta kalli Suhail ta maida kanta kasa. Sadam ya bude ba ki zai yi magana wayarsa tai ringing sai ya firo ta daga aljihu ganin number Daddy ya sashi saurin picking.

"Hello Daddy"

Sai Daddy ya amsa daga dayan bangaren.

"Sadam ya hanya ka isa lafiya?"

"Sorry Daddy mantawa nai na kira ku, na isa lafiya kalau"

"Zinneera fa?"

"Tana lafiya Daddy"

"Ba ta wayar"

Sadam ya mikawa Zinneera wayar.

"Daddy yana son magana da ke"

Zinneera ta dade tana kallon screen din wayar kamar mai kirga seconds din dake tafiya na kiran sannan ta mika hannu ta karba zuciyarta cike da tsoro da kuma fargaba, Hajiya Karima har za tai magana sai kuma wata zuciyar ta hana ta. Lokacin data kara wayar a kunne kin cewa komai tai har sai da Daddy ya fahimcin ta karbi wayar ta hanyar numfashin da yake jin yana fita da karfi ya ce.

"Ya ta kina lafiya?"

Sai idonta ya cika da kwalla har ta kasa amsawa.

"Kin gudu kin saka duk hankalinmu ya tashi, da gurina kika zo ai kin san zan baki mafaka ko?"

"Daddy....."

Sai kuma ta fashe da kuka ta kasa magana.

"Wani abun ne? Fada min idan wata matsalar ce"

"Na gode na gode sa kai magana da ni, na gode da ka tambayi lafiyata, na gode da ka kirani yarka na gode da komai Daddy"

Daddy yai murmushi kamar tana a gabansa.

"Ba komai Zinneera Allah yai miki albarka"

"Amin na gode"

Ta fada hawaye na mata zuba sannan ta mikewa Sadam wayar sukai sallama. Hajiya Karima ya kwanto da kan Zinneera jikinta, tana share mata hawayenta.

"Ta so muje na siya miki"

Sadam ya fada bayan ya saka wayar a aljihunsa.

"Yasmin zata fi ka sanin garin nan, zai fi kyau su je tare"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now