43

1.5K 315 158
                                    

Daure da tawul Suraiya ta fito daga bandaki da alama wanka tai. Sai ta samu Mommy zaune saman gadonta tana jiran fitowarta.

"Suraiya kin tabbatar ba ki fadawa kowa ba?"

Shine abunda Mommy ta fara tambayarta.

"Ban fadawa kowa ba, amman miyasa kike tsoron a aji?"

"To ai ba abun dadi ba ne Suraiya, yarinyar da tai kokarin kashe shi sai kuma yanzu ace zata haihu da shi? Haba wannan ai ba abun murna ba ne"

"Amman Mommy maybe cikin na shi ne fa"

"Na ji na san na shi ne ai, amman gaskiya ba zai zauna da ita ba, dan nasan yana sonta har yanzu zai yin kokarin maidata"

"Ba kin ce saki uku ba ne"

"Uku na ce yai shi kuma yai daya, Suraiya bana son yarinyar nan a yanzu, mu yi mata hallaci iya hallaci mun nuna mata so iya so, amman ta zabi saka mana da kashe Sadam? Gaskiya ba zan iya yarda ta haihu da shi ba"

"To yanzu me za ki yi?"

"Zubar da cikin za'ayi"

Suraiya tayi saurin kai hannu ta rike bakinta tana zaro ido.

"Kisan kai fa kenan Mommy? Aa gaskiya nima ba sonta na ke ba, amman be kamata laifin wani ya shafi wani ba, idan ta haihu da shi ba wani abu bane kuma nasan Sadam sai so abunda zata haifa"

"Yarinya ce ke karama Suraiya ba zaki gane abunda na ke nufi ba, bana son ki fadawa kowa maganar nan, kar Sadam yaji maganar nan balle Alhaji, kuma ina son ki yi mata allurar zubar da ciki tun kamin maganar samun cikin ta kawo gidan nan, nasan za su iya tunanin fadawa Alhaji ko Sadam dan haka ki yi mata allura kawai cikin ya zube ki yi duk abunda za ki iya a yau din nan ba sai gobe ba domin za su iya zuwa fadar cewar tana ciki...."

"Mommy Wallahi ba zan iya kashe rai ba"

"Cikin wata nawa ne?"

"Ban sani ba sai ta kai fitsarin an auna, Mommy dan Allah kar ki cilasta ni Wallahi ba zan iya ba, ko da na wani ne balle na Sadam, kuma Wallahi kin san duk yaji ba zai yafe min ba"

"Au fada masa za kiyi? Ni ban isa nai sirri da ke ba?"

"Ba zan fada ba. Amman gaskiya ni ba zan iya aikatawa ba"

"To ki jira ni zan yi da kaina tunda haka kike so"

Mommy ta fada a fusace sannan ta tashi ta fice daga dakin cikin bacin rai.

"Da na san haka abun nan zai zama Wallahi da ban fada ba..."

Cewar Suraiya cikin kukan da bata san da zamansa ba sai yanzu.

ZINNEERA POV.

Tana shigewa dakin, Umm ta nufi dakinta rike da baki tana ta salati kamar wacce ta ji wani mugun abu.

"Umma lafiya?"

Aleeya dake aikin gyaran dakin ta tambaya.

"Ina lafiya Ciki ne da ita...?"

Aleeya ta rufe baki da sauri.

"Ciki?"

"Eh daman ni naga alamar hakan"

"Yanzu ya za ayi kenan?"

"Zubarwa mana, idan aka bar cikin har ta haihu ke kina ganin Sadam din zai aureki ne? Kuma ai Yaya zai iya cewa ta a gyara auren tunda saki daya ne, ni ko wallahi ba zan bari haka ta faru ba, tunda ta zabi cimin mutunci ba kuma zan yarda ta je tai riba biyu ba, ai ba dan ke bana son ki samu jindadin ba na hanaki na goya mata baya, amman yanzu tunda na gano manufarta wargatsa zumuncina da Yaya wallahi ba zan bari ya lalace ba, kuma wannan jindadi sai dai wata ta same ko kuma ke amman ba ita ba"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now