ZR-06

2.6K 550 72
                                    

  Babu inda ba aji ihunta ba, tun Nabeel na dukanta har ta soma bashi tausayin, domin ba dukan wasa yake mata. Babu kalar kukan da bata yi wani zakaji shi kamar na mage wani kamar na kare bayan ta gama na mutane. Mutanen da ke shigowa ne ke ta batawa Umma hakuri akan a kyaleta, bata fadawa kowa gaskiyar dukan da ake mata ba, sai cewa tai wai Nabeel ta zaga shiyasa ya zaneta. Masu bata laifi na ta yi daman ansan halinta indai tsiwace da rashin jin magana ta bata ji bata gani.

A dakinsu tai ta aikin kukanta, tun tana jira Umma ta shigo ta rarrasheta har ta gaji ta hakura dan kanta ta daina kukan. Misalin karfe goma sha daya na dare Abbah ya dawo, tana jin motsin shigowarsa amman bata tashi ba dan tasan bata da gaskiya.
  Bayan kamar minti talatin ya shigo dakin a hasale, tana ganinsa tai saurin tashi zauna tana matsar kwalla.

“Ba ni wayarki, wato iskancin na ki da rashin kunya kara yawa yake ko?”

Sai kawai ta fashe da kuka sai a yanzu ma ta tuno da wani zancen wayar data baro a motar Sadam.

“Ba magana nake miki ba”

Wani mugun zabura tai sakamakon tsawar daya daka mata iya karfinshi.

“Ban... San... Ban san..... Inda... Take... Ke.. Ba... ”

Ta amsa cikin muryar kuka kamar zata shude.

“Wannan wane irin rashin kunya ne, ki taka da kanki zuwa dakin saurayi? Wannan sam ba tarbiya ba ce”

“Wallahi Abbah ba mu komai ba, komai ba mi yi ba, ko dan iskancin da ake ganin kamar mun yi na rantse da Allah ba mu yi ba...”

“To miya kaiki inda yake...? Shi ya kiraki”

“Aa ni ce naje da kaina, saboda bashi da lafiya ne sai hankali ya tashi”

Wani kallo yai mata irin kallon nan na har yanzu baki da wayo, ya juya ya fice daga dakin. A dakin ta kwana sallah isha'i ma sai can tsakar dare ta fito tai alwala ta koma cikin dakin tai sallah. Da gangan ta bi ta kan Aleeya ta taka mata hannu, haushi kowa take ji a cikin gidan tun da ita kadai aka daka akan laifin da take gani na rashin dalili tun dai ba su yi komai ba.
  
Washe gari, wuri ta shirya cikin blue atamfa da farin Hijab, amman tai zamanta a dakin ta ki fitowa har sai da Abbah ya fita, sannan ta fito cikin kafarta mai ciwo tana dinshigi, bata jin gaisuwa yau tun da an taba ta jiya da dare, dan haka kawai ta zo jikin kofar Umma ta tsaya tana turo baki kamar ana ja mata shi.

“Umma ba ni kudin makaranta”

Wata uwar harara Umma ta watsa mata sannan ta daga fillo ta jefo mata dari hudu na napep.

“Yau ma ida kinje daga makarantar ki wuce gidanshi”

Bata dai ce komai ba, ta shiga tsakar dakin ta dauki kudin ta fice tana ta gunguni. Bata san Umma ba zata ce mata ta dawo ta karya ba, ko da suna abun arziki ba kullum take ce mata tsaya ki karya ba balle yau da take fushi da ita. Aleeya dai dake aikin gyara wandon uniform dinta ta kalleta ta ce

“Ba zaki tsaya ki karya ba”

Kamar jira take ta juyo kanta fuskarta da hawaye.

“Eh ba zan tsaya din na ci ba, ina ruwanki bakar munafuka, kin jidadi an dake ni ko Allah Sai ya saka min, bakar annamimiya, hegiya mai fuskar an wuta, da wasu hakora nata kamar kasuwar cibabe...”

Fitowar Umma ne yasa ta gintse maganar ba dan ta gama, Aleeya dai ta tsaya tana mata kallon mamaki, ita take neman yi mata abun arziki ta maida shi na fada.

“Halin ne na ki baki fasa ba ko? Yar'uwarki kike cewa mai fuskan yan wuta? Wato duk dukan da aka miki jiya baki natsu ba ko?”

Sai ta fashe da kuka tana nuna Aleeya.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now