39

1.5K 244 98
                                    

A gurin ta kwana har asuba bata runtsa ba, Nabeel din ma be runtsa ba sai gadin yar'uwarsa yake, yana ta ganin rashin kyautawa a abunda Abba ya aikata, ta wani bangaren kuma yana tausayin yar'uwarsa na rashi uwa, da ace tun farko Hajiya Karima ta tsaya ta kula da su, yasan dukan abunda zai faru ba zata kisu ba a matsayinsu na yayanta, ya tabbatar da ace yau Umma ita ta haifi Zinneera da cikinta ba zata yarda Abbah ya turata waje ta kwana ba, and now Zinneera ta rasa Umma saboda abubda ta aikata.
   Ana sallati Nabeel ya ce da Zinneera ta tashi su shiga gida, tunda daman kwana a cikin gidan ne Abbah ya hanata yanzu kuma safiya ce. Tashi Zinneera tai ta sai ya karbi abun shinfida da tabarma yana gaba tana baya har suka shiga cikin gidan. A bakin balcony suka samu Abbah yana alwala tun daya ya dago ya kallesu sai Zinneera tai tsaye a bakin kofar kamar an dasata. Nabeel kuma ya karasa gurin Abbah yana masa magana a hankali.

“Abbah kai hakuri dan Allah....”

Kamin ya karasa Abbah ya daga nasa hannunsa dake da sanyin ruwan daya fara alwala.

“Ba zata zauna min a gida ba, taje can ta karata”

“Abbah korarta zakai?”

“To me zata min idan ta zauna? Aurar da ita nai dan taje ta kashe dan mutane? Ko kuma dan ta kashe auren ta dawo?”

Hayaniyar Abbah ce ta saka Umma ta fito waje tana daura dankwalin kanta tana hamma alamar yanzu ta tashi daga bachi.

“Idan ka koreta bata da inda zata je inda ya fi nan, Abbah kai mata ko wane irin hukunci amman ban da kora domin ita macece, kai ma ba zaka so ta rika tafiya rabe rabe gidanjen wasu ba”

“Babu abunda zaka fada min wanda zai hana ni korarta a gidan nan dan banga amfanin zamanta ba, na ji da maganar jama'a da za a fara yi ko da ganinki kinyi aure kin dawo. Ke wuce ki fice min daga gida...!”

Ya karasa yana dakawa Zinneera tsawa, ba shiri ta juya da sauri jikinta har bari yake ta fice daga kofar.

“Ka gafarce ni Abbah, indai Zinneera ba zata zauna a gidan nan ba, nima ban ga amfanin zamana ba”

Nabeel ya fada sannan ya zubar da kayan dake hannunsa tabarma da zanen lullube ya nufi dakinsa. Sai a lokacin Umma ta saka baki tana ta bawa Abbah hakuri.

“Gaskiya wannan hukunci be dace ba, nasan ta aikata abunda be dace ba, amman kai mata uzuri, idan ma ka koreta wani karin abun magana ne, kuma baka san hukuncin da zasu yanke ba, ka saurara mata na wani dan lokaci tukuna...dan Allah kai hakuri”

Be ce komai ba, ganin hakan yasa Umma ta nufi dakin Nabeel ta daga labulen dakin ta leka.

“Nabeel bar hada kayan nan babu inda za ku je... ”

Sannan ta nufi waje dan dawowa da Zinneera. A zauren gidan ta sameta tana ta rusar kuka ta jingina kanta da ginin gurin.

“Wuce ki shiga gida wawuyar banza”

Tana fadar hakan ta juya ta koma, sai da Zinneera ta share hawayenta sannan ta soma takawa kamar marar lafiya ta shigo cikin gidan kanta a kasa har ta shiga dakinsu wanda suke kwana ada ita da Aleeya da Larai da Aliyu.

SADAM POV.

Ko da wasa bachi be ziyarci idonsa ba, shi da damuwa suka kulla abota, idanuwansa kuma suka kasa gasgata masa cewar Zinneera bata sonsa da gaske, wani wata rayuwa da sukai ta farinciki idanuwansa ke ta kawo masa hotonshi. Misalin sha biyu da rabi ya sauka daga saman gadon da yake kwance yana ta juye juye ta nufi wardrobe ya bude ya dauko lace da Zinneera ta saka ranar da aka kawo ta gidansa ya risina a gurin ta jimke lace din a hannunsa yana cikawa bakinsa iska, can kuma ya lumshe ido ya busar da iskar. Lokaci daya kalaman data fada masa a asibiti suka dawo masa a rai, sai yai saurin mayarda lace din ya rufe wardrobe din ya nufi bakin gado ya zauna.
Farkon abunda ya fara ji is Zinneera bata yauta masa na auren shi bayan Sadiq take so ba...

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now