34

1.5K 232 64
                                    

Nan da nan jikinta ya fara rawa sosai abunka da wanda bata saba ba, numfashin har wani gargada yake sai dai ba tai unkurin yin komai ba har sai da taji yana kokarin rabata da tufafin jikinta gaba daya sai tai hanzarin fado kasa daga kan gadon da sauri ta kai hannunta tana lalaben bedside lamp ta kunna, tana ganin yadda yake tai saurin juyawa tana boye jikinta.

“Me ya faru”

Ya tambaya kamar wanda maganar bata son fitowa daga bakinsa.

“Sadam ba yanzu ba, be kamata mui yanzu ba”

Samun kansa yai da murmushi duk kuwa da irin yanayin da yake ciki, jin shiru yasa ta juyo ta kalleshi kadan ta kawar da fuska da sauri.

“Kaga zan iya daukar ciki... Kuma.... Kaga ina karatu karatuna zai iya samun matsala, ni bana son haihuwa yanzu”

Fadada murmushin yai kamin murmushin ya zame masa dariya, dariya bata wasa ba, kawai shirmenta na burgeshi wani lokacin abunda take ko yar shekara goma sha biyar ba zatai ba. At first ya dauka tsoro take ji saboda irin tsoratawan nan da kawayen amarya suke mata na daren farko, amman wannan maganar ta tsoron ciki tasa shi dariya da mamaki. Sauko da kafafunsa yai ya karasa inda take zaune tana kallonsa ya kai hannu ya shafa fuskarta tare da matsar fuskarsa kusa da tata.

“Komai na ki burni yake Zinneera, ban san iya adadin kaunar da zan kara miki nan gaba ba...”

Har ta bude baki za tai magana sai ya saka mata bakinshi cikin nata ya kai dayan hannunsa ya kashe lamp din...

At first ta dauka abun mai sauki ne, har sai da taji ya fara fin karfin jikinta da kwakwalarwa, a duk yadda aka fada mata da kuma yadda take jin labari sai ta tarar abun yafi haka, ashe duk labarin da take ji sharar fage ne akan abunda take ji a yanzu, babu kalar rokon da bata masa ba, a duk yadda take tsammanin Sadam zai raga mata saboda yana kaunarta sai ya samu kansa da rashin tausayinta a wannan bangaren, tun tana kuka da hawaye har ta fara kukan ba hawaye, gaba baya ta soma ganin kamar ba a duniya take ba. Shi kansa Sadam be san a duniyar da yake ba har sai da natsuwarsa ta dawo jikinsa. Yaji tausayinta sosai ammn tausayin bd hanashi sake mika bukatarsa gareta, ba kuma jiran yake ta karba ba, shi yake aiwatarda komai a gonarsa.
  Na samu natsuwa da nishadi irin wanda be tana mafarkin samu ba, ya wanzu a duniyar gamsu fiye da kima, wata kila saboda ita tana halinsa ne kuma ya same ta a mace cikanciyar mace wanda hakan ya kara mata kima da martaba a idonsa.

Misalin shida da kwata na safe ya shiga tashinta a hankali. Tana bude ido ta kalleshi sai ta ganshi biyu tsabar har yanzu azabar bata saketa ba, ga kuma nauyin bachi da yake idonta sai da ya sumbanci fuskarta sannan idanuwan nata suka watsake ta soma ganinsa daidai. Fashewa tai da kuka.

“Dan Allah dan girman Allah ka kyaleni hakan nan na shiga ukuna”

Murmushi yai ya zauna gefen gadon tare da kai hannu ya janye Bedsheet din da take lullube da shi ya tasheta zaune, babu tufafi a jikinta amman bata da wani kuzari da zata iya saka koda hannunta ta tare kirjinta. Masauki yai mata a kirjinsa ya kai hannunsa ya shafa kanta.
Be san ta ina zai fara yi ma Allah godiya da kyautar da yai masa ba, na bashi ikon auren Zinneera ko kuwa na ni'imar da Allah yai mata wanda ta sama mishi natsuwa da kwanciyar hankalin da be tsammani ba? Ko da be same ta a budurwa ba, ya san zai so ta domin ba dan wani abu na jikinta yake sonta ba, ballantana yanzu da ta rike tarbiyar iyayenta ta kawo yanci har gidan mijinta.
   Daga ita har shi sun lula wata duniyar, shi dai ya tare a zangon kaunarta da godiya ga mahalinsa akan kyautar da yai masa, na samu mace kamar ta. Tsabanin ita da take tariyo abunda ya faru a daren jiya, har ta bakincikin yadda tunani ya kasa bata hadin kan da zata kare Sadam daga kaiwa ga tanadin da Sadiq kawai tai ma shi. Ta karya alkawari data dauka masa na cewar jikinta nashi ne shi kadai, lallai ita sakarya ce kowa yai gaskiya daya ce bata tunani irin na mutune, yanzu idan ta samu ciki fa? Ina alkawarin da tai ma Sadiq? Nan da shekara daya zata iya rasa masoyinta akan abunda ta aikata na dare daya.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now