Life Is So Confusing

2.2K 321 31
                                    

Tafiya take kalaman Sadiq na kai kawo akwakwalwarta, kokarin banbance ganganci da kuma son zuciyarsa take, da gaske yau tunani take irin na mutane. Daga unguwar lodge road zuwa Abdullahi Fodio Road tafiya ce mai nisa, amman cikin kankannen lokaci ta iso kamar wace tai tafiya cikin iska. Ita kanta ba san ta iso ba sai da ta tsinci kanta a kofar gidan. Wata farar takarda ta fara arba da ita aje a zauren gidan. Bata yi tsammanin ita aka ajewa dan ta karanta ba, kamar yadda zuciyarta ke raya mata ba iska ya dauko ta ya kawo ba, domin takardar fara ce kal babu alamar datti ko tamukewa a tare da ita. 
  Risinawa tai ta dauka, sai ta fara arba da sunanta a saman takardar kamin wani dogon sharhi ya biyo baya, a zuci ta karance kalaman ta haddace su akanta tas, sannan ta doshi cikin gidan tana share hawaye. Bata samu kowa a tsakar gidan ba, hakan kuma ba karamin dadi yai mata ba. Kai tsaye ta wuce dakinsu ta zaune a gurin da take ganin zai isheta tai kukan da babu mai jinta, yau kuka take ba na shagwaba ko fada da wani ba, kuka take na damuwa irin damuwar da bata taba jin yanayinta, bata iya tantance komai a yanzu, da gaske son Sadiq take ko tsanarsa? Ranta yana sosuwa a kowane harafi na labarinsa, ina ma be zayyana mata komai ba.

  Kanta ne ya fara rawa dama na haka yake mata a duk lokacin da take kuka. Kana jin yanayin kukan kasan bana mutane ba ne, ta ba yi ta ci abunta har ta tsude Umma bata ce mata Uffan ba, amman yau sai ga Umma da gudu cikin dakinta ta rikata.

“Zinneera lafiya”

Idonta ne ya fara rikidewa kamin tabar jikin Umma ta soma shureshure abunda bata taba ba.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”

Ita kadaice kalmar dake fito daga bakin Umma, domin ita kanta yau ta san Zinneera ba ita kadai take ba. Tashi tai zuwa kiran mutane, domin Abbah tun fitarsa yai gaba da bacin ransa. Makota ta shiga tana kukan a taimaka mata domin babu kowa a cikin gidan sai ita kadai. Ka kace kwabo gidan ya cika da mutane mata, duk wanda ya san Zinneera a ranar sai da ya tausaya mata domin ta fita hayyacinta wasu abubuwa take da duk wanda ke kallonta ya san ba yin kanta ba ne. A take aka je har Islamiyarsu aka nemo mai makaratu har mutum biyu suka suka yi alwala su ka soma yi mata ruqya. An kusan magariba ana abu daya sannan su soma bada hakuri suna fadin za su tafi.

“Su waye ku?”

Daya daga cikin malaman dake mata karatun ya tambaya. Sai suka yi shiru ba su ce komai ba, a nan ya cigaba da yi mata karatu sai ta fara kugi cikin wata kalar murya, tana fadin.

“Zamu tafi?”

“Miyasa kuka shiga jikinta?”

“Son ta muke, tun tana da wata hudu a duniya”

“Me tai muku kuka shiga jikinta?”

“Batai mana komai ba, a bakin kofa Karima ta ajeta mu kuma muka shafeta, da ta girma sai muka shiga jikinta, duk wani abu da take mu ne mune muke saka ta”

“Ku fita da izinin Allah, ko na kona ku”

“Zamu tafi, amman za mu dawo”

Shine abunda suke ta fada jikinta nata karkarwa, bakinta har kumfa yake fitarwa. Ta samu minti talati tana haka sannan ta soma bachi kamar ta suma. After like five minutes ta farka a firgice tana kallon mutane dake zagaye da ita, Umma kam aikin kuka kawai take.

“Lafiya miya faru?”

Ta tambaya tana kokarin tashi tsaye, iyakar abunda ta sani, kuka take na abunda ya faru tsakaninta da Sadiq  bayan shi bata sake sanin abunda ya biyo baya ba sai ganinta a tsakar gida kowa yana kallonta,ga malaman makarantarsu har biyu rikeda kur'ane. Umma taje ta rikata da sauri.

“Ba komai zo ki yi sallah ki kwanta”

Sannan ta kalli malaman.

“Idan Malam ya dawo za a aiko da abun sadaka, an gode sosai”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now