He Wiped Away Her Tears.

2.8K 345 35
                                    

Ya dade a tsaye gurin yana ta tunani abubuwa mabanbanta, ya zai bullowa lamarin taya Zinneera zata yarda da shi me zai fada mata da zai wanke kanshi. A hankali ya bude idonsa ya soma takawa ya zuwa inda bindigar take, kusa da kwali ya hangi wata farar takarda a kasa, hannu ya kai ya dauka ya duba.

*TUNATARWA CE KAWAI*

Shine abunda aka rubuta cikin manyan harufa. Matse takardar yai a hannunsa kamin ya kai dayan hannunsa ya dauki bindigar.

“Duk rashin hakuri ne ya ja min”

Ya furta idonsa na kokarin cika da hawaye.

“Wannan ce bindiga ta biyu daya kawo wasan abunda zai kawo gaba? Wata police zai turo su kamani, da wani ya ci karo da bindigar nan ba Zinneera fa? What else zai faru?”

Magana yake da kansa hawaye na masa zuba, be damu daya share ba, ya saka bindigar cikin kwali tare da takardar ya rufe ya mike tsaye yana fadin.

“Ina zan samu miliyan ashiri? Haka zan yi ta zama a rayuwata kenan? Waya sani ko bayan miliyan ashirin din zai sake bullowa da wani abu?”

Bedroom dinsa ya nufa can cikin dorowar daya aje wacan ta farko ya saka wannan, sannan ya zauna bakin gadon yana sauke ajiyar zuciya.

“Na saka rayuwata cikin hadari, yanzu kuma ban san waye next a iyalina ba”

Zinneera ce ta fado masa a rai sai yai saurin mikewa tsaye ya nufi bathroom.

“Dolle ne nai magana da ita, karta tona min asiri ya kamata na fada mata gaskiya...”

Sai kuma ya dan tsaya.

‘Idan ya fada mata gaskiyar zata aure shi?’

Ita ce tambayar da yai ma kansa.ya san tana son shi, amman idan har ya fada mata gaskiya kuma ta fadawa iyayensa ba za su yarda ya aureta ba. Sai dai ko da hakan zai faru ba zai ki fada mata gaskiya ba, domin ta riga ta ga bindigar idan har be fada mata gaskiya ba, ba zata yarda da shi ba, hankalinta ba zai kwanta ba, idan kuma yai mata karya dan ya wanke kansa a gaba ba zata yarda da gaskiyarsa ba.
  Be dauki wani dogon lokaci yana wankan ba, ya fito a gagauce ko mai be tsaya shafawa ba, ya saka tufafin sai turare ya dauki makullin motarsa ya fice.

MOMMY POV.

Sai da Daddy ya gama karya sannan ta kwashe kayan ta maida gefe tana dauko masa zancen Umma.

“Jiya kun dawo cikin dare sosai, ya su Umma?”

“Lafiya kalau”

Bata ji Daddy yace komai ba.

“Ina yar gidana Zinneera?”

“Tana nan, wai aure zasu mata”

Mommy ta daki kirji kamar wacce taji wani mugun abu.

“Aure? Ba karatu take ba”

“Nima shi na gani, ina tunanin karatun nata ne suke son su lalata, wai wani abubuwan da take sun yi yawa ayi mata aure ko zata natsu, ni kuma ina ganin aure ba solution ba ne”

“Haba dai, suna tsawalawa yarinyar nan dai, yanzu ita Zinneera har wani abu take da take bukatar aure?”

Daddy ya tabe baki.

“Na fada mata kurciya ce, kowa da irin tasa nan da wani lokaci ko ance tai ba zata yi ba, itama kanta ba son auren take ba, dan jiya daki ta shiga ita kadai wata kila ma kuka take”

“Ashe ba zasu iya daukar abunda Siyama take ba, dan Allah idan gajiya su kai da ita ka dawo da ita nan, tun da daman can tana son zaman nan”

“Anya mahaifinta zai yarda”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now