42

1.3K 244 128
                                    

Wata kalar kunya ce ta baibaiye Zinneera lokacin da ta shiga dakin likita, duk wani bayani sai ta kasa yi idonta ma sai ta kasa dagawa ta kalli Suraiya wacce ke sanye da yellow lace ta dora rigar likitoci sama idonta sanye da farin gilashi, hannunta na dama kuma rike da pen tana kallon Zinneera. 
Sun dauki minti talatin a haka Zinneera ta gagara ko da dago kanta ta kalleta balle har tai mata magana sai matsar yatsun hannunta take.

“Me ke damunki?”

Suraiya ta tambaya kamar da fada.

“Ba komai”

Sai tai saurin mikewa tsaye zata fita.

“Look ni likita ce a nan, babu ruwana da damuwarki idan zaki fadi ciwonki ki fada idan kuma ba ki fada ba ke ta shafa”

Komawa tai ta zauna idonta cike da kwalla.

“Kaina yake yawan ciwo, kuma ina yawan bachi, da kasala, wani lokacin i a jin kamar zan yi amai kuma ba zan yi ba, ga yawan bachi”

Suraiya ta dan tabe baki tana kallonta.

“Yaushe rabon da ki ga al'adarki?”

“Yanzu ina cikin wata na uku”

Dan rubutu tai a takardar guda biyu ta ta mika mata sannan ta dago ta kalleta.

“Kije laboratory a baki wata yar karamar roba ki yi fitsari ki kawo min. Wannan kuma za ki basu jininki ne da fitsarinki sui miki text”

Hannu Zinneera tasa ta karba kamar wacce akaiwa kyautar kudi.

“Na gode”

Ta fada a sanyaye.

“Kar ma ki gode”

Suraiya cewar Suraiya tana watsa mata harara. A sanyaye Zinneera ta fice daga office din rike da takardun dayan hannunta kuma na rike da nikab din data cire lokacin da zata shiga office din ta nufi gurin da Aleeya take zaune tana jiranta kusa da ita ta zauna.

“Tace na kai wannan lab wannan kuma nai fitsari na kawo mata”

“To kije ki kai mana”

“ban san gurin ba”

“Tambaya za ki yi mana, ni ba zan iya tashi rakaki ba kuma mu dawo nan dan wahala”

Mikewa tai ta nufi hanyar fita daga ward din tana kallon wata mai tallar dafaffen kwai, har ta wuce ta sai kuma ta kira domin ranta ya biya sosai.

“Nawa kwai?”

“Naira hansin”

Ragowar naira talatin din siyan kati dake hannunta ta kalla.

“Za ki bar min talatin? Wallahi su kadai suka rage min”

“Aa ba a ce na saida haka ba”

Yarinyar na fadar hakan tai gaba, Zinneera kuma ta hade yawu ta cigaba da tafiyarta. Da tambaya da tambayar har ta isa gurin ta mika musu takardar sai suka ce sai taje ta siyo sirinjin da za a dibi jininta da shu, suka mika mata roba biyu wacce zatai fitsarin a ciki ta kawo musu daya, sannan suka nuna mata inda zata je ya siya dari uku na awon jini da fitsari.

“Zan iya bari har gobe saboda ban zo da kudin awon ba yanzu”

“Ba matsala duk lokacin da kika shirya sai ki kawo, daman ai sai gobe za a dauki jinin saboda ba a son ki karya kuma fitsarin na farkon safe zaki kawo mana”

“To na gode, dan Allah ina zan yi fitsarin?”

Macece ta kwatanta mata inda zata bi ta isa bandakin cikin asibitin. Kwatancen tabi har ta isa bandakin tai fitsari tai sarki sannan ta nufo hanyar dawowa. Wayarta ce tai ringing ganin number Sadiq yasa tai saurin dagawa.

ZABIN RAIOnde histórias criam vida. Descubra agora