HAJIYA KARIMA

1.9K 263 16
                                    

BAYAN KWANA BIYU.

         Umma tai farinciki sosai lokacin da Daddy yai ma dansa tayin Aleeya, tasan yayi hakan ne ba dan komai ba, sai dan karfafa zumuncinsu. Ko ba komai ta san yarta zata jidadi sosai aure gidan naira kuma inda ake ganin kimarka ake girmamaka. Sai dai hakan be sata ta hanke hukunci ba har sai da tai ma Aleeya maganar kuma ta fadawa Abbah.
  Abbah kusan yafi kowa farinciki domin Abbah na cikin irin mutanen da keson aurar da yarinya da zarar ta fara girma musamman Aleeya dake da jiki sosai lokacuta da dama idan suka fita tare da Zinneera ana daukar cewar ita yayar Zinneera saboda yanayin jikin Zinneera.

Unexpected maganar auren ta zo ma Aleeya.

“Ni ni Umma? Ko dai Zinneera?”

Shine abunda take ta tambaya, lokacin da Umma ta labarta mata cewar Sadam ya ganta kuma ya aiko yana sonta.

“Ke ba mutum ba ce da zai yana son ki?”

“Umma kawai ina mamaki ne, kin san irin yaran masu kudi basu cika son chubby girls ba, musamman idan ace mutum ya zauna kasar waje”

“Ai ba duka aka taru aka zama daya ba, anjima zai zo ku gaisa dan haka sai ki shirya”

Ta yi saurin rufe fuskarta cike da kunya da kuma farinciki da bata taba jin irinsa ba, ba zata ce son Sadam take a take ba, amman ta jindadin wannan albishir din da Umma tai mata.

“Idan kin ganshi kina son shi kun daidaita kanku sai iyaye su shigo ciki, n Ji Abbanki ma yana zancen hade ki da Zinneera”

Tashi tai cikin dariya da kunya ta bar dakin. Umma ta bita da kallo tana murmushi kamin da maida dubanta gurin Zinneera wacce ke zaune a dakin amman har suka ci maganar suk sude bata saka baki ba domin hankalinta baya jikinta kwata kwata.

“Zinneera...”

Sai da Umma tai mata kira hudu a na biyar ta amsa da sauri da alama sai yanzu ne hankalinta ya dawo jikinta.

“Na'am Umma magana kike?”

“Zinneera me ke damunki?”

Ta sanda kanta kasa tana wasa da hannunta idonta cike da kwalla.

“Maganar da Abbah ku yai ne?”

Nan ma shiru tai.

“Zinneera iya hakurin daya kamata ayi Abbah ku yayi akan Sadiq, domin ba kowa ne zai so ana magana ana dagawa ba, wannan shi ne karo na hudu da Sadiq ke ta daga auren ba tare da wani uzuri ba, ban san uzurinsa ba, amman ina tunanin indai har da gaske yake ya kamata ya unkuro ya kawo jiki ko da ayi auren a yanzu ba, san an biya sadakinki ko kuma ma an saka muku rana nan da wani lokaci, Zinneera wannan karon uzurin Mahaifinki zan karba, idan mu ne yau gobe ba mu ba ne, kuma duk uba na gari yana son yaga yarsa ta kama dakin mijinta, musamman mahaifinki da ba karatu yake so mai zurfi ba, amman ya yarda ki cigaba da karatu ya kamata ke ma ki faranta masa rai ta hanyar auren nan”

Ta dago tana kallon Umma hawaye shar a idonta.

“Sadiq ya fada min Abbah yace masa daga wannan ba zai sake daga masa kafa ba, amman Umma baku yi tunanin shi ma Sadiq din yana da wani uzuri na dabam ba? Kuma duka yaushe Sadiq ya fara neman aure da har za'a ce an dade ba yi ba”

“Amman ke Zinneera baki taba tambayar kanki miyasa Sadiq yake ta daga auren ba? Yana da gidan zama har mota yake da ita kuma yana aiki amman kullum sai ya rika cewa be shirya ba, sai yaushe zai shirya ne? Amman ya kamata ace ko sadakinki ne ya biya yadda hankalin mahaifinku zai dan kwanta”

Hannu tasa ta share hawayenta.

“Ina da damar nai masa wannan maganar? Idan nai masa maganar ba zaki ce na yi rashin hankali ba?”

ZABIN RAIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant