Thirty Million

1.7K 270 69
                                    

Zinneera na gurin zaune tana sharar bachinta hankalinta kwance kamar tana a gida. Har aka watse taron babu wanda wanda ya san da zamanta a gurin domin dabam dabam aka tafi kasancewar dare yayi sosai sai wasu suka soma tafiya tun kamin a rufe taron, Umma ta koma tare da yayanta guda biyu Larai da kuma Aliyu sai ta bar Aleeya ganin ta koma gurinsu Mommy ana ta fira, a zatonta Zinneera ma tana harabar gurin ko kuma wani gurin a cikin kamfanin, haka yasa Umma bata tsaya nemanta ba, ta shiga motar data kawo su ta maida su gida.
Lokacin da su Daddy suka tashi zuwa gida sai suka tsammaci Zinneera ta bi Umma sun tafi gida tare, babu wanda yasan da zaman Zinneera a inda take sai Sadam, shi kuma ya gagara fadawa kowa cewar tana can gudun kar aje dubata a tarar ya lullubeta da rigarsa, idan aka gani ya Aleeya zata kalleshi? Me zai fadawa Daddy bayan yace ya daina shiga sabgarta, he just can't talk anyone tana can. Mota daya suka shiga da Aleeya da Siyama, a bakin gate din ya fada musu cewar akwai wata a ciki kar a rufe gate din gaba daya, sai da ya sauke su family house dinsu sannan ya kama hanyar gidansa a lokacin 1:21am, zuciyarsa nata raya masa yaje ya dauke ya kaita gida, sai kuma ya hana kansa, domin yana son ya manta da shafin rayuwarsa, ya kamata ya daga mata kafa yanzu kam, yasan Sadiq yana da gaskiya akan kishinsa yana jin idan shi din ne ma ba zai iya bari ko kallonta Sadiq yai ba, and Daddy ya riga ya hada shi da Aleeya akam me zai cigaba da kulata? Wayarsa ya ciro ya nemo number Sadiq wanda ya manta when ya su kira juna, sako ya aika masa ba tare da tunanin ko fargabar komai ba.

'Kaje ka dauki Zinneera tana can cikin kamfani tana bachi a vip'

Yana aika masa sakon ya maida wayarsa aljihu ya danna horn, ba a wuce minti biyar ba mai gadin ya bude masa gate. Daf da kofar shiga ya faka motarsa ya fito ya soma taka stairs din.

"Sadam Darling tun da la'asar nake jiranka"

Juyowa yai ya kalli inda muryar take fitowa, sai a yanzu ya lura da Malika sanye da doguwar rigar atamfa.

"Ya akai kika shigo ne?"

"Mai gadinka ya bude min na tararda wannan kofar rufe"

Ta fada tana wani lankwafar da kai tana cizon baki. Juyawa yai ya shigaba da hawa stairs yana gaba tana bayansa har suka shiga falon. A saman dorawar dake gefen kofar ya aje keys din hannunsa, yana kokarin cire cover shoes din kafarsa yaji ta rumgume shi ta baya ta kwantar da kanta jikinsa tana yawo da hannayenta a kirjinsa. Lumshe ido yai ya sauke ajiyar zuciya kamin ya bude ya juyo ya banbare hannayenta daga jikinsa.

"Malika please na fada miki ki daina zuwa gidan nan idan ba ni na nemo ki ba"

"Ina son ka Sadam, ina jin dadi mu'alama da kai ba zan iya jira har sai ka neme ni ba, ni da zan samu yadda na ke so zan zauna a gidan nan kamar matarka na maka alkawarin zan maka komai"

Murmushi yai ya nufi bakin gadonsa ya zauna, yana fuskantar windows din dakin.

"Bana alfahari da kaina, amman na san ba dan neman matan dana sakawa kaina ba, babu abunda zai sa wani ya ci mutumcina ya ci min zarafi a gaban mahaifana, and mahaifine mutum ne mai dattako da mutumci ko kadan baya son yaga iyalansa suna aikata wani abu na zubar da mutumci, and Daddy yana da gaskiya Zina ba abun kwarai ba ne Malika shiyasa muke boyewa idan muna yi, kuma muke gudun a ji ko a gani, ya kamata ni da ke duk mu tubar ma Allah"

Zuwa tai ta zauna kusa da shi ta kai hannu ta shafa bayansa.

"Baka da bukatata?"

"Idan nace bana bukatarki na yi karya, domin ni namiji ne kuma mai lafiya da kwanciyar hankali, amman zan yi kokarin kawar da wannan mummunar dabi'ar a tare da ni. Bana son na tsallake wata uku ban yi aure ba kamar yadda mahaifina yai alkawari, ni kaina ina bukatar auren domin samun salama da kuma kare kaina daga Zina"

"Sadam be kamata mu daina yanzu ba, akwai masu aure da yawada suke yi kuma zina fa ba wani abu bace yanzu ta zama yayi yana da wahala ka tararda saurayi ko mai aure baya yi, bayan haka kuma zamu iya rokon Allah yafiya idan mun aikata kasan Allah mai yawan yafiya ne kuma mai jinka, in yaso duk safe sai mu yi istigifari kenan"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now