page 2

4K 308 13
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 2*

Shafa kumatun Bintu Hajje tayi cikeda tausayawa kafin tashiga bata labarin asalinsu ta bangaren mahaifiya....

Sunana Khadija kaman yanda kikasani sannan in zaki shake ni yanzu infada miki kamannin iyayena bazan iya ba abunda kadai nasani shine nataso marainiya banida Uwa banida Uba, kawai dai nataso nayi wayau nakuma tsinci kaina agidan marayu ne inda muke rayuwa da yan uwana marayu wanda suma sun rasa nasu iyayen kaman ni. tunda nayi wayau nakeson sanin asalin iyayena dukda kuwa nasan mutuwa sukayi to anma yakamata ace sunada dangi aikoh?Miyasa su yan uwan iyayena bazasu daukeni ba zasu bari akawoni orphanage wannan dalilin yasa watarana naje na tamabayi one of the care takers dinmu dayake tanada saukin kai batada matsala bataki fadamin ba don Itama tajima ah orphanage din sosai cemin tayi Khadija nikaina bazan iya fadamiki dalilin dayasa yan uwanki basu raineki ba tunda bawai zuwa akayi akayi handling dinki garemuba hand to hand,A'a zuwa akayi aka ajiyeki da dare wanda kukan kine yafito damu daga dakunan mu har muka kawo miki dauki hakanan alokacin ba irin bincikeda ba ayiba acikin Maiduguri don gano dangin iyayenki amma shiru sabida kinsan wani sa'in akanyi kidnapping Yara akawosu,but one thing I'm sure of shine ke asalin Yar Maiduguri ce Khadija,kallo daya kowa zaiyi miki yasan ke shuwa ce........

Goge kwallah na nayi sannan nace "akaini Maiduguri to mana Aunty inyaso se in nemi dangi na" Murmushi irinna manya matar tayi sannan tace "A cikin garin Maiduguri kike Khadija so basai kinje ko'ina ba nidai shawarar dazan baki kicigaba da addu'a kawai Allah ya bayyana miki iyayenki insuna raye"
Nace Mata

"Amin ya Allah"

wato alokacin ma nibanmasan awani gari nikeba tunda bafita mukeyiba inbawai takama ba. Haka nacigaba da rayuwata acikin gidan marayu harna manyanta nayi Primary school amma banyi Secondary school ba sabida gwamnati bawai tana funding dinmu yanda yadace bane ba sannan tunda nagama Primary school ake koya mana sana'o'i during our free time harnakai shekaru sha shida to awannan lokacin ne nafarayin samari don inada farin jini fiyeda yanda kike tsanmani Bintu dukdama bansan dalilin farin jinin nawa ba shin kyaun da Allah ya zuba min ne kokuma baiwa ce daga Allah?.....
Only God knows......
Dakyar na amince da mutum daya *Sadiq* wanda yana matukar Sona awannan lokacin kuma shima maraya ne kaman ni sede yagirme mini dakusan shekaru goma,yana sana'an shi dede gwargwado yanakuma samun na kashewa wanda inada yakinin in mukayi aure to tabbas zai iya rikeni da yardar Allah,kwatsam sega wani Alhaji yazo kawomana taimako anan yaganni wai yanaso nanuna ni inada wanda nakeso anma dayake shidin mai power ne sannan yana yimana taimako sosai yasa care takers dinmu suka takuramin lallai lallai saina aureshi haka aka rabani da Sadiq aka auramin Alhaji Yakubu. At first kaman mutumin kirki daga baya kuma yacanza zuwa mugu,laifi kadan zanyi mishi yakai hannu yace zai dukeni in takaice miki zamana agidan Alhaji was like living in hell,banida sukuni banikuma da kwanciyar hankali sau biyu ina kaiwa kararsa orphanage dinmu anma akaki daukan mataki ganin cewa afuska shi mutumin kirkine bugu da kari gani sukeyi inaso inraba auren ne sabida bana sonshi shiyasa nake making excuses haka nakoma nacigaba da zama dashi ammafa babu abunda yacanza sema wanda yakaru gashidai mai kudi amma abincima saiyaga dama yake bani harna samu ciki amma baidaina dukanaba wannan dalilin yasa nayanke shawarar guduwa inbarshi don bazai yuyu inhaihu 'yata tataso cikin kuncin rayuwa ba haka nashirya duk wasu abubuwan dana tabbatar zan bukata sannan nadauki duka gold da akasamin ah lefena naje nasaida su akasuwa nadawo da kudin washegari da asuba bayan yafita masallaci nafice nabar gidan se park nikaina bansan inazanjeba awannan lokacin all i know is I want to be far away from Alhaji Yakubu,park nawuce which was my first time going there Ina isa masu samo passengers suka shiga tambayata inda zani suna irgo min sunayen garuruwa anan ne natsinci sunan gari Damaturu dasauri nace Damaturu zani.......
Cikeda farin cikin yasamu passenger mutumin yace "Yauwa Hajiya biyoni" haka nabishi muka yi wurin wata rakwababbiyar mota banwani jima agurinba Motar tacika kafin muka kama hanya nidai zuciyana nacikeda tunani kala kala daban masan sanda muka shigo gariba sema jidanayi motar ta tsaya nan kowa yafara sauka nima sauka nayi aka fitomin da kayana daganan kuma yan napep suka shiga zuwa suna tambayana "Hajiya inazakije?".......

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now