Page 6

3.2K 270 7
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 6*

*ASALINSU*

Alhaji Ibrahim Aliyu Tumbido asalin Fulanin Yola ne wanda duk danginshi sunacan,babban family house garesu kuma sananne don kuwa kaf cikin garin Yola babu wanda baisan Familyn Tumbido ba sabida kudinsu,nagartarsu dakuma halin girma da Allah yayi musu. Ibrahim Aliyu Tumbido tunda yagama jami'arsa a Oxford University yadawo gida inda ya karanci Architecture and alhamdullah da result yafito yasamu yanda yakeso wannan dalilin yasa yafara shirye shiryen tafiya service inda suka turashi wani Construction industry anan garin Damaturu,daman construction industry din na wani Babban mutum ne a Yobe. Kanuri ne inda yaji dadin aikida Ibrahim sabida kwazonshi dakuma sanin yakamata irin nasa shiyasa koda yagama service Industryn ta roki yayi aiki dasu seda yakoma gida yayi shawara da iyayensa sannan yayi accepting offer dinsu and that was the begining of his success. Ibrahim mutum ne da Allah yayi mishi baiwa irin na zane he's a great artist da inya zana abu seka rike baki kana mamaki shin abun computer sketch ne kokuma hannu ne yazana to wannan baiwa nasa shiyayi leading nashi to so many successes dayasamu a rayuwa dan ko industryn dayake aiki dasu jisukeye dashi kaman mi don duk wani project na gine gine kokuma contract in aka basu to shi suke daurawa akai shima kuma he never failed them sabida suna biyanshi yanda yakamata ahaka ne har suka fara soyayya da 'Yar me industry din Maryam kyakyawa da'ita daka ganta kaga mahaifinta,sunason juna fiye da yanda alkalamina zai rubuta hakanan suna mutunta juna and they're both ready to spend the rest of their lives together shiyasa babu bata lokaci da amincewar Maryam din Ibrahim yaturo iyayenshi gida akazo akayi tambaya aka basu aka kuma sa rana a take kasancewar anriga da ansan juna babu wani further bincike daza ayi it's just like a family wedding ma. Bayan Auren Maryam da Ibrahim suna zaman lafiyansu sede dan abunda baza arasa ba kunsan ance zomu zauna zomu saba, problem dinsu daya rashin haihuwa donkuwa shekararsu biyar suna tare anma Maryam ko batan wata bata taba yiba wannan dalilin yasa hankalin Maryam yatashi dukda kuwa surkanan ta basu taba nuna damuwar su akan hakan ba to anma ita tana ganin dole wataran zasu fito suyi magana kilan yanzun kawaici sukeyi dukdama haihuwa na Allah ne anma aibakowa ke gane hakan ba?wani dare Maryam tasamu Ibrahim da zancen tanason suyi adopting Baby from the orphanage dubanta yayi sannan yace "Maryam what's the rush for? Komai lokaci ne,I just believe that lokacin haihuwar takine baiyiba inlokaci yayi zaki haihu in Allah ya yarda" murmushin dayafi kuka ciwo tasakar mai sannan tace "Nasani Dear I just need someone by my side,inason Inga ina rike little Baby like every Woman does koda kuwa lokacin haihuwar nawa ne baiyi ba nibanga aibun dauko maraya ba besides inmuka rikeshi lada zamu samu Ibrahim"
Rike fuskarta yayi ganin tadamu sannan yace "Toshikenan zamuje muyi adopting din kada kitada hankalinki please" Cikeda jin dadi ta rungume shi tanayi masa godiya atleast ko Allah baibata haihuwa ba she'll have someone dazata kira amatsayin 'Danta ko 'Yarta hakanan tasan babu mai budan baki yayi mata gori. Cikin weekend suka je sukayi adopting newly born Baby Boy dako sati ba ayiba da kawoshi orphanage din nan suka cika duk wasu formalities as his new parents suka kuma dau alkawarin rikeshi amana kafin suka wuce Yola sukayi introducing nashi to the family members and Alhamdulillah yasamu karbuwa gurin danginsu don Tumbido dakanshi yazaunar da duka familyn nasa aka bude taro da addu'a sannan yadubi Mami dake zaune gefe hannunta rike da yaron yace "Maryam miko min yaron nan"
Gyadamai kai tayi cikeda ladabi sannan tadaukeshi tamika ma surukin nata dakanshi yayi masa huduba da Muhammad sannan yashiga jadaddama ahalin nasa kan kada ayarda a nuna ma yaronnan banbanci kokuma yaji wataran ana fadin shidin ba jininsu baneba yace "Daga rana mekaman tayau kusaka ma ranku cewa Muhammad jikana nane kaman sauran jikokina don har cikin raina nakejin yaronnan is a blessing to our family so duk wanda yayi tunanin wulakantashi ko tozartashi to bashi yayiwa ba niyayiwa tunda nine Kakansa"

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now