page 16

2.5K 281 53
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert@wattpad*

*Page 16*

Ita babu abunda yafi daga mata hankalima irin cewa da akayi su tattara subar unguwar zuwa gobe. ina zasuje? wasuka sani? waye sukedashi dazai iya taimakon su? wadannan sune tambayoyin dasuka shiga yimata yawo akai. Family biyu kadai tasan she can rely on agarin nan wanda sudinma ayanzu bazasuyi mata anfaniba tunda Mallam isah mai napep da Matarsa Rashida ma sunjima da barin garin Damaturu sekuma Yusra kawarta datake makaranta yanzu,da ace tana gidane ma zata iya sanar da'ita dukdama wata zuciyar na yunkurin hanata because Yus ra has done a lot for her family bata tunanin zata kuma sake daura mata wani nauyin kuma.

Haryanzu tana dafe dajikin ginin wanda yazame mata makari sabida irin juwan datake ji kuma haryanzu tanajin surutan mutane akanta dukda yanzu yafara raguwa ma'ana mutanen sungama tsegumin su sunfara komawa muhallinsu. Jitayi andafa kafadarta wanda hakan yasata dago kanta daga jikin ginin tadubi Yar uwartata da'itama idanunta fal suke da hawaye,rungumar juna sukayi hakanan sunajin tausayin junansu dasauran yan uwansu dakyar Khadija tayi karfin halin jan hannun Bintun suka yi hanyar cikin gidan wanda alokacin har anfara kiraye kirayen sallar maghrib,abakin kofa suka tarar da Amir da Ilham na nasu babin kukan cikeda tausayin su Khadija tashafa kansu tana fadin "mushiga gida maza. everything will be alright insha Allah" Amir dayafi Ilham wayau yace "Toh inazamuje Yaya Khadija? muda bamuda kowa agarin nan inasukeson muje don Allah?".....

"Shhhhhhhhh Amir" wannan shine abunda Khadijan tafada kafin takarada banace maka komai zaizama tarihi ba insha Allah,ya gyada matakai ahankali sannan tace "Toh maza kaje kayi alwala kawuce masallaci kada karasa jam'i" yace "Toh" kafin yafice.
suma sallar suka wuce sukayi duk rai ajagule hakanan cikin su babu wanda yabi takan abincin da Khadijan ta dafa dan gwanda ilham ma taci kadan.

Bayan maghrib kuwa sega Mamman Noor nan yadawo hankali tashe don tundaga hanyar shi nadawowa yasamu labari wurin abokin shi Haruna. zama yayi gaban Bintu dake zaune kan sallaya tana adduo'inta yace "Yaya Bintu wai meyake faruwa ne, yanzu Haruna yatareni yana fadamin wasu labarai daban gane kansu ba" itadai bata cemai komai ba sema kallonshi data tsaya yi gabadaya batada strength din maimaita ma wani abunda yafaru ma Amir dake gefene yamaimaita mishi abubuwan dasuka faru,salati da salallami Mamman yashigayi kafin yace "It's all his fault. shiyasa akullum nake ce miki kidaina bama mutumin nan fuska gashi yau yajamana kora agidnnnan,Ina zamuje? wamuke dashi dazai taimake mu. yayi tsaki "ni bantaba ganin mahaifi irin namu ba, parents are always there for their children anma namu mahaifin sede ma ruguza mana rayuwa dayakeyi akullum,wallahi konayi rantsuwa bazanyi kaffara ba Yaya Bintu. indai zamu bar unguwarnan tomu kadai zamuyi tafiyarmu babu inda zaisake binmu bare har yasake causing mana wasu problems and believe me this time maganar ki bazatayi tasiri agurinmu ba" daganan Mamman yatashi yasake ficewa agidan yana huci kaman zaki binshi da idanu Bintu tayi inda ta tsinkayi Khadija nafadin "nima Ina bayan Mamman dan dabaiyi causing commotion din yau ba babu abunda zaisa akoremu ah unguwar nan besides he has been a burden to our lives so it's better we let go of him". batareda Bintu tace da Khadija komai ba tatashi tana share hawayenta tayi cikin gida sabida tasani tabbas intace zatayi magana bazasu kwashe ta dadadi ba but one thing is for sure duk inda zasu saka kafarsu to tabbas mahaifin su nabiye dasu..

★★★
Tunda yabar gidan yake mamakin wannan al'amari dayafaru. towaishi laifin mema yayi? Is it a sin don yatsaya yana magana da Bintu akofar gidansu? atunaninshi she's old enough ace anhanata fitowa hira da samari kansu bareshida ba hiran yaje guntaba. duk wani tunani dayayi dan gano inda laifinshi yake abun ya faskara samun gefen titi yayi yayi parking motarshi tareda sakin wani wawan ajiyan zuciya. kallon mirrorn gaban motar shi yayi yana karema fuskarsa kallo duk ya kumbura yayi jaa dashi. shikanshi yasan ko karen hauka ne yacijeshi bazaije gida gurin Mami haka ba dan haka yayi reverse yatada motar yanufi gidansu Hamza.

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now