Page 20

2.9K 300 45
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 20*

*Not edited. So overlook typing errors please*

Tsayawa sukayi itada Mamman suna Jin abun al ajabi yayinda acan cikin dakin kuwa ganin yaki tsayawa ko allurar suyimai dazaisa yasamu yakoma bacci yasa likitan yayi deciding su daureshi jikin gadon kawai. ai Mami naganin haka tayi hanyar kofar dakin cikin kuka tana fadin "ita karsu daure mata 'Da don Allah. Danta ba dabba baneba" dakyar Daddy yarikota yanabata hakuri hakadai aka daure Mu'azzam jikin gadon akasakeyimashi wannan allurar dan that's the only solution to his problem dai ayanzu sanda likitan yafito samun Daddy yayi yana tambayarsa kosunyi magana dawancan likitan nan Daddy yacemasa sunyi magana and he's sending some drugs and allurai gobe insha Allah.

Gyadakai likitan yayi sannan yace "I thought bakuyi magana bane dasai ince I'm afraid you've to transfer him to *Neuro psychiatric* dake nan Maiduguri may be they can know the actual problem and have a solution for it anma tunda yace zai aiko magani mujira mugani zuwa goben" "toh" kawai Daddy yace mai sabida he can't believe the thing has gone to far dahar za'ace sukai Mu'azzam Neuro psychiatric likitoci suduba shi acan wanda yanada tabbacin indai sukaje can ya tsandara wannan ihun cikin mutane sede adebeshi akai dakin marasa hankali to which shikuma bazai taba barin haka tafaruba...

Bintu ganin komai yadan lafa agurin yasa tacema Mamman sukarasa gurin,Mama suka fara gaisarwa wanda ta ansa musu sama sama sabida irin tashin hankalin datake ciki Mu'allim dake gefen Mama zaune ne yadago yadubesu sakamakon jin familiar voice din dayayi. hada idanu sukayi da Bintu cikin sauri yamaida kanshi kasa dan bayason taga halin dayake ciki sede abunda baisani ba Bintun tariga taga komai taga yanda idanunshi sukayi jazir suka canza launi,sunwani kankance gwanin ban tausayi da alama ma yajima baici ishasshen abinciba tareda samun kwanciyar hankali ahankali takarasa ta dayan bangaren dayake tatsuguna gefen kujerar tana gaidashi "Ina wuni Yaya Muhammad?" cikin raunanniyar muryarshi yace "Lafiya Lau Zahra" tace "Yamai jiki kuma?" "Dasauki" yayi maganar muryarshi na cracking wannan lokacin cikeda tausayinshi tace "Allah ubangiji yabashi lafiya" yace "Amin" sekuma sukayi shiru dukansu yayinda kowa ke sake sake cikin ranshi. shiyanason yayi mata fadar miyasa tafito da dare bayan tasan is not safety while Itama tanason tafada mai kalaman dazaisa yaji sanyi aranshi,kalaman dazasusa yasamu courage yakarbi kaddararkanin sa hannu bibbiyu tareda sannan yagane komai wuya akwai dadi anma batada courage din fadamai wannan din dan hakanan taji bakinta yau yayi nauyi. Mamman karasowa yayi yagaida Mu'allim din damai jiki wanda alokacin har Mama tatashi tashige ciki abunta Dan already su Mami ma sunjima acikin dakin da Mu'azzam din yake. Jin shirun yayi yawane yasa Mamman tambayarsu Mami kan sunason sugaisa dasu tashi Mu'allim yayi "suna ciki ba inyi musu magana" cikin sauri Bintun ma tatashi tana A'a kabarsu kawai wataran mwa dawo mugaisa babu musu yace Toh dan Allah yagani bayason su Bintun suga halin da Mu'azzam din ke ciki abunda baisani ba Bintu tariga data gama ganoshi dan sanda take tahowa gurinshi takalli direction na Window and that's when taga yanda aka daddaure Mu'azzam din. haka suka ajiye mai fruits din dasuka kawo sukayimai sallama suka tafi dukda yace zaisa driver yayi dropping nasu off anma sukaki kwata kwata ganin Bintun na tareda Mamman yasa baitakura musu ba.

Yauma Abba abuge yashigo musu gida yagama babatunshi yawuce daki babu wanda yakulashi dan kuwa tun washegarin daya dawo gida yakoma halinshi nada Bintu kuwa yanzu tarage tada hankalinta dangani takeyi bashine solution ba addu'ar shiryuwa dai bazata daina yimashiba insha Allah. yanzuma tana kwance gaba daya abun duniya yadameta data rufe idanunta fuskar Mu'allim data bari ah asibiti da kaninshi dake kwance helplessly take gani,watodai shi rayuwar nan duk yanda Allah yayika ka gode mishi dan bakasan irin baiwar dayayimaka ba gashidai familyn Tumbido babu abunda suka rasa arayuwarsu inbanda rashin lafiyar Dansu daya ruguza musu duk wani farin cikinsu na rayuwa. ranar dakyar tayi bacci hakanan washegari batafita aiki dawuriba kasancewar batada wasu ayyukanyi sosai.

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now