page 12

2.6K 267 16
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 12*

Yanda yarike ledan kaman wani kashi seya kusan baka dariya yayinda yake yatsina fuska sannan kaman me tsoron leda yashiga kaiwa kusa da hancinshi sanda yaji kamshin nama bakaramin wara idanu yayiba sannan yadubesu "Ina nawa?" Bintu tace "Kayi hakuri Abba gobe zansaya maka" yana shirin korafi seyayi sululu yafadi agurin alamar bacci tayi awun gaba dashi tsaki Mamman yayi yana fadin "Better because I can't stand this Man" hararanshi Bintu tayi kazo ni kadaga shi kashigar dashi ciki anma Mamman seyayi kaman baijita ba girgiza kai tayi cikedajin haushin kanin nata kafin takoma takwanta don tasan itadaya kam bazata iya dagashiba shi Mamman dinne dayaga ran Yayartasu yabaci daga baya yatashi yashiga dashi cikin dakinshi.

★★★

Mu'allim yana office har bayan isha'i kasancewar ayyuka sunyi masa yawa gashi haryanzu sunata samun matsala da clients dinsu,sunki basu hadin kai kwata kwata due to abubuwan dasuka faru months back,gani sukeyi companyn will fail them again gabadaya Mu'allim yarasa abunyi. Yananan office dinshi zaune wayarshi tashiga kara dubawa yayi Hamza ne ke Kira don haka yadaga cikin sauri yace "Hamza yaushe akasar?" Don yaga da numbersa ta Nigeria yakirashi. Dariyan Hamza yayi sannan yace" yaushe agari dai dannikam inacikin Damaturu ma yanzu haka" cikeda zumudi Mu'allim yace"Really! shine baka fadamin zuwarka bako?"....

"To Mallam yimin iyayi kaji. kaida ba'a gane kanka kwanan nan dan rabon damuyi chats ma harna manta"cewar Hamzan dan hargitsa suman kanshi Mu'allim yayi  yace"kabari kawai Hamza aiyukane suka sakani agaba wallahi shiyasa" dariya Hamza yayi sannan yace "Allah yataimake" yace "Amin" kafin yakarada "yaushe zaka lekoni to?".....

"Gobe Saturday ko?" Cewar Hamzan gyada mishi kai Mu'allim yayi kafin yace masa zaizo gida yasameshi goben daganan ma sesu gaisa da Mami don sun kwana biyu basu hadu ba Mu'allim yace"Allah yakaimu sekazo Hamza". Se after 9:00pm Mu'allim yabar office shima dan Mami tadame shi da kirane kan yadawo gida. Sanda yashiga katafaren parlourn nasu Mami nazaune kan Sofa yayinda hannunta ke daukeda remote din TV tana kallo harta fara gyangyadawa tsabar zaman kadaici gashi daman bawai tasaba hira da masu aikinta baneba duk inda dare yayi dakinsu suke wuce su huta kafin washegari kuma. Jin motsin mutum ne yasata bude idanuwanta tadubeshi tace "Son seyanzu?" karasawa yayi inda take tareda zama gefenta sannan yace "I'm sorry Mami wallahi ayyukane sukamin yawa kwanan nan shiyasa bana dawowa dawuri" shafa fuskarshi tayi ahankali tace "Ayyuka daman suna karewa ne Mu'allim? besides dare mahutan bawa ne don Allah duk inda kaga dare yayi kayi kokari kadawo gida inkuma zaman yazama dole ne kakira kafada min kaji?" Yace to Mami insha Allah zangyara. To tashi muje kaci abinci sekayi wanka ka huta ko? Yace "toh caring Mami na" dariya kawai tayi sanda suka isa dinning table din shiya zuba musu abincin suka ci tare don itama bataciba kafin suka kira su Daddy sukayi hira sosai gwanin ban sha'awa kafin sukayi sallama da juna sanda Mu'allim yaraka Mami daki tace"Son gobe ba aiki ko?" Gyada matakai yayi alamar eh kafin tace "yauwa zakakaini gidan Mama nakwan biyu banjeba" cikeda jin dadi yace "Yauwa Mami daman banason zuwa nikadai sabida korafin tsohuwarnan " batarai Mami tayi "mahaifiyar tawace keda korafi?" Cikin sauri yace "Sorry Mami kema kinsan Mama se ahankali" tace "aiko sena fadamata ina maganar aure ne da takeyi maka bakaso?" Sunkuyar dakai yayi kasa kamar wani marar gaskiya dariya tayi sannan tace "ai Daddyn ku nadawo zan zugashi yanemo ma yar kauye adaura kawai" pity face yayi haba Mami na, Mu'allim dinki ne fa tace koma wayene nidai ba ruwana murmushi yayi sannan yayi mata saida safe yafice.

Washegari Hamza  yazo dasafe sukayi breakfast tareda Mami da Mu'allim din cikeda farin ciki Mami na fadin "Hamza yauka tuna da Mami kenan" dan sosa kanshi yayi cikeda kunya kafin yace "Aa Mami bana garine da inanan aiharsai kin gaji da ganina" tace "waya fadama Uwa nagajiya da ganin Danta?" Murmushi kawai yayi sanda suka karasa cin abincin sannan Mu'allim da Hamza suka baje ah parlour suna jiran Mami ta shirya wuraren goma da rabi nasafe suka bar gidan kafin suka nufi gidan Mama dake extension na *Obasanjo estate* yayinda su daman ah *Redbricks* suke so da dan nisa tsakaninsu. Sanda suka isa unguwar gaban wani katafaren gida Hamza yatsaya  tareda yin horn daman da motarsa suka fito. bai jima dayin horn din ba  sega mai gadi ya leko don ganin wanene kafin yakoma ya wangale musu gate din fuskarshi daukeda murmushi.

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now