page 4

3K 395 17
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU*🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad...

*Page 4*

Seda suka gama feeding juna shida mahaifin sa sannan Mami tajashi zuwa dakinshi dake can sama,wanka yayi yasauya kaya zuwa na bacci sannan yazo yakwanta tareda makurewa guri daya lokacin ne kuma Mami da Daddy suka shigo dakin suma zasu wuce nasu dakin su kwanta shine suka zo suyi mashi saida safe, murmushi Mami tayi tareda kissing forehead dinshi ahankali tace

"Good night Son"

Gyada mata kai yayi yana murmushi,thesame thing Daddy yayi mashi kafin suka zauna dukansu kusa dashi,Daddy nazaune kan bedside drawer dake kusa da kan Mu'azzam din yayinda Mami ke zaune gefenshi akan gadon har bacci menauyi yayi awun gaba dashi wani irin ajiyan zuciya Mamin tasauke sannan tadubi Mijinta tace
"Muje mukwanta tunda yayi bacci"
Daddy yace "To Mamin Mu'azzam" yatsina fuska tayi playfully kafin tace "zaka farako?"
Dariya yayi kafin yaja hannunta suka fice zuwa dakinsu wanka sukayi sukayi shirin kwanciya dukansu biyun. Mami ne tafara kwanciya ta lulluba abunta tareda lumshe idanu yayinda Daddy kezaune a bakin edge din gadon yajuya mata baya yana tunanin duniya jin bataji motsin yakwanta ba yasa tabude idanunta ahankali tace "Dear tunanin me kakeyi?"
Cikin sauri yace "Na'am Maryam?"
Jin yakira sunanta yau din yasa tasan abun serious ne don haka tatashi zaune yayinda yajuyo gareta shima cikeda damuwa tace "What's wrong Daddynsu Muazzam?"
Kai tsaye yace "Babu" cikin sauri tace "Aa karkama cemin babu inbaka fadamin damuwarka ba wazaka fadama Ibrahim?" murmushin karfin hali yayi sannan yakamo hannunta cikin sauri takwace hannun tana fadin "Kadama kamin dadin baki kafadamin meyasa kake tunani?" dukyanda yaso yakiyin dariya seda yayi looking at her reaction......

Batarai tayi inda yajata jikinshi yana "Kiyi hakuri zan fada miki uwar azarbabi"
"Eh naji kaidai fadamin"
Dagowa tayi tana kallonshi tanajiran jin mezai fada cewa yayi "Kinsan mutanen nan sunkirani dazu?"
Cikeda curiosity tace "wasu mutane kuma Dear?"........
Ahankali yace "London. sunason susake bama Mu'azzam wani project wannan shekarar ma wai sunyita kiran layinishi baidauka ba haka sunkira office dinshi ba'adagaba,sun tura mai mail almost a week back anma baiyi musu reply ba and they need him urgently shiyasa nisuka nemeni suka fadamin suna tambayar inayake ko lafiya. Nadai ce musu yananan lafiya Lau I'll get back to them soon shine gabadaya kaina yadaure Maryam,bansan wani mataki zandauka ba" Tunkan yarufe baki Mami tace "He's going nowhere Dear kafadamusu sunemi wani yayi musu Mu'azzam bayida wannan lokacin" Daddy yace iyasa zaki yanke shawara dawuri haka Maryam?"

Atake idanunta suka ciko da kwallah don inta tuna abunda yafaru last year wani irin kututun bakin ciki da karayar zuciya takeji, ahankali tace "so kake insake tura 'Dana kasar da bashida dangin iya bare na Baba?So kake intura shi yasake gamuwa da kaddarar data fadamai wancan shekarar komi?" Ta numfasa sannan takarada "I'm not that selfish Ibrahim. Sonda nakeyima Mu'azzam yafi success din danakeso yasamu arayuwa besides health comes first,so he's going nowhere" dafe kai Daddy yayi ganin tarikicemai lokaci guda daman yasan za'arina shiyasa baiso fadamata ba,yasan tabbas she'll be stubborn shiyasa yaso yafara magana da Mua'allim tukunnan duk shawarar dasuka yanke se ayi ta donshi kanshi ayanzu baisan miye decision dinshi ba yanason Mu'azzam yaje anma inya tuna implications din ciki seya karaya gabadaya. Ahankali yashiga rarrashin Mamin da fadin kikwantar da hankalin ki nima inason Mu'azzam equally bazan taba yin abunda bazai anfaneshi ba,cikin kuka Mami tace "Nidai babu inda zashi kabarmin 'Dana kusa dani"
Cewa yayi "Toh shikenan naji Maryam,kiyi hakuri kidaina kuka babu inda Mu'azzam zaije shikenan?"
Gyada kai tayi tana shesshekar kuka ah kirjinshi dakyar yasamu ya rarrasheta hartayi bacci yayinda shikuma yakasa assala komai gabadaya tunanin duniya ta isheshi daga wayarsa yayi yaga karfe daya da rabi he's very sure Mua'allim yayi bacci  by now so bazai kirashiba se gobe kawai daganan yatashi yashige bathroom yayo alwala sannan yazo yatada sallah yana mikama Allah kukanshi.........

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now