page 15

3.4K 283 39
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Alhamdullah The Moon 🌕 has been sighted and it's declared that Fasting and other forms of Ibadah will be starting tomorrow insha Allah🥰  So, Ramadan Kareem to all the Muslim Umma around the globe,inafatan yanda aka za afara damu lafiya Allah yasa muga karshensa lafiya, Allah ubangiji yasa mudace cikin wannan wata mai albarka, Allah yasa muna cikin bayin dazai 'Yanta,ya Allah kakawo mana karshen wannan cuta data addabi duniya baki daya badan halin mu ba🤲*....

*Amin ya rabbi*

*Sannan inason insanar da fans dina wannan shine last post dina na RAYUWAR BINTU ayanzu harsai bayan Ramadan in Allah yakaimu,yasa munada rai da lafiya zamu dora daga inda muka tsaya. Allah ubangiji yasa mudace*

*Page 15*

Tafi minti uku tsaye gurin batareda ta motsa ba hakanan tana mamakin irin kirkin Mu'allim din wanda ayanzun har hakan yafara bata tsoro. jitayi wayarta tashiga kara wannan dalilin yasa ta motsa tadubi wayar Mu'allim dinne ke kira jiki sanyaye tadaga jitayi yace "bazaki fito bane kosai na sake doubling punishment din?" murmushi tayi sannan tace "Ina zuwa Yaya Muhammad" nan ta katse wayar tareda ficewa daga harabar office din ah mota tasamesu ya hakimce ah baya yanata danne dannen waya abunsa wannan dalilin yasa tabude gidan gaba tashiga abunta kafin Mallam Shamsu ya tada mota. har kofar gida suka kaita kafin tayi musu godiya tashige gida abunta. Tofa haka kullum Mu'allim inya tashi tafiya zece da Mallam Shamsu subi ta gidansu Bintu adauketa sannan dawowa ma tare sukeyi,sesun ajiyeta sesu wuce gida shida drivern shi hardai natsawon kwanaki uku,aikuwa wannan yawan jele da Mu'allim keyi ah unguwar yajawo hankalin jama'ar unguwa suka fara gulmace gulmace kan Bintu nason 'bata rayuwarta sabida kakarta tarasu tafara seducing maza 'Ya'yan masu kudi da kyaunta dan tasamu kudin ciyar da kanta dakuma kannenta kunsan mutane dasa ido gakuma judging mutane without a genuine evidence haka,dukdama su haryanzu maganar bata zagayo kunnensu ba barema susan halin da ake ciki. yau Friday tunda Bintu tadawo daga aiki takejin wani dadi na musamman inta tuno gobe babu fita aiki because the week has been so tiring atleast gobe da jibi tasamu ta huta without any worries...

Da dare suna kwance ah tsakar gida Khadija tace "Yaya Bintu kayan abinci yakusa karewa fa koma ince yakare don shinkaface dabaifi kwano biyu ba da taliya biyar kadai yarage mana agidan,dan ajiyan zuciya Bintu tayi sannan tace "semuyi ta managing dashi tunda cikin sati mai zuwannan za ayi mana salary in Allah ya yarda" da mamaki Khadija tace "haba?" Bintu tace "wallahi. haka naji su Ibrahim nafadi" cikeda damuwa Khadija tace "to anma ke za'a biyaki kuwa? naga bakijima da farayi musu aikinba?" "koma basu da niyar biyana dole zanroki Yaya Muhammad abani koda na iyakacin aikin danayine tunda we really need the money barema kuma bana tunanin bazasu bayardin ba"   Khadija tace "Allah yasa subayar din" suka amsa da "Amin" dukansu biyun kafin suka canza hira kuma.

Washegari dasafe Mamman Noor da su Amir suka shirya tsaf suka fice inda zaisauke su Ilham da Amir din ah islamiya shikuma ya wuce garrage yayinda sukabar 'yan matan agida, bangaren Bintu kuwa harsuka fice tana bacci bata tashiba daman tunjiya ta kashe musu warning kada kowa yatasheta da safe because tanason tayi bacci.

Tun bayan tafiyarsu Mamman Noor Khadija ta tattaro kayan wankin ta tahauyi sabida daman sun taru cikin sati shiyasa tayi deciding tayi yaudin tunda babu makaranta,seda tagama tsaf sannan tahau gyaran gidan tashare ko'ina tayi wanke wanke sannan tayi wanka tasaka normal kayanta dashirin tashiga makotarsu wurin kawarta Zainab tayi mata tayi mata kitso. Tananan zaune taji kamar tsayuwar mota ah kofar gidan anma bata damuba ba ajima ba kuma taji kamar anayi musu sallama da mamaki tazari hijabinta tasaka sannan tafice daga varender ta tsaya sannan tace "waalaikumus salam ka shigo mana" daga labulen da akayi kofar dashi Mu'allim yayi sannan yashigo fuskarsa daukeda murmushi yayinda yake sanye da kananun kaya yau ajikinsa kuma sun amshi jikinshi babu laifi,mamaki sosai Khadija keyi ganin wannan farar halitta mekuma zati da kyaun gani ah gidansu dakyar tayi karfin halin cewa "Ina kwana" Mu'allim ya amsa da "lafiya lau,yakike?" Itama cewa tayi "lafiyan" kafin sukayi shiru duka don shi kanshi yarasa dalilin zuwa gidan su Bintu without any reason itace tayi breaking silence din tahanyar cewa "bawan Allah sede bangane wanene ba?" Yace "I'm Muhammad. Boss din yayarku and I'm here to see her" ai Khadija batasan sanda tasaki murmushi ba hakanan muryarta tashiga cracking "au,ai laa sorry banganeka ba ai bismillah karaso mana" takarashe maganar tana kokarin shimfida mai tabarma ah varender babu musu yasamu guri yazauna akan taburmar yayinda tawuce kitchen tadebo mai ruwa ah tsaftataccen kwanon silver ta ajiye mai kafin tace "ba intashe ta bacci takeyi" cikin sauri yace "no karki tasheta nasan bazata jimaba zata tashi" da mamaki tadubeshi tanashirin yin magana sekuma ya katseta tahanyar cewa "Ina Mama inason mugaisa?"..

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now