Page 13

2.5K 290 24
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 13*

Tajima zaune kan kujerarta tana tunanin mafita dukda kuwa batasamun ba. Tayi nisa cikin zurfin tunaninta wanda hakan yasa yayita mata magana batareda tasan ma yanayi ba wannan dalilin yasa shi knocking table din dadan karfi wanda hakan yasata yin firgi git sannan cikin sauri tadubeshi,dan furzar da iska tayi "Aww Ibrahim kaine?" saurayinda aka kira da Ibrahim yasaki murmushi "wai tunanin me kikeyi haka?" tace "mekagani?" ajiye document yayi gabanta tareda cewa"najima tsaye inayimiki magana bakijiba. Anyways ga document dinnan kiduba zaitaimaka wurin organizing abun conference din daza ayi Monday insha Allah". Murmushi tasaki nagode Ibrahim yace "Never mind" kafin yajuya don tafiya cikin sauri tace "Yauwa Ibrahim inason inyi maka tambaya in babu damuwa". "Allah yasa nasani" shine abunda yace mata cikeda nervousness tace "batun companyn nan ne daman. tunda nafara aiki nayi noticing anasamun matsala". Ajiyar zuciya Ibrahim yayi kafin yakaraso inda take yace"karkidamu it isn't any of your fault" yayimata maganar fuskarshi cikeda assurance. atunaninta bazai boyemata komai ba sannan sunfi kusanci da Mu'allim kaf cikin employees din company din hakanan Itama cikin sati dayan datayi harsun saba sabida shi mutum ne me saukin kai da iya mu'amala da mutane shiyasa tayi masa wannan tambayar,ahankali tace "Miyasa kowa Inna tambayeshi seyacemin ba fault dina baneba?  inbabu fault dina to menene? I'm also his secretary indai anason asamu cigaba dani yakamata ace matsaloli ma za ana iya fada min because who knows ta'ina solution din zai bullo" wannan karan dariya Ibrahim yayi ganin yanda tayi kicin kicin da fuska gashi guiltiness din bebarta ba haryanzu dukda kuwa yacemata babu laifinta aciki. Jan seat din dake kusa da'ita yayi yazauna akai kafin yafara yimata bayani "Fatima kinga nima banjima da fara aiki a company dinnan ba inaga yanzu zankusa shekara biyu anma hakan bazaisa ince miki bansan komai gameda company dinnan ba tunda mahaifi na anan yayi aiki haryayi retire infact ni maisunan mahaifin Ogan mu ne shiyasa dana gama karatuna suka daukeni aiki". Yace "At first danazo dukwani abu da akasa gaba ah companyn nan turn out to be a success harzuwa lokacin da Yallabai yatafi London to daganan nefa komai ya tabarbare sabida rashin lafiyarsa" dasauri Bintu tace waye "Yallabai kuma?" Ibrahim yace "kanin Oga" gyadakai kawai tayi sannan tace "to anma miye yahada rashin lafiyar sa da aikin company kuma?" nan Ibrahim yabata labarin yanayin rashin lafiyar sa dukdama shi baisan sabida mace baneba shidai kawai yasan yasamu matsala ah kwakwalwarsa dayaje London shiyasa yafada mata abunda yasani kawai dakuma yanda abun yayi affecting company dinsu cikeda tausayin su Bintu tadan share kwallarta sannan tace "Nagode Ibrahim" tashi yayi tsaye yana fadin yanzu dai kinyarda bake bane cause na duk abubuwan dasuke faruwa ko? Gyada masakai tayi ahankali kafin sukayi sallama yatafi. dafe kanta tayi tana tunanin rayuwar duniya, ashedai duk kudinka da ikonka akwai abunda zai gagareka? ah tunanin ta duk wani mai kudi bashida matsala shida iyalansa,he has all that he wants ashedai suma Allah yana jarabtarsu ta duka hanyar dayaga dama. Like in the case of Mu'azzam daga shi har iyayenshi tasan babu wanda yataba tunanin abu haka zai faru dashi sede Allah dayafi komai yakuma fi kowa iko akanmu seya jarrabesu yaga shin zasu cinye wannan jarabawar ne koyaya?". Cire hannunta tayi daga goshinta tareda maida kanta jikin kujerar takwantar tana tunanin tayaya zata iya taimakon mutanen nan? Atleast if not for all of them,then for Yaya Muhammad sabida yayi mata abunda bazata manta ba,yanzu it's time for her to repay him besides inkomai yagyaru ma Itama she'll be of benefit infact bama itakadai ba kowama dayake aiki ah companyn don indai campany ta durkishe to tabbas kowama sallamarsa za ayi and insha Allah she won't let that happen! bazata bari talakawa irinta sukoma wahalar da sukesha ada ba don tasan dayawansu aikin nan shine survival dinsu dawannan tunanin tabar office din tatari napep tafada ma mai napep din unguwar dazai kaita hakanan tanacikin napep din tanaganin yanda gari yakaure da hadiri,yau kwana hudu kenan dasuke samun weather irin haka wanda akullum suna saka ran za ayi ruwa tunda taji wasu garuruwan anfara yimasu.

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now