page 9

2.6K 259 18
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad....

*Page 9*

Tsabar takaici Mamman besan sanda ya karasa gaban Mahaifin nasu ba sannan yasa hannu yafincike Standing fan din yana fadin "Ina sauran kudin sannan kuma awani shago kasaya don mayarwa zanyi tunda kai bakasan karike girman kaba". Bata rai Amadu yayi sannan yashiga kici kicin karbewa daga hannun Mamman din yana"bakada hankaline zakayi min irin wannan tambayar?".....
Mamman batareda yasaki standing fan dinba yace"Nidai nace kafadamin don ko baka fadamin ba senaje na sayar awani gurin dan wallahi bazan barka kayi anfani da fankar nanba, tukunnan ma inbanda rashin tausayi kudin sayan kayan abincin namu zakaje kayi shashancin ka dashi? to wai ma tsaya,daka siyo fan din dawani wuta zaka kunna ta? Mamman ya tsare mahaifin nasu da tambaya.....

Bintu cikin sauri ta iso garesu tana kokarin yakice hannun Mamman daga jikin fankar"kabari don Allah" daga mata hannu Mamman din yayi alamar tayi shiru sannan yace "wallahi bazan barmishi ba sena mayar kuma saiya bada sauran canjinma in akwai" ran Bintu abace tace "Kudin ka ne dazakace seka mayar?" Yace"koma nawaye ne sena mayar" hararanshi tayi "to semu gani ai tunda kai bakada kunya" daganan taja fan din dakarfi daga hannunsu duka tayi dakin mahaifin nasu dashi ta ajiye mashi sannan tafito Mamman na tsaye haryanzu yana huci tadubeshi tareda cewa"Kakoma bakin aikin ka tunda daman excuse kadauka" Amadu dake gefe dariya yayi tareda Ciro kudi ah aljihun sa yana nuna ma Mamman din yana dariya sannan yawuce dakinshi yana Fadin "in ansamu wani kudin kuma aje ah biyamana kudin NEPA inba haka ba nida kaina zandauka inje inbiya" azuciye Mamman yabi bayanshi dan jiyake kaman yarufeshi da duka cikin sauri Bintu tarikoshi tana fadin"Ina zakaje?" Hararanta yayi sannan yace"dakika barmishi fan da kudin mezamu ci agidan nan fisabilillahi?" Tace"Allah zaikawo" tsaki Mamman Noor yayi sannan yace"innace kina contributing to duk abunda Mutumin nan yakeyi mana wallahi banyi laifinba",yajuya zaifita tayi saurin riko hannunshi tana fadin"yazamuyi to Mamman, he's our Father try to understand"......
Kwace hannunshi yayi sannan yadaga shi yana nuna dakin da mahaifin nasu yashiga"Wannan ne Father? tonidai komi za ayi I'll never consider this useless Man as my Father. Mutumin dabaisan darajar uwarmuba tun tasowarsu mu bare mu,mutumin dabaisan responsibility dinmuba sede ma shi da yazama mana liability,mutumin da baison ganin cigabanmu sede downfall namu,mutumin da is selfish kanshi kadai yasani tayaya kikeson indaukeshi amatsayin uba Yaya Bintu?" Yakarashe maganar har jijiyoyin wuyarshi natashi tsabar bacin rai kafin yakarada"ko mahaifa sunkare ah duniya I'll never consider him as my Father infact yau daza acemin Amadu ba mahaifina bane i won't be surprise". wani irin wawan mari Bintu tasakar ma Mamman tana fadin "Mamman!! Are you out of your mind?"........

Sa hannu yayi ya dafe kuncinsa cikeda mamaki don Bintu bata taba daga hannu ta mare shiba seyau lokaci guda idanunshi suka canza launi yace"kiyimin duk abunda zakiyimin Yaya Bintu sede inason kisani hakan bazai sa incanza ra'ayina akan Mutumin can ba",daganan yajuya yafice rai bace. Bintu zama tayi ah gurin tana hawaye Amir da Ilham ne sukazo suna share mata hawayenta kallonsu tayi cikeda tausayawa sannan tace kutashi kufara shirin islamiya lokaci yakusa....
Amir ne yace"bazamujeba Yaya Bintu?".....
Tace"akan wani dalili?" Ahankali yace you're in pain,tayaya zamu tafi mubarki ke kadai sa hannu tayi tarike kumatunsa tanadan smiling dukda haryanzu hawayen baidaina zuba ba tace"Yaya Bintu will be alright kaji Amiru na?".....
Gyada matakai yayi sannan yasake sa hannu yana goge mata kwallarta kafin tajasu duka biyu tarungume su cikin jikinta jitayi Amir din nacewa"karkisake kuka Yaya Bintu insha Allah I'll read hard yanda zanzama billionaire watarana sabida inkula daku harda Abba yanda koya dauki kudi babu maidamuwa".

Batasan sanda ta saki murmushi ba jin kalaman kanin nata tareda cewa"Allah yabaka iko Amir" yace "Amin"...

Bayan suntafi islamiya Bintu nazaune ita kadai gabadaya tarasa mafita gashidai tasan babu yanda za ayi sucigaba da rayuwa haka dole in one way or the other sesun san yanda zasuyi sufara samun kudi,gashi yau dinma tun masar data siyo musu babu abunda suka sakeci su Amir din ma haka suka tafi islamiyar batareda sunci abinciba. Harsu Khadija suka dawo bata samu mafitaba suma kuma babu wanda yayi mata maganar yanajin yunwa kowani abu dai haka. Bayan maghrib sega Mamman hannu rikeda bakar leda Oyoyo Ilham da Amir sukayi masa yayinda Bintu tatashi tayi shigewarta daki dan satan kallonta yayi sannan yamika ma Khadija ledan yace gashi karba tayi tabude soyayyen dankali ne dakuma kosai yasiyo godiya tayi mishi sannan tasa yaran suka dauko gurin zuzzubawa,dubanta Mamman yayi kafin yace"nida Yaya Bintu zaki saka mana".........

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now