page 19

2.7K 316 59
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Page 19*

Seda ya tsallake dayan titin yahau dayan tukunnan yayi realising baya ma duba motocin dake tahowa sakamakon jin karar motar dataho aguje kuma tana dab dashi. duban motan yayi tareda zare idanu in shock sannan yasa hannu yarufe idanunshi cikeda tsoro don yariga ya sadakar motar bugeshi zatayi. dakyar me motan yayi kokarin controlling motar tasa with so much effort dan shikanshi betaba tunanin mutumze shigo tsakiyar titi without looking at his right and left hand side ba......

Mutanen gurin kuwa se hamdala sukeyi don kowa yariga da ya sadakar wani abun zaifaru but thanks to Allah nothing happens se faduwa da Mu'azzam dinyayi ya sume agurin tsabar shock. da gudu Mallam Shu'aibu ya tsallako titin zuciyar shi na mugun bugawa inda yashiga jijjiga Mu'azzam din yana fadin "Yallabai katashi don Allah. Yallabai! Yallabai! Yallabai" haka yadinga kiran Mu'azzam din cikeda tashin hankali. wadanda ke tsaye kansu ne sukayi suggesting yakaishi asibiti aduba shi dukdama bawai ciwo yajiba he was just shocked by the accident shiyasa yayi passing out. haka suka taimaka mai suka saka shi a mota yayi reverse yajuya zuwa general hospital dake bashida nisa da inda abun yafaru. tun yana driving wayar Mu'azzam din keta aikinkara anma tashin hankali bebarshi yadaga ba seda ya tabbatar anshiga da Mu'azzam din accident and emergency sannan yadaga call din Mama dake ta shigowa non stop. daga can bangaren Mama tace "Dan nan inaka shiga haka inata kiranka baka dauka bayan kacemin bayan la'asar zakazo" cikeda damuwa Mallam Shu'aibu yace "Hajiya bashi bane Mallam Shu'aibu ne" azabure Mama tace "kaman yaya? inashi Mu'azzam din? me wayarsa keyi ahannunka Mallam Shu'aibu. inafatan dai lafiya ko?" tayi tambayar sounding so worried don tasan Mu'azzam da waya babu ma yadda za'ayi acemata wayarsa na hannun wani tadauki abun normal issue barema ace driver.

Mallam Shu'aibu jin wadannan uban tambayoyi da Mama tayi masa yasa yace "Hajiya muna asibiti wani dan minor accident ne yafaru anan hanyar mu na zuwa gidanki amma karki damu Yallabai beji ciwo ba" Mama batabari yarufe bakibama tace "tayaya zakacemin baiji ciwoba bayan kuna asibiti? fadamin wani asibiti kuke ganinan zuwa" takarashe maganar yayinda take kokarin tashi daga zaunen datake daman tana sanye da laffaya already shiyasama bata wani tsaya neman hijabi ba tafice agidan bayan tasaka takalminta.

Kwalawa drivern ta kira tashigayi dan already Mallam Shu'aibu yafada mata asibitin dasuke. Cikin mintuna goma suka isa general hospital din Mama nata sharar kwalla. a accident and emergency din suka samo Mallam Shu'aibu tambayarshi tashigayi Ina akayi da Mu'azzam din inda yanuna mata, cikin sauri ta karasa bakin gadon dayake din yana kwance peacefully kaman me bacci. zama tayi gefenshi tareda riko hannunshi still batabar kukan ba tana hidin "Ayya 'Dan nan Allah ubangiji yabaka lafiya" drivernta da Mallam Shu'aibu ne suka amsa da Amin yayinda doctor din dake dubashi yakaraso yana bata hakuri "Hajiya there's nothing to worry about dogon suma yayi sakamakon shock daya samu anma munyi mishi allura insha Allah zuwa anjima zai farfardo" gyadama likitan kai tayi tareda yi masa godiya sannan tashiga shafa lallausar gashin kansa.

Mallam Shu'aibu ne yayi karfin halin kiran su Mami yafada musu halin da ake ciki kankace me segasu ah asibitin suna tambayar yanda abun yafaru nan Mallam Shu'aibu yazayyana musu komai cikeda tashin hankali Mami tace "Naina kuma? are you sure kaji yakira sunan yarinyar nan?" cikeda assurance Mallam Shu'aibu yace "tabbas naji Hajiya dan harya ruga aguje sunanta yake kira kaman wanda yagantane yake kokarin calling attention dinta" Mami batasan sanda tazauna dabas kan kujerar dake gabanta ba sannan tadubi Daddy tace "It means the girl is still alive komi? nibangane inda Mu'azzam yadosa ba Dear"...

Zama Daddy yayi agefenta tareda dafe kafadarta in a comforting manner yace "Anya bawani accident bane yafaru agabansa wanda yasa yayi recalling dinta?" Cikin sauri Mami tadubi Mallam Shu'aibu tace "Yes. It can be" Mallam Shu'aibu anyi accident agurin ne? dasauri Mallam Shu'aibu yace "A'a Madam game mafa yakeyi cikin wayarsa kuma kowa akan titin harkokin gabansa yakeyi nidai banga wani accident daya faru gurin ba"...

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now