Page 22

2.6K 309 108
                                    

🧊 *RAYUWAR BINTU* 🧊

Written by *Zeeneert*💞

*Zeeneert*@wattpad

*Not edited*

*Page 22*

Fuskar tausayi Bintu tayi sannan tace "Yi hakuri Besty kinsandai haka kawai bazanki kiranki ba wallahi ayyukane sukayi min yawa" zama Yusra tayi still tana bata rai "Ayyukanki sunfini kenan komi?" murmushi Bintu tayi sannan tace "Toh kiyi hakuri dan Allah" hararanta Yusra tayi playfully tanacewa "naqi,ramawa nayi ai nima inban kirakiba kita mita wani sa'in shiyasa narama yau" dariya Bintu tayi sosai sannan tace "Munyi one~one kenan?" gyadamatakai Yusra tayi tanakarema Bintun kallo "yanaga kamar kinyi shirin fitane ma?"  Bintu tace "Eyi waifa jiran Khadija nake tadawo daga makaranta muje kasuwa anma tundama kinzo semuje tarekawai" Yusra tace "ai Khadijan nakira inji kobata fita school ba inzo injira ki dan duk atunaninshi kinfita aiki setakecimin kinama gida bakifita ba shine fa na taho kawai Kuma kwana zanyi natambayi Aunty" cikeda excitement Bintu tace  "haba?" Yusra nadariya tace "Allah kuwa" rungumeta Bintu tayi tana "shiyasa nikeson ki wallahi,kice yau akwai kwanan zaune" "aikam dai" cewar Yusran "dan saikin bani labarai kala kala yaudinnan" Bintu nashirin bata ansa wayarta tayi kara Mu'allim ne ke kira. tanason dagawa anma ganin Yusra yasa tayi ignoring call din,harsaida yayi mata missed calls har uku bata daga ba se ana hudun ne Yusra tace "Bazadai kidaga bako? kinanan haryanzu da halinki na koran samari koh? wallahi babu kyau Besty, it's high time kizauna kiyima kanki fada"

Yatsina fuska Bintu tayi "keh ba wani serious call banefa,wata yaken nema baniba kuma nafadamai anma yaki daina Kira" kan Bintu tarufe baki har Yusra tasa hannu kan cinyar Bintu ta dauke wayar dan from yanda Bintu ke maganar nervously tagane cewa she's hiding something. ganin "Yaya Muhammad" rubuce ah screen din wayar yasata tabbatar da zarginta juyamata da wayar tayi tana "wannan ne wrong number Bintu? yaushe kika fara boyemin abubuwa haka?" Yusra takarashe maganar feeling so disappointed....

Jijjiga matakai Bintu tashigayi alamun ba abunda take tunani baneba sede kafinma tayi magana call din Mu'allim yasake shigowa daga call din Yusra tayi ta mika mata sannan tatashi daniyar shigewa daki,cikin sauri  Bintu tariko hannunta tana "Don Allah kitsaya" wabce hannunta Yusra tayi,tayi wucewarta daki bin bayanta Bintu tayi inda tasameta zaune bakin katifa tana danne danne cikin wayarta sa call din a handsfree Bintu tayi sannan suka gaisa da Mu'allim.

Yusra dai mamakin yanda Bintu keta kashe murya tana wani iyayi da kisisina takeyi😂 aranta tace "Ah lallai shiru shirun nan ka kallesu kawai".

Daga bangaren Bintu kuwa Mu'allim tambayarta yayi ina tashiga yanata kiranta bata daga ba cikin sanyayyar muryarta tace "Yaya Muhammad am Besty kefushi dani" yace "munshigesu laifin me mukayi ake fushi damu?" tace "gatanan tana jinka wai ban fada mata kai.. Kai. nake.." sekuma tayi shiru dariya yayi sosai sannan yace "baki fada mata ni kikeso ba?" ashagwabe Bintu tace "Uhmm. gatanan taki kulani se fushi takeyi" yace "hadani da'ita toh" Yusra dake gefe tanata dariya kasa kasa tayi baya dasauri jin ance za ayi magana da'ita tana yiwa Bintu alamar ita bazatayi magana dashiba dariya Bintu tayi sannan tace "gashi zakuyi magana da Yaya Muhammad" babu yanda Yusra ta'iya dole takarba gaisawa sukayi sannan yace "Bestynmu ayi hakuri ayafe mana dan Allah" cikeda Jin kunya Yusra tace "wasafa nakeyi mata" yace "Toh mungode Kuma innadawo har gida zanzo kitayani campaign dakyau wurin kawarki" dariya Yusra tayi sannan tace "Allah yakaimu" Mu'allim yace "Amin" nan tamika ma Bintu wayar, kwanciya Bintu tayi tana "kabata hakuri?" yace "nabata saura ke kibani" dariya tayi sannan tace "danayi laifin me?" Yace "bakibani labarin babbar kawarkiba mana" murmushi tasaki "kayi hakuri zanbaka Insha Allah anma seka isa gida kahuta tukunnan sannan  innafara baka labarinta harsai ka gaji dani" Mu'allim yace "indai kece zakiban labarin bana tunanin zangaji daji" blushing tayi kafin tatambayeshi inda suke yace "munwuce Gombe yanzu" tace "Allah ubangiji yasaukeku lafiya" yace "Amin" kafin sukayi sallama.

RAYUWAR BINTUWhere stories live. Discover now