CHAPTER 4

5.8K 375 39
                                    

ABUN YAZO INJI ME CIKI.

ALIYU'S POV

Wajajen karfe Goma na safe na shirya tare da kama hanyar gidan ya abba. Na ajiye kayana sannan na nufi kasuwa akan farar babur Dina wanda ke kyalli saboda wankin da tasha. Ba yabon kai ba amma Allah yayi ni Dan gayu dukda cewa bamuda kudi na tashin hankali amma gidan yayana bene ne kuma daki hudu da falo daya ne Dan haka yasa yaransa ke da dakin su a sama sai nawa yana kasa sai kuma data babu kowa a ciki.

Aiko yanata harhada kan kudi na sameshi kamin muka fito zuwa wani wajen shan ice cream domin yanada yaran shago Dan haka ya bari a hannunsa tunda ko yananan ma ba wai siyarwa yake ba nashi gadi ne da tabbatarwa ana kula da customers.

Nan mukayi order kamin muka zauna ya fara min bayani Niko ina shanye komai tare da kawo shawarar me zai hana tunda munada har shago uku domin ko gadon mu ne yake juyawa, toh maimakon mu sake wani shago a kasuwa sai mu Gina plaza acikinsa akwai mall, da makeup studio dasu saloon da tailoring shop kamar hakan zai kawo kudi sosai babu musu ya aminta da hakan tare da yarda ni zan kula da wajen tunda ni nayi karatu shidai zai daurani a hanya zaiyi.

Godiya nayi masa bayan mun kammala
Sannan na nufi gidansa domin fara shiye shiryen yadda plaza zai kasance lokacin har la'asar tayi Dan haka ya tsaya yayi a masallati kamin ya shige gidan. Fara aikin nayi naji kai bazan iyaba gara ya bari idan yasha ruwa sai yayi domin ina azumi irin ta alhamis da litinin.

LUBA'S POV

Ana tashi a makaranta jikinta har rawa yake me napep dinta yazo. Malamar Quran dinsu ne ta ganta cikin harshen larabci (bazan rubutashi ta larabci ba duba da korafi da wasu sukayi cewa basaji lokacin da nayi cikin KURUCIYAR MINAL sannan ni kuma in rubuta in fassara ina ganin bata lokaci ne. Thanks) tace Mata lubabah ya naga kinajin dadi haka kamar kiyi tsuntsu ki ganki a gida? Kodai anguwa za'aje cikin washe baki nayi subul da baka nace eh wallahi zanje wajen uncle aliyu. Tace halan shi yake koya miki karatu naga satinnan haddarki ba gyara in ma an mamaki da kyar ne? Shiru nayi Dan banasan nayi karya saboda babu kyau amma tunowa da Wanda na shirga a baya yasa nace eh shine.

Tace aiko ya kamata naga kwana biyunnan kina cikin walwala AI kamar wacce ke jiran lokacin biki sai zumudi kike. Ko aure za'ayi a gidanku ?
Daidai lokacin me napep Dina yazo Dan haka na dale tare da Mata sallama. Riii har gida tun kamin ya tsaya na sauko na shige gida yana fadin yar fillo ba sallama ne toh dai ki gyara gashinki duk ya fito.

Shigewa nayi abina ina dago masa hannu. Hijabi kawai na cire na hada yar jakata domin ummi da Ismail suna bacci sannan na shiga nayi wanka. Sabulun da ummi ke tsarki dashi nayi tsarki dashi nima dukda ko bansan anfaninsa ba.

Zaku tambayeni ya akayi na san na tsarki ne ? Na sani ne lokacin da ummi ke shiga wanka tare da ni domin kuwa koda daddy yayi magana yace ai na fara girma cewa tayi nice yarta daya daya kan ayi min kani ya barni naci lokaci na. Haka zata cika mana bath da ruwa yama sunan abin ? Yauwa magarya acewar ta AI bashida lahani ma yara nide ban sani ba. Toh bayan an haifi Ismail ne muka dena wanka tare. To kullum na shiga nima sai inyi tsarki da sabulun shiyasa ban manta ba. Ko kunga laifi na?

Fitowa nayi na bude dirowar mu ina neman kayan da zanna in kure adaka domin tabbas idan ba a gigin bacci naji ba toh admin kareema tace asa kaya me nuna jiki Wanda zai bayyana Albarkatun jiki.

Hehehe bansa sanda nayi shewa nan tare da buga cinya yadda ummi keyi idan an bazo musu lectures me dadi ba. Sannan nace ana yinta tunowa nayi da inada wasu half vest dina guda 5 nayi aiki da uku saura 2 kwasowa nayi sannan na bude wardrobe din ummi anan take boye sabin abubuwan mu ko a cikin akwati aiko na Samo panties Dina har Goma na saka duka a jakata sannan naga irin gajerun wando wato bumshorts guda biyu pink da royal blue na cotton ne suma na diba. amma Biyu? Kai biyu sunyi kadan nida nake shirin dogon zango? (Untichlobanty:😳😳) Dauko wandunan jeans Dina guda uku nayi da rigunansu na dauko dari biyar a kudin da nake tarawa tun sallar bara dasu kudin tara na Wanda ban kashe ba ko wanda baki keyi min kyauta. Ban tsaya ko ina ba sai gidan asabe me dinki na nuna Mata samfurin bumshort din nace duk ta yanke min wandon jeans su haka riguna biyunnan ma ta yanke ya zama cibiya a bude sai ta kalmashe.

Kasan Jean din da ta yake maimakon a jefar sai ta sake rage masa tsayi ta sama wato wajen guiwa sannan ta Nemo yadi ta mayar min su safa kuma ina bukata ne kamin magariba. Tace wanna dogon jawabi haka... aiko kinci sa'a banida aiki dan haka dubu kawai zaki kawo har kudin yadin. Nikam nace ba, wai yaushe ne bas de (birthday) dinki ? muje muci cake. Tabe baki nayi nace sai nanda wata 3 tukunna saide kuci na Ismail shine saura mai sati biyu ya shekara. Sannan na bata dari biyar din nace in nazo karba zan ciko na fice abina. Ni shiyasa nikejin haushinta ta fiya kwadayi.

Nasan zakuce wai a ina na kiyi duk dabarun nan da sanin Abubuwa tare da iyayi. Na farko dai Dama Allah yayi ni da kaifin basira ga kuma zama da ummi gani da son jin kwakwaf kuma ko me ake to ni sai na shanye tsaf tare da mai dogon nazari iya zurfin tunani na.

Barma wannan zancen yanzu fa in na kuma dauko dari biyar sauramin 1800. Cab gaskiya kudin dayawa amma dai AI uncle aliyu na ya cancanta. Toshe bakina nayi ina dariyar jin kunya Dana kirashi da nawa kamin na shige gida har lokacin ummi na bacci. Wai nikam ince ma baccin bayan la'asar ba kyau? Umm! bata tsoron barawo ya shigo ne? Daukar wayanta nayi da yake na Dan iya karatu da rubutu kadan kadan amma banda kalmomi masu wahala.

Budewa nayi na shiga WhatsApp dinta naga groups dayawa amma ba Wanda yadau hankali na sai wani wai shi KI.. R..RIK..KO KAN..NSA GAMM... aiho na gane wato KI RIKO KANSA GAM aka rubuta. (NOTE: Idan akwai group me wannan sunan to ni ba shi nake nufi ba kawai hada sunan nayi)

Shiga nayi naga voice note turum aiko na fara playing ina saurare, can sai in gyara zama da lamari yayi dadi kawai sai na Nemo earphones Dina da earpiece ba. Domin inada irin tablet haka da aka siyamin don karatu amma ana iya yin hoto acikin sa dasu game hakannan.

Tura wasu nayi zuwa wayana da wani article da naga an rubuta YAD..DA ZAAA KI...SAKA MAIIIII....GID....DA I..HU nasan idan nace zan karanta toh lallai zan bata lokaci gashi shida har ta kusa daddy ya kusa dawowa toh amma me zaisa babba yayi ihu ? Kai da alamu Wanda tayi rubutunnan batada hankali, Ihu ai sai yara.

Komawa nayi na karbo kayana tare da kai Mata Coke daya nace kar ta fadawa ummi na kawo kaya idan ba haka ba zan tona Mata asirin sanda tayi sata kuma akwai videon a wayata. Ahalin fa karya nake 😆 kawai de nasan yadda take da mugun kwadayinnan toh fa lallai tana sata Dan yawanci haka suke.

Komawa nayi na saka atamfofi na guda 3 da lace biyu dama yar karamar akwati ce. Dauko mai na nayi zan saka aciki wani Abu yace bakida wayo zata iya dubawa Dan ta tabbatar kin dau komai kawai kisa a jakar makarantar ki.

Sanda na shirya tsaf na tasheta aiko firgit ta tashi. A ah yan matan ummi har an dawo kenan? kinga ina WhatsApp ne bacci ya kwasheni ko la'asar banyi ba. Bari Inyi in daura abinci nace ummi saura minti 15 daddy ya dawo fa magrib ta kusa saura baifi minti 50 ok 55 da biyar ba. Zaro ido tayi aiko ta fada ban daki da gudu. Nace ummi ni na hada kayana zan wuce amma akwatin yayi mini nauyi bazan iya jansa har gidan ba . tace dau wayata ki rubuta habibi zai bude sai ki Dubo sani me napep dinki, yazo ya kaiki akwai dari biyar a kasan pillow kusai alewa kikai musu. Toh kawai nace naja akwatina bayan na kirasa da yake shima Dan anguwan mu ne.

A tsakar gida na barshi na shiga kitchen Dan shan ruwa saboda nayi aiki AI ko banyi ba? dabino da Zuma na gani me wasu gari aiko shine kullum ummi ke bawa daddy ina lura dasu sarai Dan zuwa yanzu yaci ace kun sanni tsurku da shiga abinda ba'a sani ba. Diban hadin zuman nayi da dabinon sannan na fice sanadiyyar hon din da me napep Dina kemin janyo jakar nayi zuciyata kamar ta fashe Dan jin dadi dukda  sai nayi jiran kwana daya kan na gansa.

Murmushi na saki Wanda ya haska fuskata lokacin da na hau napep din.... A raina nace ya aliyu na... ganinan zuwa gareka, zanbar gida kuma ban San ranan dawowa ba har sai ka zama nawa kuma ka jira in girma ka aureni!

TIRKASHI! AIKI DANYE! KASADA ABOKIN TSAUTSAYI. TOH FA YANZU DAI GA LUBA KAWAR PARIH CEWAR MAI DAMBU TA BARO GIDA KUMA ITA TACE BATA DAWOWA HARSAI UNCLE ALIYU YA ZAMA NATA KUMA YA AURETA.

WANNAN MAGANA ANYA BATAYI GIRMA BA KUWA? WAI MENENE SHAWARKU GA LUBA NE?

KARKU MANTA DA COMMENTS VOTES AND SHARE IT SA ODA WASU MA SU KARANTA ABARSU DA JIMAMI.

Miss untichlobanty 💕

9th  June, 2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now