CHAPTER 21

3.3K 230 96
                                    

Wannan shafin naki ne MaryamyakuraMuhammad,husnalhakeem, aisha_gidalle da Usumaima3315 wannan shafin naku ne Allah yabar kauna.

LUBA'S POV

Har yau ba'a sake yi min zancen uncle aliyu kuma nima ban koma gidan aunty maryam ba Dan nayi zuciya da gaske gashi har mun gama su WAEC da NECO har JAMB mun yi kuma nayi Dan kokari dukda nana ta fini a JAMB tanada 218 ni kuma 210 Dan haka ummi tace zanje gidan aunty maryam celebration.

Nace babu Inda zani ta buga ta raya nace bazan fa je ko ina ba tace toh AI shikenan kinyi wa kanki dama wata gagarumar kyauta za'ayi miki wadda zai MATUKAR baki mamaki amma tunda bakyaso shikenan da sauri nace bari na shirya ina mikewa rikeni tayi tace ai ba yau bane sai ranan asabar yanzu dai gyara zamuyi. Nace gyara kuma sai kace me shirin yin aure ?

Tace banda abinki keda za'ayi taro ayi su hotuna ai kune idon kowa zai zama akai Dan Haka dole ayi gyara. Nace kuma haka ne. Aiko ummi kullum sai tayi min gyara ga bakin shayi da take bani wai na kara kwarjini ne bansan tsimi take tace min ba!

Nide cikin jin dadi da kaguwa nake cewa ummi kidan fada min menene kyautar tace wannan kyautar zai canja rayuwar ki baki daya. Tsalle na soma Dan ni na dauka burina na hada kayan gyaran jiki ne zai cika ashe de akwai lauje cikin nadi.

Ranar juma'a ne aka Nemo mai lalle da kitso suka baza min abina sai walwala nake ina tunanin yadda hankalin kowa zai dawo kaina Dan nasan zanfi nana hadewa. Dukda bawai kyashi make Mata ko wani Abu ba.

Aiko washe gari gidan mu da gidan aunty maryam an cika anata San barka da sa alkhairi gefe naja ummi nace wai ya naji ana Allah yasa alkhairi yasa a dore.

Tace Allah yasa ALKHAIRI wa sakamakonki mana sannan yasa iliminki da kwazo ya dore nace aiho masu cewa Allah yasa gidan ta ne fa? Tace ah ah ke bakyaso alkhairi ya zama gidanki?Nace inaso mana yadda sukeyi ne kamar aure akayi min.

Dariya tayi tace sai kace yar tsana ki shirya maza daddynki zaiyi magana dake. Dakinsa na wuce yayinda ummi ta sake jaddada wa matan kar a kuskura a kirani amarya Dan surprise akeso Amin suka amsa da ba matsala.

Daddy na yamin wa'azi sosai akan rayuwa har na danyi kuka nace daddy wai ya kake magana kamar zamu rabu ne yace ai zaki tafi jami'a ki hadu da mutane iri iri kuma kinga yanzu kin girma kinyi shekaru 16 sure ko wani lokaci Dan haka ki natsu kinji diyar albarka ? Toh nace na rungumeshi daga nan muka wuce gidan aunty maryam.

Hotuna mukasha dukda matan basuda yawa duka da na gidan mu da gidan aunty maryam basufi su 100 ba ai kuwa ba'a damu da yi. Hoto da nana ba kamar itama ba graduation tayi ba har naji ba dadi.

Har na gaji Dan inata tsimayin sanda za'a bani kyauta ta na aunty maryam da iya hajjo ne kawai suka riko hannuna sukace muje nace ba tare da ummi za'a nuna min kyautar ba? Aunty maryam tace ai ita tana can ta rigamu zuwa ashe duk sani ake a kwano ummi tana gida babu inda taje.

Daure min ido akayi da muka shiga mota sukace so suke ayi min surprise da yake nasan aunty maryam wayaiyace shiyasa ban daura ayan tambaya ba ni duk na kagu naga menene ake ja min rai.

Tsayawa akayi na washe baki Dan nasan an iso kofofi naji ana shiga dani har AC mai dadi ya dakeni. Zaunar dani akayi na bude idon nagan my a wani daki dai dai misali mai mugun kyau komai na dakin blue ne yadda nakeso.

Dukda ban gane ba neme neme na fara da ido ina neman kyautar amma na tsaya sanda naga katan leda a gefena. Budewa nayi naga katan ciye ciye ne. Aunty maryam tace maza kici abinki kinji yanzu zamuje mu dauko kyautar. Ina lashe hannu nace uhm Dan magana bazai samu ba.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now