CHAPTER 29

2.7K 219 93
                                    

Haka aliyu ya dinga zirya zirya yana safa da marwa yama rasa me zaiyi su aunty maryam ne suka shigo asibitin rai a bace yana shirin gaishesu likita ta fito Dan Haka ya juya yace doctor ya jikin nata? Murmushi tayi kamin tayi magana yace wallahi mahaukaciyar kishiyarta ce ta jefi cikin nata.

Itadai dr murmushi take masa ya kasa gane Mata tace malam Ali saide ayi hakuri amma ta rasa abin cikinta sannan munyi Mata daurin mahaifi. Don Allah idan zai yuwu muna bukatar ka kaurace Mata na wata 2 zuwa uku zaro ido yayi jin maganar nata amma kamin yace wani Abu aunty maryam ta juyo dashi ta daukewa da Mari. Ummi be tasa mai ta dayan gefen daddy da uncle ABBA suka kai masa wani zafafan  Mari masu kyau a tare sanda ya fadi kasa.

Ganin idon likita yasa suka ja shi suka fita waje tana mamakin dalilin nasu na yin haka tunda ba shi ya batar da cikin ba. Murmushi kawai tayi ta tabe baki ta shige office dinta.

Su aliyu ko suna fita aunty maryam tace kaide aliyu kayi asara a da can baya kazafi nayi maka amma yanzu fa saboda tsabar kai Dan iska ne daga kai maka yarinya tayi hutu kamin ta Sami admission sai ka tumurmushe ta? Magana zaiyi uncle ABBA ya naushi bakinsa take jini ya balle mai shiko fadi yake da fari na dauka shiririta ce irin ta ladidi amma wallahi ka bani kunya zina? Zina fa? Wallahi ka cuci mahaifin mu domin su ba mazinata bane.

Cikin kuka aliyu yace me kuke magana akai ne? Ku fa kuka aura min ita aunty maryam ke da hajjo kuka kaita har gida na a sirri yanzu kuma kuke wannan zance? Wallahi tunda nake ban taba yin zina ba kuma bazanyi ba.

Daddy ne yace dallah yi mana shiru Dan iska wallahi ka cuceki kaci amana muna ganin ka iya sallah ashe ko alwala babu. Girgiza kai tayi tace wallahi billahil azeem ku kuka aura min luba lokacin akan naira 30k sanda take 10yrs a babban parlour. Wai me kuke nufi ne ? Me take faruwa ne toh? Aunty maryam ne tace shege Dan iska da ni uwarka ce da na daga maka n*n* mara mutunci, ya za'ayi mu aurar da yar mu a sirri? Kuma ma tana shekara 10 kai bakada hankali ko? Toh ina ma shaidar ka? Yace ita fa da kanta ta dage ni zata aura lokacin da tayi shek......

Shakar wuyarsa ummi tayi tana fadin ka cuceni waiyo ni na sake kuskure a karo na biyu Dana yadda dakai duba da baka cutar min da yata a karo na farko ba(a lura fa duk yadda aka gaskata mutum kar a yadda dashi 100% Dan shaidan yana nan)

Dakyar aka kwaro shi daga hannunta shiko ido yayi ja ga rashin da ga tashin hankali da azaba. Wayarsa ya raruma yace kungani gayanan dukda wayar da ce mukayi hotunan nan a ciki wallet dinsa ya zaro ya nuna musu Wanda wanke yar karama kunsan hotan da.

Dariya uncle ABBA yayi yace amma aliyu ka maidamu tatsitsai... idan ba rainin hankali ba ya zaka nuna mana hotan ranan haihuwarta kace mana hotan aurenku ne ? Yace AI ranan aka daura toh ga na ranan da aka kawo kin ita. Kwalla masa Mari ummi tayi tace Dan...... ka,wannan ranan da ta gama makaranta ne da hanuna na shiryata. Wallahi saina dauki yata kuma hikima ce zata rabamu Allah ya kaimu ta warke jikinta ya warware yadda zata iya jigilan kotu zaka gani.

Kuka take kamar mace me yasa kaddara take masa haka ne me yasa za'a rabashi da matar shi? Rabin ransa?

Zaman dabas aliyu yayi Dan dabara ta kare masa ya fara salati yana goge kwalla dungure masa kai aunty maryam sukayi tace ko da wasa kada ka kara zuwa inda yarinyar nan take sannan mu hadu a kotu .... ummi ce ta supale Zara fadi daddy ya rikota da sauri ciki akayi da ita wai ashe hawan junta ne ya tashi aliyu ko fadi yake ya Allah idan dai bazamu rayu tare ba toh kasa na mutum itama ta mutu.

Duk wannan tirka tirka da hauma hauma da tashin hankali da aka shiga da kuma sabani da aka samu ya samo asali ne daga sanda ladidi taje wajen bokanta ga yadda lamarin ya kasance:

   Suna isa zama sukayi sukace boka munzo ne domin ka duba.... yace ke dakata tun kamin kizo na duba... babu wata karayar arziki da zai samu saima ALKHAIRI.... washe baki tayi tace a toh zama daram kenan. Yace ke yar bil Adam ban gama ba... koda nace miki zaiyi tafiya karya yake yana tare da yarinyar nan ne.

Dafe kirji tayi tace ban gane ba! Yace tabbas yarinyar nan dake gidanku matarsa ce ! tace k*tma! Matarsa?! Eh lalle za'ayi ta saina masa hauka na shuka ma aliyu rashin mutunci  har mace irina zai ci amana da wannan abar? Yarinya siririya kamar mayu sun kamata?

Innayo ne tace ke zauna musan me za'ayi. Boka nikam ka kara mana bayani ya akayi hakan ta faru? sanar dasu yayi cewa auren sirri akayi. Shiru innayo tayi, ladidi ko fadi take a kasheta kawai boka a kashe min ita. Innayo tace baza'a kasheta ba AI in kika kasheta baki Mora ba kin mata me sauki...

Ke ya dace ki kasheta da hannunki amma ba yanzu ba sai mun fara koyawa Dan renin hankalin mijinki hankali tukunna. Boka so nake a shafe auren nasu baki daya kowa da suka daura auren a sirri a shafe ta a kwakwalwar su. Har ladidi da kai kanka boka so nake ku manta kai nima na manta.

Boka yace ku dai zaku manta amma ni bazan Mata ba innayo tace hakan ma yayi karatun littafi yamin Rana.

Ladidi tace ke innayo nifa an bani labarin wani littafi KURUCIYAR MINAL  itama haka ayush tasa aka shafe suka manta juna har kusan shekaru nawa amma fa daga karshe sanda suka sake haduwa gara a kasheta kawai kowa ya huta innayo tace wallahi ko kinyi asara.

kinsan dai ayush din karamin kwakwalwa gareta shiyasa ta bari suka kuma haduwa ai su banaso aliyun ya manta auren, lubabatu ko kinji dai an boye Mata kenan dama can bata sani ba.

Toh in yan uwan nasa sun mance kinga zina kawai yake yi da ita. Kinga zasu ci mana....... sa sannan sai mu kashe yar iskan yarinyar amma idan shima ya mance toh AI an gama case kawai wani aure za'a Mata babu wata matsala kinga bamu basu kwakwa ba kenan. Ladidi tace toh abin yayi amma boka kamin wannan. Ya batun kara jarumtar nan nifa banji wani sauyi ajikinta ba kuma dai nasan aikinka ba karya.

Kaga inada jarabebben miji kuma alhazawa na har 3 biyu suma ba wasa ga mijin nawa ma kara himma yake kullum. Wani suki burutsu yayi kamin ya kalleta yace wani tangarda aka samu lokacin da na aiki aljanin ya sauya halittar sha'awanki toh na mijinki ya sauya kuma a halin yanzu ni nayi fada dashi sannan irin wannan aiki Wanda yayi ta shi ke gyarawa.

Dan haka zanyi kokari mu shirya dashi ya gyara aikin kamin wannan lokacin saide kisha maganin yahudawa. Tsaki taja tace ni babban aiki ma yanzu a gaba na wa yake ta wani Alhaji. Ajiye mai damin Kudi tayi tace toh muna jira boka mantar damu. Yace tabbas zan mantar damu amma in kuka manta kuka ganku anan zaku rufeni da tambaya Dan haka zan mayar daku gida kuma kuna bacci kamar yanda aka kwanta daku.

Yakai minti talatin yana wasu abubuwa kamin ya batar dasu ya kaisu dakinsu kuma suna masu bacci kamar ma basuje wajensa ba sannan suna masu manta komai.

Hakan yasa ko da ladidi ta dawo gida batasan suna tare ba abinda yasa har ta zargesu saboda yadda luba ta murmure da kuma shakuwar da suka kara yi har de Allah yasa taji abinda suke fadi ranan na.

🥺🥺AYI COMMENT KO NAYI KUKA, AMMA GASKIYA LADIDI TA GAMA KASHEMU BAKI DAYA. WANNAN WACE IRIN RIKICI NE TA TSINKO MA SU LUBA? KU BIYONI DOMIN JIN YADDA ALIYU ZAI HUKUNTA LADIDI DOMIN NAYI IMANI DA ALLAH SAI YA BATA KASHI.

WAI YA ZA'A KAYA NE KUMA TA YAYA ALIYU DA LUBA ZASU DINGA HADEWA? SHIN LUBA IN TAJI ME SU AUNTY MARYAM ZATA YARDA DASU KO ALIYU ZATA YARDA? KAR KU MANTA TA BADA KAI NE SABODA KWANTAR MATA DA HANKALI DA AUNTY MARYAM TAYI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

6th July,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now