CHAPTER 31

2.6K 219 90
                                    

A sati na biyu ne aliyu ya farka kamar mahaukaci haka ya tashi yana dafe da zuciyarsa. Dr ne ya riko sa yana masa sannu yace dr Dan Allah ina suke ? Yace wa? Sunanta ya fada likitan yace AI an sallamesu tun last week.

Sauka aliyu yayi ya fita ana kiransa amma ina ko ta kansu baibi ba inda ya fincike drip dinsa da wayoyin da aka Jona mai suna fidda jini kadan kadan.
Wayarsa ya karba a reception ya fita a cikin mota yake kiran luba itako lokacin ta bar wayan a daki Dan bataga anfanin sa ba.

Ummi ke suburbudo Mata masifa.. nifa luba na gaji da iskancinnan ace mutum kullum bashida aiki sai kuka wai ko cewa akayi aliyunnan ya mutu AI iyakarta. Ke ana kare miki mutunci kina shiririta? Bakisan namiji ba ko?

Dauke kai tayi tace amma fi sabilillahi ko ba komai yaci ace ku nemi bawan Allah nan ba mu fa San inda yake ba wallahi nide a Nemo min aliyu na muci gaba da rayuwarmu. Wallahi duk zaman da mukayi daku Baku taba bani irin abinda yake bani ba. Tana kaiwa nan ta kara sautin kukan ta. Aunty maryam ne tace Allaaaah? kice abin naki ya girmama kodan banyi mamaki ba tunda har ciki kin dauka... tanzi har fada mana kike ya baki abinda bamu baki ba? Turo baki tayi tace nifa ba haka nake nufi ba. Ummi tace toh me like nufi tace wallahi cikin sati 2 nan ya nuna min soyaiya fiye da..... uncle abba ne ya bige Mata baki shigowarsa kenan kuma yaji duk rashin kunyar da tayi musu da gudu ta Mike ta shige daki tana dafe ciki saboda murdawan da tayi hakan yasa ta tsaya da kukan tana yatsine. Tana nazarin kar ta since daurin da akace an Mata ne saboda gudun da tayi.

Daidai lokacin wani Kira ya sake shigowa wayar ta. Dauka tayi da sauri ganin numbar sa ce yana dagawa ta fashe kuka tana fadin Dan Allah kar ace min aliyos Dina ya mutu yazo yayi min wani cikin kar ya barni.

Dukda halin da aliyu yake sanda yayi dariya jin surutun da luba take. Shifa Dan koyi bai iya samun Abu ba ko? Murmushi me sauti yayi yace yan Mata na... haka kikayi missing Dina harda kuka ? Toh karki damu ganinan a bakin gate ki Sansa ki fito inanan nayi parking kizo.

Tace la uncle da gaske Kaine? Amma guduwa zamuyi ko? Yace ah ah ba guduwa zamuyi ba mu da muke da gaskiya menene na buya ? Kawai kibi back door ki fito. Baisan har ta sambado hijab fice ba sunata waya har ta fito.

Shiga Moran tayi tana murmushi kawai ya tsaya kallonta. Yar lukuta take zama ya tabe baki yace luba Anya kin samu dani ma kuwa? Akacemin kusan sati na 2 a hospital amma babu Wanda ya kawo min ziyara kuma ki duba irin kibar da kike yi. Kuka ta fara mai tace uncle dama bakada Lafiya ne ? Wallahi kullum sai nayiwa su aunty maryam kuka cewa basu Nemo min kai ba kalli ido na.

Ta fada tana zare masa idanu dariya yayi yace wasa nake miki baby na AI nasan kin damu dani. Kamin kace me mutanenka sula hau yamutse juna. Hijabi kam an Dade  da bata takardan sallama.

Knocking din window din aka soma Allah ya taimaka tinted ne da sauri ya zura Mata hijab dinta tana gyara Riga kamin su gama kintaba me knocking din ya kasa yin hakuri ya budesu. Aiko ya ABBA ne bayansa kuwa daddy ne sunyi cirko cirko wani wasan Mari daddy ya fallawa aliyu tare da finciko sa.

Uncle abba ne ya finciko luba.... janta ya fara yi tana kafewa tayi shabe shabe da hawaye Dan Allah uncle ABBA karka rabamu waiyo jama'a ku taimaka aliyu na. Babban baby, babyn baby karka barni. Farin ciki da bakin ciki ne ya rufe sunan da luba ke kiransa dashi har spark yake sa Masa amma kuma yadda take kuka ke karya masa zuciya dafe kirji yayi yana jin zafi a ransa.

Ciccibarta uncle abba zaiyi aliyu yayi saurin dauketa yace ya ABBA zan iya jure komai anma banda shiga gonata. Ba haramta maka taba matata yana fadin haka ya shige cikin gida dauke da ita a hannunsa. Shi daddy yama rasa abin cewa uncle ABBA ko ya saki baki sai zaiyi magana sai ya rufe ya rasa zagi zaiyi ne ko me?

Bai tsaya ko ina ba sai parlour ya ajiye ta a hankali duka aunty maryam zata lafta Mata ya riko hannunta. Aunty maryam na sadaki da Allah kada ki yabamin uwar yayana. Luba kam makale uncle aliyu tayi tana fadin kar ka barni Dan Allah.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now