CHAPTER 20

3.4K 226 60
                                    

AishaIsmail625 , aysherahmaddanlami,  wannan shafin naku ne Allah yabar kauna

ALIYU'S POV

Bayan na fito masallati ne nayi ma luba message saboda dazu naga kiranta ina tare da ladidi kamin na shige masallati ina fitowa kiranta ya shigo ina dagawa cikin murmushi zan tsokaneta Dan na dauka ma hakuri zata bani na kuskuren sa tayi sannan tamin godiya na gyaran da nasa akayi Mata banci mutunci ta gaban ladidi ba kawai sai naji sabanin haka.

Ta inda take shiga ba tanan take fita ba Abu kamar wasa sai na bude baki zanyi magana sai naji ta daura magana. Jikina ne yayi sanyi Dan ban kyauta Mata ba amma ni ba da wata niya nayi ba banaso naci mutuncinta gaban ladidi yasa na gasata da aunty maryam tayi Mata magana ta Mata toh menene kuma na duka.

Tunani na ya datse sanda tace ta fasa auren kuma zata bawa me gadi dama a raina nace masha Allah dama nasan yarinta ke damunta.... amma dakata! Ta fasa aure na saboda me gadi? Me take nufi wato ya fini ko me ? Toh dukda banason ta saina AURETA ba ita uwar taurin kai ba? Ko me akayi in bataso ta tada bori? Toh AI in tasan wata batasan wata ba zan AURETA dan in kure taurin kan muga abinda zatayi.

Kiran wayar nayi taki ta daga daga baya ma naji switched off. Gida na shiga abina ina shirya bomb din da zan Mata Dan jira zanyi ladidi ta Dan shekara sai nasa luba ma daga ciki.

Ya Allah ka jarabce ni da rasa Mata na nayi kuma karbi kaddarata ya Allah na rokeka saboda tawakkalin da nayi kar ka kashemin wadannan kar ka rabani dasu. Shafawa nayi kamin nabar kofan masallatin.

LUBA'S POV

Ummi na samu nace Mata ummi nifa wallahi azo a sake zama na fasa auren uncle aliyu bige min baki tayi tace sannu shashasha kawai Dan yabaki haushi sai akace ki fasa aure? Haka zakiyi bayan auren da an bata miki rai kice sake ki? Zama nayi a kasa Wanda ummi tasan abinda zai biyo shine bori tace toh karma ki fara kinga yanzu SS3 kike ki rufe ido kiyi karatu kina gamawa lokacin kin kusa shekaru 17 ayi miki aurenki.

Bori na fara nifa Allah in aliyu za a aurenin yasin ko karatun bazaiyi ba. Ummi tace subhanallah yau ko uncle din babu ? Kuma da kike batun bazakiyi karatu ba wa jahilci zai kashe ? Ki auri aliyun ki a gidansa sai kiyi university ko ya kikace. Mikewa nayi nace toh ai sai muga yadda zan aureshi ni dama can nasan ba sona ake a gidannan ba. A fito a fadamin ko tsintata akayi yasa za'amin auren dole.

Bulala ummi ta dauko ta biyoni zonan yar banza in dauki cikinki wata 9 harda sati 2 awanni 13 nayi ina nakudar ki shine zakice tsintar ki akayi toh sai kin auri aliyun tukunna ma in baki aureshi ba wa zaki aura? Manna Mata nayi ta bankado labulen dakina ta shigo.... Luna wai meke damunki ne? meyasa kikeson bamu ciwon kai? Me yasa kikeson maida daddynki karamin mutum?

Maganarnan an gamata ke da kanki kikace a aura miki aliyu yanzu kice kin fasa? Ki bari idan kin huce ki sake tunani... turo baki nayi nace nide acewa abba na na fasa. Toh ai shikenan. Abinda ta fada kenan kamin ta sauke ajiyar zuciya ta fice.
Da daddare ummi ta samu daddy ta fada masa kamin ta karashe ya daga Mata hannu yace kiramin yarinyar. Kwala min Kira tayi na shigo parlourn ina wani mika da hamma daddy yace in baki warware ba zan ware ki da Mari tsam na mutsu na zauna yace wani shiririta nakeji wai kin fasa aure?

Nace nifa daddy ba aure na fasa ba uncle aliyun ne banaso! Ke dalla rufemin baki lokacin da mukayi justin duniya ki hakura burus kikayi mana kikace sai shi yanzu kuma kina wani magana da batada kan gado? Toh bari kiji gara ki sani aure ba fashi. Kuma in bakida hankali ki kawomin kasa da credit shida gidannan saina ballaki.

Mikewa nayi na koma daki ina fadin zakusha mamaki, sannan na fada kan gado na sai bacci.

Washe gari da asuba ummi ta tashi zata tasheni sallar asuba taga empty! Ban daki ko ina ta duba babu ni babu alamata sai ta dauka ko zuciya nayi na tafi gidan aunty maryam toh amma da asuba kuma? Daddy na ta fadawa aka Kira su aunty maryam sukace banzo ba.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now