CHAPTER 14

3.8K 222 56
                                    

LUBA'S POV

Ana gobe zan koma gida nana tace mu cika bahon wanka da ruwa muyi wanka dukda ko munsan cewa aunty maryam bazata barmu ba shiga mukayi   muka fara kokarin kunna kawai gaba daya fanfon kasan Dana shower tunda a hade suke suka banbaro.

Hakan ko ya faru ne sanadiyyar fada da mukayi akan wa zai kunna ganin ya karye yasa muka Jogana muka fito. Nana tace mummy zata dake mu. Nace kawai ce Mata zamuyi zamu kunna ne sai sulbi ya kwasheni saboda kar na fadi sai na rike shi kuma ya balle. Nana tace zaki dau Levin nace a ah saide ke. Small tace haba yaya lubaaaa! AI kece babba ki dauka please! Kuma kinga ke bakuwa ce mummy bazata dake ki ba.

Nace toh na yarda zan dauka amma ya zamuyi muyi wankan? Small tace muje dakin mummy, nace lallai kuwa AI bazata barmu ba zatace zamu karar da ruwa saide muje dakin baki.
Haka muka fito tsogai tsogai daga mu sai pant  muka sauko har kasa muka murda dakin bakin amma a kulle nace kawai mu hakura.

Har mun fara haurawa sama small tace muje dakin uncle.... nace a ah babu ruwa na. Nana tace kai sister bayanan fa kin manta yana fita zuwa wajen gininshi?  Small tace yanzu zamuyi mu fito.... nana tace zo muje kawai tana ja na nace toh amma ke zaki kunna, small ta kunna na zafi ni kuma in kashe duka biyu saboda ni zan dau lefin bella famfo. Sukace sun yarda.

Ahankali muka bude muka Ganshi yana bacci ya rufu da bargo har kai Dan haka sadaf sadaf muka shige cikin bayin wanka mukasha munkai 30 min muna wasan ruwa har mun manta da akwai wani uncle a daki muna ta kara abinmu.

Koda muka gama fita sukayi akan ni zan bude hanyar ruwa ya wuce sannan na kashe famfo na biyo bayansu.

Ina kashewa na fito naji kamar uncle na magana shi daya bude bargon nayi ina bubbuga shi domin ya tashi Dan ummi tace in mutum yana bacci yana magana a tasheshi.

Zafi naji jikinsa nace la uncle bakada lafiya bari in Kira..... ban karashe ba sanadiyyar matse hannuna da yayi irin mutum najin Radadi. Zafi hannuna ya soma na fara kokarin warta ina uncle banaso ka barni, zafi banaso Dan Allah ka tashi banaso.

A zabure ya tashi ya saki hannuna ya sauko daidai lokacin aka banko kofar dakin......

AUNTY MARYAM'S POV

Tunda na tashi daga bacci naji gidan shiru babu hayaniyar yaran. Dakinsu na nufa na samu nana zaune a bakin gado yayinda mama ke ban daki amma bansan kaya take sawa ba. Nace ina luba? Tsilli tsilli da ido tayi tun daga nan nasan akwai matsala Dan haka na fice da wuri na nufi dakin aliyu zuciya ta na wani irin bugu Allah dai yasa ba abinda nake gudu bane.

Abinda na jiyo shiyasa na fara kuka tun kamin na iso luba ke kuka tana fadin bataso ! A saketa, zafi! Hankada kovar dakin nayi na gansu tsamo tsamo shi yana tsaye daga shi sai gajeran wando yayinda take dauke da Dan kanfai kawai.

Mari uku zafafe na sake masa nace aliyu ka bani kunya! na kara masa wani. Ba dauka kai mutum ne me tsoran Allah ashe ba haka bane! Ba kuma wanka masa wani. Girgiza kai take amma ko in kula..

ALIYU'S POV

Zazzabi yasa na kwanta bacci daga nan bansan me ya faruwa ba sai ji nayi ana tashi na daga mummunar mafarkin da nakeyi. Dakyar na dawo hayyaci na saboda zafin ciwo ga tsorata naga luba najan hannunta tana kuka da sauri na sauko Dan jin menene matsalar dukda jirin da nakeji amma kan nakai hannuna kanta aka banko kofar aunty maryam ce. Daukan ruwan Mari kawai naji kamin tahau wasu maganganu da bansan inda suka dosa ba kuma bayan ko wani jimlar sai ta wanka mini Mari zuwa yanzu na soma jin jiri..... fadi take kaide anyi asaran d'a asaran kani. Da haihuwar irinku gara bari wato shiyasa aka ki ayi aure saboda ansan cewa ana murkushe yaran mutane.

Me gadi ne ya shigo sanadiyyar yadda take daga murya amma bashi daya ya shigo ba da jama'a ya shigo dan ya gane meke faruwa cikin suna fadin ina kwarton? Aciroshi muci ......
Me gadi ne yace laha'ila ha illallahu Alhaji karami meke faruwa? ban gane ba.

Aunty maryam fashewa tayi da kuka tana nuna ni da luba dake kuka a lungu dan bata taba ganin ran aunty maryam ya baci ba. Ita abinda yafi bata tsoro kar a wauwaska Mata Mari irin na aliyu saboda ta balla famfo.

Nace Allah bansan meke faruwa ba kawai gani nayi tana kuka ni bacci ma nake zazzabi gareni taba....! jifana aunty maryam tayi da wani kwalba hakan ya datse min magana ta yayinda take fadin ba dole kayi zazzabi ba? Aliyu na daukeka Lamar kani ashe kai kura ne cikin farar ajiya? shege tsinnenne saina fadawa baban nana. Waya tahau dannawa yayinda na fara salati ina fadin wai karde har yanzu mafarkin nake kode mafarki nane ya zama gaskiya na shiga uku ni aliyu.

Sassabata akayi sama dani wani yana fadin baka shiga uku ba sai an gicce maka....... dan kaza Kazan ka yar kanwar matan wanka zaka lalata?fyade aliyu? Jibgata aka farayi yayinda mafarki na ke zuwa mini tar kamar a gaske domin ko gani nake ilhama akamin. Fadi nake wallahi ni ban Mata FYADE ba suna karya kake.

Ga dai abinda na gani a mafarki

*Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku Aliyu FYADE kake Mata? Abban nana kawo agaji. Ihu akayi masa makwabta suka shigo nan aka rufesa da duka kamin aka sassabesa akayi waje dashi domin a gicce masa girman sa yayinda yake salati yana fadin wallahi ba laifi na bane yarinyar ce tayi min FYADE bani na Mata ba.*
*Wani ne yace zama ka tsara ne idan kaka babu gaban ka.... (CHAPTER 1)*

Salati kawai nake Dan babu sarki sai Allah kuma shi zai iya mini. Waje baki daya suka fitar dani anata duka na gabaki daya jini yamin kaca kaca tun ina ihu da salati har na koma fadin WALLAHI YARINYAR CE TAMIN FYADE bani na Mata ba! Danko zuwa yanzu naga mutuwa kawai neman tsira nake.

Fadi suke yi mana shiru Dan munafuka. Tsabar na daku kasa magana nayi dagabaya. Tayar mota aka dauko ana kokarin a konani yayinda nake fadin kar kuyi gaggawan hukunci ku tambayi luba kamin a kashe ni daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba.

LUBA'S POV

Ni duk gaba daya tsoran kar a daukeni nake Dan tunda uncle aliyu ya karba toh nima bazan tsira ba abinda wani mutumi ya fada ne yasa naso na gane meke faruwa dukda ban tabbatar ba saboda wasu kalmomin ban taba jinsu ba. Kodai wani ya fadi abinda nayi ma ya aliyu ne ? Dama yace idan aunty maryam zata mishi duka idan taji toh amma menene abinda za'a yanke. Tunowa nayi da wani film da aka yanke kan wani da sauri na Mike ina fadin ku barshi karku yanke shi zanbi bayansu da gudu Dan sun Riga sun fice nikam banason na rasa abokina. Ihu nakeyi wasu Mata na rikeni ko yaushe sukazo oho. Nide fadi nake kar a yanke shi har na suma.

AUNTY MARYAM'S POV

Lullubi na nema Mata domin jikinta ya soma nuna alamun girma dukda ko YARINYACE. Hankali ne ta shigo min ganin yadda bataso aji masa ciwo na fara nazari. Amma AI irin wannan lamari yaran tsoron mutumin dake musu sukeji amma ita hana dukanta take. Wannan lamarin harda kisa fa, balle ansan halin aliyu na kirki karfa muje kuskure ne! Toh amma ai na KAMASU babu suturar arziki.

Amma kuma AI bawai na KAMASU suna tsaka sa aikatawa bane. Ko zina dole a kamaka dumu dumu sheda hudu kowa ya gani. Anya banyi kuskure ba? Da sauri na fice........

🥺🥺😢😭 YAU ALIYU NA YAGA TA KANSHI ALLAH SARKI BSBU ABINDA YAKAI KAZAFI CIWO😭😭

KU BIYONI DAN JIN YA ZATA KAYA, WAI SHIN AUNTY MARYAM ZATA ISA KAMIN A KONASHI KO KUWA LOKACI ZAI KURE MATA?

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU DAN ALLAH ACIGABA DA COMMENTS HAR SAI KUN KARAR MIN DA DATA 😉

INA JIRAN COMMENTS FA!

miss untichlobanty 💕

15th June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now