CHAPTER 9

4.7K 259 46
                                    

ALIYU'S POV

Bansan sanda na zame zan gudu ba Dan na dauka aljanune suka soma bi na kuma. Wayata ta fadi zuciyata ma kamar ta fasa kirjina ta fice ga wani gumi dake tsattsafo min Dan wallahi nayi mugun tsorata. Kunsan irin yadda zakanajin karar bugun zuciyar ka a kunnan ka? To haka nake jiyo nawa. Kiu tayi da ido a cikin bargon tana kallona da sauri na dauko bakar jallabiya ta na zura.
Narantse da Allah yarinyar nan zan mugun yi Mata wulakanci.

Nufota nayi kaman wani zaki zan Daukota naga ta kame jikinta.... Allah sarki ta dauka dukanta zanyi AI ko hauka nake bazan taba dukan yarinya ko mace ba sai in babu yadda na iya. ( wasu mazan ma su yanzu in basu taba dukan mace ba toh basu burge ba. Wani fa sai yaja balance, ya antayo bismillah kamin ya kwalla miki Mari. Allah dai yayi mana gyara baki daya.)

Daukota nayi na ajiye a gabana na daure rai dukda ko zuciya ta na fadamin na rungumeta kar na saketa ganin yadda take bari gaba daya sai zuciya ta ta dagwale min. Kawai nace saki jikinki ba dukanki zanyi ba. Da alamu hakan da na fadi yayi tasiri Dan ta saki jikin nata ammade ba sosai ba.

Cigaba nayi da cewa "amma me kikeyi a dakina? Uban wa yace ki shigo ban sani ba? Wai meye matsalarki danine? Wa ya aiko ki kitakura min? Bakisan kina takura min ba kullum?" Idonta ne ya soma cikowa sa kwalla, ji nayi zuciya ta ta raunana amma dole nayi mana iyaka idan ba haka ba zan iya lalata Mata rayuwa Dan zuwa yanzu hakuri na ya soma karewa. Tsoran Allah kawai ke rikeni , to amma idan ni na jure wani zai iya jurewa?

Muryanta na rawa tace ya akayi na ta kura ma ka? Cikin tsawa nace nan!.... ina nuna Mata kasa na kamin naci gaba da cewa kin hanashi zama sakat tun ranan da kika taba min kin..... caraf ya fadomin na tuna da wacce nake magana gashi na hau sakin layi kila ma bata gane inda na dosa ba. Rage murya nayi nace tashi ki fita Dan Allah banason ganinki....

Take hawayen da take rikewa suka soma zuba kallon idanuna take taga dai da gaske nake kawai ta sauka tana dingisawa ta fita kuma wallahi abinda na gani a idonta bansan yanda zan kwatanta ba disappointment, tsanan kanta , da bakin ciki na gani da ma wasu da ban gane ba.

Tana rufe kofar na tura kaina cikin pillow kamin na tashi na wargaza gashin kaina. Kara na kwalla ahhhhhh! Kamin na naushi katifa na nayi cillo da pillow dasu bargon. Ban daki na shiga da kaya a jikina na sake ma kaina ruwa. Wallahi yarinyar nan ta kasheni ta bunne. Na dauka na gama ganin komai a duniya ashe banga komai ba emotion disorder tayi causing mini tun ranan da na soma ganinta.

Kwanciya kawai nayi nahau rafka bacci abincin daren da banci ba kenan Isha'I ma biyoni akayi sai tsakar dare na tashi nayi ga kaina na min mugun ciwo.

LUBA'S POV

Sanda nasha kuka na tun da na fito daga kasan benin a hanya mukayi karo da aunty maryam da sauri ta riko tana fadin luba ya akayi kike kuka? Me ya sameki? Kodai su nana ne suka ki yin wasa dake Dan kinji ciwo? Girgiza kai nayi ina shessheka nace kawai hannuna ke min ciwo tace Ayya zo muje ki kwanta sai in baki kaza da magani ko? Gyada kai nayi sannan ta daukeni ta kaini daki anan ta bani abincin da magani sannan nayi bacci.

Washe gari ko daki ban bari ba saboda karma ba hadu dashi kuma nasha alwashi bazan kara shiga harkanshi ba har sai yazo yamin magana tunda shi bad uncle ne. Haka dai na dinga jin haushi har na huce amma fa inanan akan baka na bani zuwa inda yake.

ALIYU'S POV

Haka mukayi kwana biyu bamu hadu ba kuma Alhamdulillah na daina tunaninta saide kawai inajin wani iri a zuciyata  na maganar Dana fada Mata. Yaci ace na duba cewa ita yarinya ce amma kuma ko ba komai Dan ita nayi. A rana na uku ne na tafi garinsu binta wai zatayi birthday party... ni ban wani zuwa party amma wannan opportunity ne da zan gudu daga matsalata kawai sai na yarda. Tunda na shiga hall din ba wani haske.... gashinan dai rana ce amma kamar dare. Toh hankali na bai kwanta ba amma sai dai na shiga aka sako tafi tare da balle ni da haske wai ga saurayin birthday girl.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now