CHAPTER 30

2.7K 192 50
                                    

Luba batasan wa ke kanta ba yayinda aliyu yaki komawa gida kuma yaki ci banda ruwa ba abinda yake sha har ya rame.

Har dare bai koma ba yana tsaye a waje harsu ummi suka tafi gida aka barta da aunty maryam lokacin ne ya shiga Dan ganin matarsa domin hakurinsa ya kare. Da sallama ya shiga kamin ya karasa aunty maryam tace rike abinka ka koma. Na rantse da Allah aliyu kada ka bata min rai ka fice daga dakinnan kaji na fada ma.

Kuka ya fara Mata aunty maryam kada kuyi min haka koda kowa zai juya min baya ke bazaki juyamin ba. Tace dalla can rufe min baki wallahi ni ba baya ba har keya na juya maka ka fita domin ganin ka koma min rai yake. Bai kulata ba ya karaso da sauri ya kama hannun luba ganin ta fara kokarin bude ido.

Sannu! Sannu lubabatu na ina ke miki ciwo ? Me zakici? Kinajin yunwa? In kawo miki ice cream? Dafe kanta tayi tana kara kankame hannunsa da nata ke ciki murmushi tayi tace uncle aliyos da gaske babyn mu ya mutu.

Aunty maryam ne tayi musu shiga sauri tace iye ? A lalle yar banza ashe da yaddarki.. no wonder har murmure wa kikayi daga zuwa gidansa. Yar iska wato kema kinsan dadi ko ? Shine zaki baje min taburmar rashin kunya ko?

Kama hannun sun tayi ta raba tace toh AI sai ka fice ko Dan uban yarinya yace ko kusa da ita kazo sai ya kasheka. Luba ne ta zauna da sauri tana yatsine fuska saboda zafin da taji amma de wannan ba shi yafi muhimmanci ba. Tace kisa kuma ? Me aliyu na ya muku zaku kashe min shi? Aliyos ka basu hakuri ta fadi haka tana shigewa jikin shi fuskarta ko tuni ya jike da kwalla.

Aunty maryam ne ta banbarota da sauri tana fadin ji jaka ballagaza tanzi na gane me ya faru wato da kika bishi da farko baki samun abinda kike nema ba shine da kika girma kika sake komawa ko? Toh AI burinki ya cika kinji me muke ji harma da kyautan ciki aka biki. Allah na gode ma da ka barar da shegen nan ba tare da ya shaki iskar duniya ba.

Aliyu me yace kul aunty maryam ina miki ganin uwa saboda ya ABBA shi ya reneni yamin gata amma idan kika kara sheganta min da to.... mari ta tsinka masa tace sannu fitsararre dande nasan iyayenka suna da kima ne kuma ba yan iska bane da kaima na kiraka da shegen.

Ficewa yayi hannunsa akan kumatunsa yama rasa me zaiyi tunani akai gida ya nufa ya samu ladidi ta daura kafa daya akan daya... dadinshi daya da ita batada kazanta toh amma ina anfanin tsaftar? Wuce ta yayi Dan bakin cikin yau ya wadatarshi gobe a daura daga inda aka tsaya.

Gabanshi tasha tana wani jijjiga tace sannu ubale ai babu inda zaka.. bayan ka gama lalata da shegiyar nan kaci amana ta yanzu kuma kace zaka wani shige daki. Kautar da ita yayi yana huci Dan yasan yadda yakeji yanzu in ya riketa bazai Mata da dadi ba.

Kwalarsa taci tace billahillazi sai ka fada min uban wa yace ka ci amanata? Wato shine harda wani babynka ko? Kai bakaji kunya ba cikin shegen?
Kwalla Mata wani Mari yayi sanda ta zube a kasa ya rikota ta riga ya dagata. Kirjinta ya kama kam yana janta tanan har kitchen suna shiga ya hankadeta ta bige abin plates suka fado kwalba biyu suka shige Mata hannu.

Cup ya dauko yace rike maza rike karba tayi da sauri har bari jikinta yake yace yauwa. Toh dama ina zargin ke kika hado min munafurci za'a rabani da matata, kika kashe min jini kuma yanzu kike kiransa da shege ko? Toh zaki biyani shege na Dan ni dama yan biyu nake sa rai.

Wani cup ya dauko ya dauko hannunta daya fashe yasa a ciki yace wannan cup din shine ba Hassan ko Hassana kuma wallahi in kika cire hannunki jini bai cika cup din ba wuka ya dauko a drower ya lashe wukar kamar maye. Aiko wani sauyi cikin ladidi ya bayar ajiye wukan yayi ya falla Mata Mari bakin ya fashe yace yauwa toh zanyita falla miki Mari na zagar min yara da kikayi jinin bakin naki kuma shi nakeso ya cika wannan kofin a matsayin usaini ko usaina.

Kinga idan kika biya min toh ba bashi... haka ya dinga falla Mata Mari JININ yana zuba cikin cup din zuciyar sa fa shima ta girgiza saboda karfin kimanins balle yadda yake bin sunna baya dukan mace amma haka kawai yaji ya tsani ladidi fiye da tsanan da yayi ma kafirai baisan cewa shirkan da take bane yasa ya tsaneta.

Bai barta ba  Sanda ta cika cup biyun nan lokacin hakware 5 sun fice. Daurewa yayi a farin leda guda biyu lokacin ta suma ma. Yaiyafa Mata ruwa yayi ta ja numfashi amma ta kasa motsi fuskarta baki daya ta sauya halitta. Ya miko Mata kulli biyu na jini yace yauwa yanzu so nake kiyi musu addu'a ko auntyn su. Shiru tayi yace ko bazaki karba bane. Karba tayi Dan bazata iya magana ba. Yace toh maza yi musu addu'a bakinta ta juna alamun bazata iya magana ba ya dauko wuka da sauri ta bude bakin amma sai jini kawai ke zuba yace Mike muje.

Tashi yayi zatayi bayansa yace no no ai sarautar ki tafi haka queen ladidi Ai ke ta kan carpet din kwalabe zaki bi maza taka da girman ki kinji sarauniya? Kukanta ne ya tsanan ta. Itakam bata taba shiga urin wannan masifa ba tunanin yadda zata gudu kawai takeyi.

Fartanya ya cillo Mata yace maza toh ki haki rami ki bunne min JININ naki da kika biyani 'ya'ya na dasu ni zan tafi hotel wajen yan Mata na ko? Kada ma kiyi tunanin guduwa Dan sojoji da yan banga ke kewaye da gidannan. Mikewa yayi daga tsugunon da yayi yace oya hug me amarsu a rungume ni. Kin motsawa tayi yace bazakiyi ba? Da sauri ta Mike tana dingisawa ta rungumeshi baisan sanda hawaye suka zubo masa ba.

Wallahi yana kaunar matarsa amma da ya ganta yakeyin kamar ya yankata da sauri ya ture ta ya shige mota ya figa a guje. Hotel ya kama daki suit me ciki da parlour yana shigowa kuwa ya fashe da kuka numfashin sa ne ya soma daukewa nan ya tuna yabar maganinsa a gida domin da hawan jini aka haifesa.

Kiran dr zaiyi wayarsa ba kati Allah yaso yana da Mobile banking app sayan kati yayi daga account dinsa ya Kira dr yana dagawa yace masa zuciya ta zata tarwatse.....ahhh ban taba jin irin haka ba ina kaza kaza hotel room number 158 yana kaiwa nan muryarsa ta soma sarkewa yana fadin dr ka hanzarta zan mutu ... daga nan numfashin sa ya dauke.

Luba ko tunda aliyu ya fice ta fara kuka aunty maryam me nayi miki kikeso ko rabani da aliyu na sannan wani zance kike cewa munyi zina bayan ke da kanki kikace na kwantar da hankalina zakiyi min bayani tace ni? Kema ya tsurkuta niki karayar ne zaki lafta min ? Toh bani bace wata ya sadaki da ita kukayi magana.

Murmushi luba tayi tace ko wani abun mukayi muku bai dace kuyi mana  wannan hukuncin ba wallahi muna son  junan mu. Gwabe Mata baki tayi tace ji yar iska mazinaci kikeso? Toh wallahi baki isa ba..sautin kukanta ne ya karu tace aunty maryam kuyi hakuri Dan allah kada ku rabamu na rokeki.

Aunty maryam bata ko kalle ta ba ta kwanta abinta tayi bacci itako haka ta dinga kuka har karfe biyu da rabi kamin bacci ya sace ta. Haka tayi sati a hospital aka sallamo ta amma aliyu ko motsi baiyi ba kuma bai shiga coma ba.

Ladidi ko mamar ta ta Kira ga mamakinta aka bar mahaifiyar ta shigo amma an hanasu fita anan me gadi ke fada Mata AI shi yanzu zaman cin turo kawai yake Dan aliyu yace banda bude ma bakinta gate babu abinda zaiyi amma kuma kada a bari ita ta fita kuma suma in zasu fita sai sojoji sun kalli fuskarsa an tabbata sune ba ita ba.

Haka mamar ta ta zauna da ita kan ta ya sabe kamar ma ya dawo amma de har yanzu bakin bai sabe ba.

MASHA ALLAH ! TOH ANAN ZAN DAN DASA AYA. MENENE RA'AYINKU AKAN HUKUNCIN ALIYU? SHIN YAYI TSAURI KO YAYI DAIDAI ? KARDE KU MANTA BAI GAMA HUKUNCIN BA.

YAYA ZA'A WARWARE WANNAN LAMARIN NE WAI? KUNA GANIN LADIDI ZATA SAMU TA GUDU ?

KU BIYONI A SANNU KUJI YADDA ZA'A KAYA ...

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

6th July,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now