CHAPTER 33

2.7K 217 50
                                    

A bangaren su luba kuwa kwantar da ita yayi a kujeran baya ya fara bata hura Mata iska ganin da karfi ta shaki numfashi ta soma ja da karfi da alamu tana bukata.

Ajiyar zuciya ya sauke yace sannu baby na sannu kinji? Me ta sameki nasan de ba haurowan da mukayi bane ko shine? Girgiza kai tayi tace numfashi nane ya kage. Dama satinnan bana iya zama wajen da babu iska ko an kunna ac sai nabar window a bude.

Yace subhanallah shine baki fada min ba? Toh muje asubiti ko? Kai ta daga Dan ita ma tanaso tasan matsalar ko an taba Mata wani abun ne a ciki. Amma karfa su jiyo wata masifar gara ma su fara yawon in ma mutuwa ce daga baya ta mutu Dan bazata yadda ta mutu bata ci abinci ba.

Dariya aliyu yayi yace hajiya ta ina jinki fa. Ba a tunani kike wannan maganar ba dariya tayi tace kaga kaifi na? Yace karma ki damu babu wani batun mutuwa.

Park suka tafi sukayi ra wasanni da ciye ciye sun mance shaf da sunada wata matsala ganin yamma yayi yasa yace muje asubitin nan sai na mayar dake gida. Turo baki tayi tace amma uncle dole ne sai naje gidan? Nifa Allah bana son komawa ni dakai nakeson zama... saboda kafi min su Kaine ka nuna min gsky tun ina karama kuma ka soni su kuwa banda......

Da sauri ya toshe Mata baki yace kul luba wadannan fa iyayenki ne koda ni bai zama dole na musu biyaiya ba ke wajibi ne kuma kuskure kowa yana yinta nima nayi har sau biyu ban tsawatar miki da wuri ba na barki kina nema ki tsoma kaina a ruwa sannan na kuma yadda aka boye auren mu Wanda na tabbata kaunar da nake miki ne ya janyo min yin wannan sukacin saide har yau abinda na kasa ganewa shine yadda akayi na fara son yarinya...

Ji yayi ta rungumesa tana kuka tace uncle maimata. Yace me? Tace abinda ka fada dazu da gaske kana kaunata? Murmushi yayi yace sosai kuwa luba ban gano hakan ba sai randa baki kwana a kirji na ba kika kwana a wani waje ranan da aka kashe mana jinin mu kuma ake ma soyaiyar mu barazana. Kuskure na na uku shine da ban taba fada miki ina kaunarki ba.

Lubabatu...ni Aliyu bala bakabe ina matukar sonki kuma kaunar ki ya ratsa jinina saide inaso ki sani.... San kara aure.... da sauri ta zabura saboda yadda gabanta ya fadi... shi kuwa ko a jikinshi yace inde har Allah zai halittu min wata Wanda tayi daidai da ke zan aura amma in bani watan ki ke daya ce a duniya toh dake zan zauna.

Ajiya zuciya ta sauke tana duka kirjinsa cikin wasa tace har ka bani tsoro wallahi kamar hanji na zai zazzago. Dariya yayi yace Allah uwar yayana harda hawaye ya fadi haka yana goge Mata hawayen.

Tafiya sukayi suna isa asibitin yakaita wajen likitanta bayan sun gaisa yace likita dama batun matata ne tace tunda wannan abin ya faru bata fane meke Mata dadi ba takanji ciwon mara, sannan bata iya zama a inda babu iska. Luba tace kuma ni daya sai inji inason nayi kuka sannan wani lokacin haka kawai ana cikin zama sai na fara bacci.

Dan murmusawa aliyu yayi saboda ya tuna yadda takeyi ne sanda taje da ciki bai sani ba kawai ita daya sai tahau bacci. Akwai ranan da ta shiga ban daki bayan sun raya sunna tace zatayi fitsari kamin nan shi ya cire bedsheet shiru shiru bata gama ba yace zan shigo ba shiru dama kullum yakan tsokaneta tare zasuyi wankan amma sai ta dage bazai shigo bayin ba.
Yana budewa yaga ta baje akan shadda tana baccinta harda yawun bacci.

Har ya gama tunanin sa luba tanata Jerowa likita abinda takeji ita dai dr murmushi kawai takeyi sanda taga abin ba karau bane tace toh naji daga nan AI ko baki min bayani ba nasan me ke damunki.

Kallon aliyu tayi tace ka tuna lokacin da na sanar dakai matarka ta rasa cikinta? Yace sosai kuwa likita har haushi kika bani saboda yadda kike wannan murmushin taki Dan dariya tayi tace toh fa baro baro haka zaka fada min? Toh shikenan yanzu ko zan birge ka.

Abinda baka sani ba matar ka tana dauke da cikin yan 4 ne.... zaro ido aliyu yayi yace ban gane ba Dana yara 4 na rasa ? wallahi ladidi kin shiga uku. Tace tsaya mana lokacin da kishiyar ta ta jefeta guda daya ne ya fita sauran yaransu uku suna nan kuma yanzu haka watan su uku harda kwanaki idan kunaso zamu iya yi muku ultra sound da pregnancy scan domon kuga hotansu.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now