CHAPTER 36

2.3K 214 54
                                    

Alkali yace ke kuma wacece kuma me hadinki da wannan Shari'an? Shigowa kotun tayi tace nice ladidi matar aliyu wadda ake ikirarin mijina yayi min fyade.

Toh wannan maganar ba haka take ba mijina yayi min abinda yafi FYADE abinda ya ninnika FYADE abinda ba ko wace mace akewa ba.

Miji na bai taba kyautata min ba kyautatawa ba halin mijina bane baya kyautata ma matansa.
In akace shi mutumin kirki ne an cuceshi.

Alkali yace ke mu ba gasar iya magana mukeyi anan ba in kinada abin fada toh in babu kuma kada ki batawa shari'a lokacinta.

Ajiyar zuciya tayi tace kamar yadda na fada baiyi min FYADE ba laifi na ne nice na hada tsimi na ajiye a fridge shi kuma yasha lokacin da ya dawo gida ďan ya dauka juice ne kuma batason ya tasheni a bacci. Kallonta aliyu yayi ya saki baki jin yadda ta feso karya amma de yayi tsit baice kala ba.

Tace kuma kamar yadda nace ba mutumin kirki kadai bane mijina mutumin arziki ne ga dattako da iya nuna so da kauna Dan albarka abin alfahari na... kamar yadda nace bai taba kyautata mana ba bauta mana yakeyi ni da aunty lubabatu.

Aunty maryam haba kawai ta rike luba dake zaune a kasa tana kuka ma kamewa tayi. Toh kode asibitin da taje ya taba Mata kwakwalwa ne.
Lauya hindatu tace look mrs ladidi idan har akwai Wanda yake tursasa ki ki fadi wannan magana ne toh ki fada ma kotu kada kiji tsoro.

Ladidi tace babu me tursasa ni babu abinda mijina yamin rashin fahimta ce kawai ya faru da mahaifiya ta kuma de shekaru bai wani ja ba bare nace tsufa ce.

Alkali yace toh ya batun lubabatu da akace zina suke? Tace haba mai Shari'a? Wace Mata ce zata bari ana zina a gidan ta tayi shiru? Billahil azim ba zina suke ba matarsa ce.

Lauya hindatu tace amma ko kina da bayanin abinda ya samu hakorin ki? Tace AI wai hakwara na ? Ranan da suka kawo mana kyakkyawan news ne tsabar jin dadi aljanu na suka tashi to a garin su rike nine ma na yaushe mana jaririn mu kuma anan ne na dinga gwara baki na.

Tsumu tsumu lauya tayi wato de ta fadi or what? Alkali ne yace ikon Allah... duba da jawabin da  muka saurara daga bakin ladidi kotu tayi wulli da wannan case sannan duk wani laifi da ake tuhumar aliyu da aikatawa ta wanke shi. Malam aliyu Allah ya bada zaman lafiya ya kuma raya yan uku yana kaiwa nan ya buga gudumarsa yace court!

A bakin kotu kowa jiki a sanyaye yayinda aliyu ke nazarin wani munafurci ladidi ta tsiro dashi luba ko ganin zuciya take Mata ladidi ta riko hannun luba tace sister wai da gaske yaran mu basu zube ba? Wani tsalle luba ta daka a tsorace Dan ita ba haushi ladidi ke bata ba ganin ta banziya take Mata.

Makalewa tayi ajikin aliyu ladidi tazo da yar sandan ta tace yaya aliyu ina wuni murya a sanyaye yace lafiya ladidi daga nan baice kala ba ta riko hannunsa suka fara tafiya a hankali su uku kowa da tunaninsa ladidi ba abinda ke Mata yawo a zuciya sai nadamar abinda tayi.

Aliyu ko tausayi ta bashi da tana so da matasa an dauresa a zuwarnan nata amma ta tattare duka laifi ta bashi. Yan jarida da gulma nan sukayi musu ca da tambaya babu Wanda ya kulasu luba ya cicciba yasa a mota ya karbi sandan ladidi ya jingina a gefe itama ya dauketa ya sata a gefen luba kawai sai suka ga ya fara kuka.

Kewayo wa yayi ta bangaren luba yace fito baby a hankali ta fito ya shiga tsakiya ya miko Mata hannu alamun tazo. Shigowa tayi ya kwantar da ita a jikinshi ya kwantar da ladidi ma dukda cewa yana jin haushinta amma yana sonta.

Driver yace ina zamuje Alhaji karami? Yace gidana... suna isa suka shiga parlour sake zama yayi a doguwar kujera suka zauna a gefensa kawai sukaga ya dafe goshi ya fara musu kuka kamar yaro. Babu abinda yake tunawa sai yadda ya dinga dukan ladidi kamr bashida imani da yadda suka sha wahala.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now