CHAPTER 7

5.1K 234 17
                                    

AFWAN FOR THE TYPING ERRORS....

LUBA'S POV

Da sauri uncle Dan gayu ya ciccibeni tare da daurani a kujera yana fadin luba? Luba ina ke miki ciwo? Kafata ya rike yana latsawa na kwalla kara. Kallon aunty maryam yayi yace tayi targade a kafa.

Niko tsabar azaba ma na kasa hawaye fadi nake hannuna , waiyo ummi hannuna uncle ka taimaka min hannuna. Yace daga hannun mu gani. Nace bazan iya ba ji nake kamar baya jikina waiyo Allah na😭😭. Aunty maryam tace akwai me gyaran targade a unguwan nan. Nan nan ne gidansu jummala abban nana kuje.

Hannu yasa zai daukeni sai kuma ya tsaya hakan yasa uncle abba ya daukeni
Muka nufi gidan aiko kakarsun tace hannun dama na karya kafata kuwa gurde wa nayi haka ta sallame mu zamu tafi naga fa mutumi na bazai daukeni ba aiko nace shi zai daukeni. Haka na basu hujjoji na Dan dole ya daukoni muka taho. Kunsan yara idan suka samu wani Abu daya suka kama toh sunyita yi kenan a hanasu ayi duk yadda za'ayi amma suki dannawa sai sunji wuya ko kuma yadda zasu samu wasa daya ayita yi suna jin dadi nifa nawa shine in ganni a jikin uncle aliyu.

Ji nayi ya fara saka na kamar zan fadi da alamu tunani yake ba da biyan komai ba na sakala hannuna a wuyansa jikinsa damshi da alamu gumi yayi hakan yasa na kara lika jikina da nasa naji ya danyi bari kamin yace jar ubannan....

Uncle abba ne yace kai aliyu bansan shirme gaban yarinya kake irin wannan magana? Waima me yasa ka fadi hakan Dan dabur dabur yayi kamin yace nauyinta ne ya bani mamaki yar cikula da ita kamar budurwa...... tsabar nauyi .

Araina nace lallai ma ya maidani jinjira Lamar Ismail ko? a fili ko nace toh me marabata da budurwa? Haka dai muka cigaba har muka isa gida karbana aunty maryam tayi ta ajiyeni a kujera Tana fadin kar a fadawa gidanmu saboda kar su damu abari sai na Dan ware tukunna.

Zama sukayi aka soma zuba abinci, wai kujerun bazai ishesu ba kamar yadda aunty maryam ta fada. Ya ABBA ne yace a Nemo stool. A raina nace wai shagali za'ayi bsbu ni? Yadda Nike hango turo haka Aunty maryam ce ta datse min tunani ta hanyar cewa luba kekam babu hannun daman ma saide a baki a a baki.
Dauka na tayi a ririce Kamar jaririya ina wani narkewa ta daurani a cinya tare da miko min loma har zan karba naga uncle aliyu ya lunkume nashi a raina nace AI baka isa kaci tuwonnan lafiya ba. Nifa bawai ina nufin Dan in daga masa hankali da wani ba kawai de kunsan yara da neman magana

kauda kai nayi tare da fashewa da kukan karya ina shagwabe baki uncle ABBA yace luba drama queen yanzu kuma ya akayi? Nace ni so Nike uncle aliyu ya bani.... ganin kowa ya tsira min ido alamar tambaya yasa nace saboda.....saboda kun zuba yaji a naku. Wuf uncle Ali yace toh AI sai a zuba miki mara yaji ko?

A raina nace can AI duk wayonka uncle sai nahau cinyanka dan naga alamu fushi kake dani sai in baka hakuri dukda bansan laifi na ba. Amma daddy na yana fadin duk sanda kayi ma wani laifi toh kaikayi girman kai wajen bashi hakuri. Da ka cuta gara a cuceka.

Yace sai tabaki da cokali ai ko? Uncle ABBA yace kawai karbeta ka bata mana me kake wani zillewa? Kama ci sa'a tana son kuyi shiri bakasan 'kiuyan luba ba ko? Sanda muka shekara harda rabi kamin muka Saba. Kuma gaskiya ne banida sabo da wuri shiyasa idan naga bakin mutum nake kaffa kaffa sannan inyita kallon bakon ina nazari.

Mikewa yayi tare da kewayo wa ya karbeni kamin ya koma muka zauna shiru akayi anacin abinci in yayi loma daya sai ya bani daya.... ganin yaki magana yasa bance masa komai ba sanda ya bani lomar na dan gatsa masa cizo. Ahhh ! Yace nikam na kyalkyale da dariya su aunty maryam ma dariya sukayi masa ya bata rai yace ga abinda banso AI. An taimaka ana bata abincin ta rasa yadda zatayi godiya sai ta gantsara min cizo. Aunty maryam tace kara'i tajeyi sanda ta fara hakuri babu Wanda baisha cizo ba sai kai... zaro ido yayi yace dama suna zuwa tun tana yar ficiciya ? Uncle ABBA yace kaji min kai da wani zance toh ba yar kanwar matata bane?

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now