CHAPTER 37

2.3K 254 39
                                    

Yace toh ni bari na dauki duk wadda naga dama yana fadin haka ya rufe ido aiko kowa ya Mike mai kai masa damka nati me girgiza kai nayi ladidi tasa hannu zata bude idon nasa kawai sai ga gawain wata Mata da na innayo sun baiyana.

Cikin kaskanci duk diwa da kazanta na fita daga jikinsu. Ya nuna dayar matan yace kunga wannan matar  sunanta jummala itace matar kawuna kuma itace ta bada shawarar a koya min tsafi akayi min karya cewa almajiranta za'a kaini. Bata taba kyautata min ba saide ta kuntata min, ba ta da aiki sai hada guri a unguwa yau tana can gobe tana can. Aikin kenan.

Wannan kuwa ya fada yana nuna ladidi yace inajin ba sai nayi dogon bayani ba itace innayo cousin din ladidi. Wannan da kuke gani shaidaniya ce tazo wajena tace taga mijin ladidi kuma ya Mata amma bataso ta dameshi cikin sauki Dan za'a gane takunta so take a bata ma ladidi suna sai ta rabasu.

Batasan cewa tun lokacin akwai lubabatu ba ni ko na sani amma nayi shiru abina. Anan tace na sa duk abinda ta umarci ladidi tayi kuma hakan akayi ban taba aiki ya subuce ba sai akan ladidi lokacin da tace ta soma zina amma ladidi ta kasa saide bazata ketare maganarta ba Dan haka tayi pretending haka innayo ta kawota wajena da duk wani kullu da ladidi tayi bata cikin haiyacinta.

Malam aliyu saide kayi hakuri dukda nasan maganar da zan fada bata da wani muhimmanci saide hada guri toh amma yadda ladidi ta kasa cin amanar ka yasa...... sai kuma tayi shiru bakin aliyu na rawa ga hawayen nadamar abinda tayi wa ladidi na zuba mai yace in...ina..ji..jinka.

Ajiyar zuciya ya sauke yace wannan dalilin yasa na fara son matarka amma kuma tana da aure ni kuma babu abinda nake darajawa irin aure. Da naso tsafi daya zanyi ladidi ta zama tawa amma bazan iya cin amanar aure ba.

Faduwa aliyu yayi gaban ladidi ya kwanta a cinyarta kamar yaro yana gunjin kuka yana fadin ladidi na ki yafe min kinji.😭😭
Babu Wanda bai share kwalla a wajen ba yace tabbas ke din nagar tacciyar Mata ce Wanda samun irinki sai an tona.

Bayan wani lokaci boka har yayi tsafi ya watsar da gawan a jeji bayan aljanu sun zukesu sun busar dasu. Tashi yayi jiki a sanyaye yace yan uwana ni zan tafi zanje na kwana ido biyu na warware duk wani aiki da nayi cikin jahilci sannan kuma na nemi tuba kuma na roki Allah ya yaye min son ladidi kar na cutar daku a kanta.

Ya bude kofa kenan aliyu yace malam boka... kowa sanda ya murmusa saboda sunan bai zauna ba da gyara murmushi bokan yayi yace musa ne sunan aliyu yace Ayya mallam musa ka bani minti kadan mana muna zuwa aunty maryam son Allah a bashi abinci.

Kamo hannun ladidi yayi suka haura sama suna shiga daki ya rungume ta yace ladidi na ... nasan ban kyauta miki ba hakan yasa naji ban canceki ba. Shin ko zaki iya duba girman Allah ki yafe min? Makalewa tayi a jikinsa tace dama can ni ban rike ka ba na yafe ma duniya da lahira.

Yace ladidi kinga a sanadin mu da kuma son da bokan nan yake miki yasa ya gano gaskiya sai nake ganin bamu kyauta masa ba idan har muka barshi ya tafi bai sameki ba. Ladidi tace me kake nufi? Yace idan har bazai sameki ba me zai hana na sakeki ki auresa ? Kinga muma sai muyi irinta ansar yadda suka dinga bawa muhajirun matansu kuma sai na bashi aiki a a karkashina karki damu baza ku bar gidannan ba muna tare kinga dama na siya gidan makotan nan namu sai ku zauna a ciki ko ya kika ce? 

Tace yanzu kenan zan zama ba matar ka ba? Yace ba dole ladidi ni zan zauna dake in baki yarda ba amma bakaga yardar ki shi zaisa mu zaunar da musa tare da mu kinga bazai koma ruwa ba kuma Allah zai bamu lada. Ki duba zuciyar ki akwai ko da dogon sonsa ne idan ma babu kina tunanin zaki soshi?  Murmushi tayi yayi dariya yace aiho wato dama kina crushing aure nane ya rike ki ko? A hankali ta daga kai yaja Mata hanci yace haba mu didi ba ko kunya?

Kuma kike narke min a jiki a sai kisa na fasa AI toh nide yanzu bazan yarda ki tafi ace kina tuno kusantar mu ta karshe ba kin bani dama na gyara? Ta tureshi tace jimin kai in nayi ciki fa ta ya kuma za'ayi sakin ? Fuskar yara yayi Mata yace toh zan samu kiss daya?

Shiru tayi ya like ta gini ya sumbace ta na lokaci mai tsayi kamar bazaiyi numfashi ba ya rungumeta kam ya sumbaci goshinta suna murmushi suna hawaye. Yace bye my ladidi saduwa ta gari yana fadin haka ya raba jikinsu yace toh kinsan de mai hakan yake nufi ko daga kai tayi yace na ..... sai yayi shiru ya kasa karashewa Dan gabi yake ya kaskantata yace na warware iriyar auren mu guda daya ladidi.

Rugowa tayi da gudu zata rungumeshi tana kuka tace kin manta me nace ne bai halarta ba abinda zakiyi. Fadawa gado tayi ta fashe da kuka shima ya zauna a kasa yayi tagumi Anya zai iya? Kawai abinda ya gani a idon musa yasa zai rabu da ladidi Dan ko tsananin kishi ya gani lokacin da ya kwanta a cinyarta .

Ga kalama da musan ya furta sanda yake shirin tafiya kar shedan yafi karfinsa ya tsoma kanshi a ruwa. A hankali ya fito ya karaso wajensu kowa yayi jungum jungum luba kamar kulya ta makale a lungun kujera ya kalli musa dake zaune yana tattaba yaysunsa da alamu istigfari yake yi yace masa Dan uwa musa kaje ka gyara ayyukanka la shirya ko? Daga ladidi ta gama idda za'a daura muku aure nine ma waliyinta.

Kowa kallonsa yayi a tsorace luba ta Mike da sauri taja hannunsa suka shige dakin da ladidin take tace masa uncle me kakeyi haka ya zaka saki aunty ladidi lokacin da aka gano batada laifi? Yace lubabatu sanda muka tattauna AI bayanin yadda sukayi da ladidi tayi Mata. Kamar zaucacciya taje gefen ladidi ta zauna kallonta kawai take sai ta rigumota ta soma kuka ba abinda ke Mata ciwo sai yadda basu Saba da ladidi ba kamar yadda ta Saba da sauran matansa.

Tace aunty ladidina tanzi da gaske tafiya zakiyi waiyo ni lubabatu Dan Allah karki ba barni kice kin fasa. Girgiza kai ladidi tayi tace kiyi hakuri lubabatu in da rabi zamu sake zama tare kuma yanzu ma ba tafiya zanyi ba nan nan makota ne gidan da zamu zauna. Girgiza kai luba take tana fadin amma AI mijin mu ba daya ba Dan Allah ni muci gaba da zama ko fada ne munayi kullum karki barni dannalkah wallahi bazanyi dadin rayuwa babu ke ba😭😭

Yake ladidi tayi tana goge kwalla tace kanwata ki dena kuka kinji karki manta fa ba ke daya bane a jikinki kuma ai ga uncle aliyun ki ko? Karki damu time table ma zamuyi yau in an yini a gidanku gobe a gidan mu zaku yini kuma kinga yanzu ma muna tare tunda anan zanyi idda kamar yadda sunna ta nuna mana kinji ? Toh luba tace suka fito su uku suna murmushi. Su aunty maryam da suka koma yan kallo gashi sun tuna komai da ya faru ras suka........

😭😭😭 GASKIYA BAN TABA RUBUTA CHAPTER YA TSIMANI HAR YA SANI SHARAR KWALLA BA SAI WANNAN... WAI SHIN KUMA YA TSIMAKU KO NI DAYA CE? KU FADA MIN A COMMENT SECTION 🤧 SANNAN KARKU MANTA KUYI VOTING TARE DA SHARING. INA KAUNARKU LODI LODI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

16th July,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now