CHAPTER 18

3.3K 246 44
                                    

AHALI NA DA MASOYA LUBA NA WATTPAD WANNAN PAGE DIN NAKUNE DUK WANDA YAYI KOKARIN YI MUKU KEACE KU HADASHI DA YAN SANDA😉

ALIYU'S POV.

Ko da nayi sallar asuba dawowa nayi na samu ladidi na sallah Dan haka na koma na kwanta abina. Inaji ta kwanta a baya na tana me sakale hannunta ta ciki na kamawa nayi na rike a haka mukayi bacci... wayata da aka Kira ya tashe ni wai aunty maryam ce ta aiko mana abinci....

Lokaci na duba naga 8 da rabi ma ta wuce Dan haka na fito naje na karbo ina shigowa naji kara a  kitchen Wanda nasan tabbas ba ladidi bace danko ladidi tana bacci lekawa nayi naga fara ce tafi ladidi haske da siririntaka nasan ba ko wa bace sai luba amma abinda yadan mota ni shine kayan dake jikinta.

Tanaso ta ballowa ladidi jagwal danni ka ida ta idan na auri mace ranan farko bazan miki komai ba saboda kidan Saba kar a hada miki zafi bibbiyu sannan kar ma ki dauka na aureni ne Dan wannan Dan haka inde bawai naga alamun kema kinaso ba toh ranan farko kinyi escape saboda nasan yadda ake tsinka musu gaba.

Gashinta dake tsefe bata daure bane idona ya fada akai rabon da na ganta babu lillibi tun ranar da aka kamamu na ganta da Dan kamfai daga ranan da kaya me mutunci nake ganinta harda hula.... sanda ta soma girma kuwa harda hijab.

Gashinta ya kara cika da tsayi Dan yanzu yakai tsayin wajen bra strap. Amma fa ghar tanzi baiyi baki ba kuma ni nafison shi a haka... dungure kaina nayi ina cewa kaji shirme yarinya ma ke damunta da tayi wayo zata ce bataso dama nima ba sonta nake ba Dan ci ne da ita kamar gara amma bata kiba. Cikinnan kamar faranti... tunowa nayi da iskancin sa tayi min jiya aiko dama na daure guntun karkashin hiya na ajiye Dan na Rama... daukowa nayi naje na dauko flask din Dana ajiye bakin kofa na ajiye kan centre table na parlour fitowa tayi bakinta a cike amma a haka tana kokarin tura wani cake.

Tana ganina ta shige bayan labule da alamu taji kunyar yadda na ganta ne bude bayan labulen nayi tana shirin kutsiran doughnut haka kawai naji nima inason ci Dan haka ina Mata wani murmushin mugunta Dan nasan me zanyi na dauki daya.... kanta yana kasa tayi tsimu tsimu kamar kulya da ruwa yayi wa duka amma da shike akan abinci ne da sauri ta dago tana turo baki matsa Mata karkashin nayi kuma da alamu ta wanke gashin lakatowa tayi ta gani kuma gashi na dauka Mata doughnut biyoni tayi zata kwace bayan tayi min raki cewa na bata Mata gashi.

Ladidi ce ta fito ni daga nan na nuna Mata abincin na shige ciki danko luba ta tsokalo min haja.... jin shiri ladidi bata dawo ba gashi a matse nake yasa na fito da alamu surutun nan na tsiya luba ke Mata. Dauketa nayi ina fadin in ta biye wa luba hira bazai kare ba tazo na bata wani labari aiko muna shiga daki na canja salon labarin.....

AUNTY MARYAM'S POV

Tun jiya da daddare aka nemi su luba aka rasa an Kira wayar su duka uku amma a kashe sarai nasan bazai wuce gidan aliyu suka tafi ba dukda na hanasu Dan haka na jira su dawo bayan siyan bakin amma shiru har 12 wayar aliyu zan Kira na tuna yayi aure yanzu bai dace na kirasa ba.

Samir na kira nan yake tabbatar min AI shi ya kaisu ma amma a dawowa bai gansu ba ya dauka sun dawo da wuri ne. Nace masa babu matsala toh sannan na kashe wayar bazan nemosu ba su da kansu zasu dawo su sameni.

Washe gari ma aika akai abincin su Aliyu ina tsammanin ko zasu biyo shi amma shiru... nidai na baza ido naga sanda zasu dawo in basu dawo Dan Allah ba AI sa dawo Dan Kayan su.

LUBA'S POV

bayan na shiga daki na samu mama ta shi nana muka make Dan itace sarki bacci kuma munada style din tashin ta tare zamu daga hannu muka balance sannan mu lafta Mata duka. Wanka sukayi mukaje kitchen abincin da ladidi ta ajiye muka dibo mukayi shagali abin mu.

Shiru basu fito ba har azhar ta kusa kuma inason daukar liffaya ta... knocking nayi naji shiru Dana gaji kawai na shigewata. Cikin bargo na gansu suna murkususu take suka dago suna harbo min wata kallo nikam tabe baki nayi na bude drower aiko naga liffaya ta. Juyawa nayi zan fice uncle aliyu yace ke luba kanki daya kuwa? Ya zaki tsirmo dakin mutane babu sallama? Tabe baki nayi nace da farko de nayi knocking har na gaji na biyu kuma wata tsiyar kuke da kake haki kamar kayi dambe da zaki?

Ranshi ne ya baci sosai amma dinshi kawai ke fadin haka yace abinda kikeso na miki sanda kike karama muke ko zaki jona mu ne? AI da gudu na fita danko an Dan bani katin haske akan abun kuma ba'aso ko maganarta anayi rashin kunya ne inji ummi sannan masu aure keyi. AI ko kirjina kamar zai fado sanda na isa wajen su nana dan aunty maryam tace in mutum yaje yayi ko maganar abin ne mutuwa zaiyi cab bab shirya mutuwa ba da din ma yarinta ke damuna.

Hanya muka kama har gida su nana na fadin madam kode uncle aliyu ya biyoki da wuka ne. Irin wannan gumi da kike haka? Kasa cewa komai ma nayi.... me napep ne ya nemi ya kawo mana shirme wai kudin da muka bashi yayi kadan Dan rainin hankali dari dari ake kaiwa mu uku mun bashi dari biyar zai mana hauka aiko mu uku muka dunkule hannu yadda super heroes na cartoon keyi mukace ko yabar kofar gidan mu ko mu canja masa halitta.

Hmm ashe Dan daba ne ba kawai mutuminka ya sauko ba man kace me ya zaro wuka... take cikin su nana ya duri ruwa da gudu suka shige gida nima na tsure amma Nasan idan ban saita shi ba zai iya dawowa Dan nasan halin yan shaye shaye.

Hade fuska nayi ya kasa gane meke raina Dan baiga alamun tsoro a idona ba sai hargagi yake yayinda cikina har kugi takeyi Dan tsoro ina nazarin barkonon tsohuwa wato tiya gas da almajiri ya koya min jiya bayan mun cashe. Toh na hada gwanin farko amma bansan tayi daidai koko da matsala ba. Kut!! Na hadiya yawu nayi shahada kawai zaro na fasa mai a fuska sannan na warce woman bayan na rushe hanci na da liffaya ta.

Yankar sa nayi da wukar nace kai Dan mahaukaciya nima nan da kake gani na dabancin nan Yinsa nake, yasin ko ta anguwar na ka sake bi saina zaro yayan hanjin ka na wulla masa wukarsa na gudu. Tun daga bakin gate na fara tari Dan duk dabarata na shaki gas din kawai de banason ya gane ne ya kawomin wargi aiko abinda ban sani ba shine ya mugun tsorata da yaga tiya gas din bata min komai ba gashi akwai yuwuwar idonsa ta Sami matsala.

Ina shigowa su aunty maryam suna fitowa a haukace Dan yadda su nana suka fada Mata Dan daba ne har wuka gareshi ta tsorata. Ganin na shigo a jigace yasa akayi ciki dani nasha su ruwa bayan tari da hawayen da nake ya lafa kawai na fara dariya. Tsayawa kallona sukayi waiko kan da kwalabe ne?

Nan na basu labarin yadda akayi ina dariya aunty maryam tayi ta fada wai na dena fada da maza sannan uban wa yace na kiyi hada barkonon tsohuwa kuma me zanyi dashi. Tsilli tsilli nayi daidai lokacin wayar aunty maryam tayi ruri dagawa tayi tana fadin ango kasha kamshi take naji wani kullu a cikina jin yadda yake daga murya bai gama ba aunty maryam ta kashe wayar tare da sambodomin wani kallo.....😳

TOH ANAN ZAN BARKU KUYI MANAGE DA WANNAN. KAR KU MANTA KU SAMBADO MIN COMMENT DAN NAJI DADIN BAKU UPDATE DA WURWURI.  YAN WATTPAD KAR A MANTA DA VOTE FA! INA YINKU KAMR BA GOBE.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

21st June,2020.

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now