CHAPTER 27

3.1K 241 73
                                    

Da sauri ta hade rai tana shirin yin kuka ya janyota jikinsa yace lubcy me kuma akayi? Tace nide gsky banaso.... yace bakyason me? Tace banason nayi ciki yanzu gashi har yanzu wani bari na zuciyata bata aminta muna da aure ba.
Ajiyan zuciya yayi yace luba in tambayeki..... shiru tayi yace kintaba ji ko gani nayi ko samun labari ni mazinaci ne?  Girgiza kai tayi yace wallahi luba tsoron Allah da naji ban lalata ki ba yasa ya bani ke ta halali na dama manzon Allah ya fada cewa duk abi da Allah yayi bawa zai samu toh zai samu saide rashin hakuri yasa ya Samu ta haram.

Ki yarda dani ni mijinki ne ko da kuwa duniya zata tashi luba tun kina 10yrs aka daura mana aure rananda kikace kina kan bakanki. Tunda aka yi min kazafi ban sake hada jikina da naki ba sai ranan Har mukayi selfie na sumbaci kumatun ki Kin tuna ko ? Har aka siya miki tukun kayan sawa da na wasa akace birthday gift ne? Da ana saya miki kaya me yawan wannan ne?  Kiyi nazari mana gizo na saka a wajen.

Rungumeshi tayi tana kuka🥺😭 na yarda dakai uncle Ali kaidin miji na ne ba shakku. Shafa kanta yayi suka zauna yace yauwa matar arziki janyo wayar sa yayi suka soma kallon hotunan da sukayi lokacin da aka daura auren sunata dariyar kamannin luba sanda take kwaila.

Can tace kai gaskiya uncle aliyos nayi farin ciki da Allah ya bani kyautar ka amatsayin miji kanada kasa kuren ka a matsayin ka na Dan Adam amma Allah ya gani Kaine gwarzo na saide Abu daya ke hadani dakai bakamin da saukin in ka rikoni.

Dariya ya fashe dashi harda faduwa yace kai luba bakida dama ki fito kanki tsaye ki fada min dama can abinda ke ranki kenan saboda lokaci yayi toh nima ban manta ba zo muje.

Gudu tasa tana wallahi Allah ni ba da wata niya na fada ba na shiga uku ya haiyu ya kaiyum ka cece ni.... baki shi  ke yanka wuya. Har ta bayan gidan suka fita yace toh shikenan tsaya gudunnan ya isa yanzu de tsaya na miki hoto. Style ta fara masa ya harba mata hoto......

Ashe wayo yake Mata sauran flash yake kunnawa yana kashewa bata ankare ba ya daga ta sama yayi cikin gida

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Ashe wayo yake Mata sauran flash yake kunnawa yana kashewa bata ankare ba ya daga ta sama yayi cikin gida. Da ita

Da yamma lis su aunty maryam suka dawo gida luba ta soma kwalawa Kira tace au kaini da shirme ashe tana gidan kawunta Ali. Driver nr ya wuce da ladidi yayinda aunty maryam ke nazarin nemawa yaran nata admission kamin su samu mijin aure.

Luba da aliyos suna gasar magana me hikima wadda kullum sukeyi... kowa zai wasa kwakwalwa ne ya kawo magana me hikima Wanda nashi yafi hikima shi yaci.

NOTE:SHAWARACE NAKESO NA BAWA MASOYA NA TA WANNAN SIGA DAN HAKA A DAUKA KUMA A RIKE.

Luba tace JIRGIN RUWA BAYA NITSEWA SANADIN TEKUN DAKE TABASA, A AH YANA NITSEWA NE YAYINDA RUWA YA SHIGA CIKINSA DAN HAKA KAIMA KADA KA BARI MAGANAN MUTANE TA SHIGA ZUCIYAR KA BALLE SUSA KA NITSE KA DAWO KASA DASU.

Jinjina kai aliyu yayi yace wow lubata ashe de Kan yana ja toh ga nawa ki saurara KADA KI SAYAR DA MUTUNCINKI DOMIN KI SIYO SUNA DA KUMA DAUKAKA. Shiru dukkansu sukayi tace aliyos Dina yau ka cinye ni danko dayawan mata sun fada wannan musamman yan Mata mutuncin su a bola sude indai za'a sansu a duniya toh shikenan sai su tattare kayansu daga gaban annabi. Suyi watsi da dokokin Allah sai daga baya lokacin da duniya kolin koli dasu tayi musu tofin Allah tsine su dawo suna kaicona kaicona. Inda za'ayi magana sai suce lokacin su ne abarsu suci duniya da tsinke daga baya zasu tuba sai kace sunyi signing kwagila da Allah cewa bazai dau ransu suna zunubin ba.

Yace haka yake Allah ya mana tsari da shaidan amma ke kikayi winning bani ba domin yanzu mahassada ta ko ina nema suke su danne ka da sunga kayi motsi zasu kawo ma farmaki balle ka Mike ai sai buzunka. In suka dinga jefanka da batanci da izgili saide ka bari Allah yayi muku hisabi. Wani fa makocinka ne amma ko gani yayi ka wanke tsohuwar riganka tayi fess fiye da baya. Toh sai ya cije yatsa ina ga in yaga kayi sabon dinki ko an wuce da kaza gidanka.

Inkai talaka ne yace Allah yasa taki dahuwa ko Allah yasa a Koreka gurin aiki ko kasuwa ta baci ma shide yadda bazaiyi dadi ba kaima karkaji inma me kudi ne kai ya dinga yadawa kudin haram ne, sata ce, ludin kwaya ce haka de za'ayita yi har sai randa ka bakunci kasa shiyasa dole ne mu toshe kunne mu rufe ido indai munsan ba sabawa Allah muke ba toh kar mu fasa abinda muka fara.

Tace toh yanzu a takaice de kowa yaci Dan haka dama ka'ida Wanda ya fadi shi zaiyi girki kuma ya sumbaci Wanda yayi nasara toh tunda dukanmu munyi nasara sai muje muyi girki tare sannan ka sumbace ni nima in maka.
Cikin kwaikwayon muryanta yace "ka sumbace ni nima in maka." Sai anjima in anyi magana tace bataso da wani idonta a wajen.

Girki sukayi sunata hirar su yana tsokanarta tana aliyos bana so yace nikam inajin dadin sunan nan ko wa ya bani shi tace wata fan dinmu ce sister Aisha Ahmad Dan lami. Yace aiko ta kyauta da gudun mawa Allah ya kara mana masoya nida luba ta. Tace ameen lokacin ta gama jera abincin Dan yau tsakiyar parlour zasuci ladidi ta rantabo sallama.

(😂😂😂😂 yanzu haka nasan o o da o o ji ake kamar a ciji yatsa Dan bakin ciki ladidi ta bata show..... su uhm uhm harda cewa yar iska ba?.... toh nide kar a hada dani nayi nan🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️)

Wani Abu ne ya tokare musu zuciya dukansu biyu tana bin aliyu da kallo tace mijin kace min kayi tafiya murmushi yayi yace sosai ma AI kusan kullum a hanya muke daga can zuwa can dazu da yamma ma na sauko bakiji gajiya ba amma tafiya tayi dadi abin mema ya samu.

Murmushi tayi dukda hankalinta be gama kwanciya ba Dan ta tsorata da yadda luba ta murje ta murmure da shike da siririya ce sosai amma yanzu ta dawo yar daidai da ita. Ga tayi haske sosai harda kumatu. Ladidi tace oh ke kuma irin wannan kiba fatan baki cinye abincin gidan ba ita de luba shiru tayi jiki a sanyaye ta zuba abincin ta Mike zata shiga kitchen ladidi tace da da kika kawo plate daya tare dashi zakuci? Saita bude baki zatayi magana sai ya koma Dan kuka dake shirin kwace Mata.

Cikin halin ko in kula aliyu yace a ah ni daya zanci a plate din ladidi tace toh AI cokali biyu nake gani yace kin manta mutuniyar taki batamin kadan ne ai da ta zubamin nawa sai ta cinye guntun a flask din ba tare da ta juye ba yanzu ma kila ke zata samo ma kwano ko luba? Daga kai tayi... Ladidi tac e na dauka dazu ka dawo kuma har kunada tsafin cin abinci yace nikam kina zargin wani Abu ne? Tace ba ko daya.

Fashewa da kuka luba tayi ladidi tace subhanallah me aka miki yarnan? fatan de ba fasa zama kikayi a gidannan zaki koma gida ba? Aliyu ne yace yo kinsata a gaba da tuhuma ga yunwa na kwakularta saboda aikin da tayi dazu kice bazatayi kuka ba? Wani dam ! Ladidi taji ta zauna ba tare da ta shirya ba tace aiki kuma? Yace bakiga gidan naki tas ba?
Mikewa luba tayi ta shige daki gaskiya an gama da ita yanzu fa kenan bazata kara zama a cinyarsa suci abinci ba? Kuma bazasu sake nunawa juna kauna a baiyane ba? Na shiga uku na!

AYI MANAGE DA WANNAN. INA GODIYA DA KAUNARKU GARENI ALLAH YA BARMU TARE MASOYA NA ACI GABA DA WATSO COMMENTS DA SHARING TARE DA VOTING. NI KUMA ZAN CIGABA DA BAKU UPDATE.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

2nd July,2020

YARINYAR CE TAYI MIN FYADEWhere stories live. Discover now