EPISODE_1

453 21 2
                                    

💀💀💀
*KOFAR AJALI*
'''[when in no way out]'''
💀💀💀

_________________________

*Written*
Abdul Alhaji musa 10k
*phone no:*
+2349077974042
_________________________

*🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

*In the name of Allah, the most gracious and the most merciful, may Allah sustain me with courage and comfort from the starting point to the last chapter*

*FREE BOOK*💯✅
*EPISODE 0⃣1⃣*

Karar kwankwasa kofane ke tashi,sa'annan wata siririyar murya ta soma biyo baya.
"Brother!! Brother!!,Katashi daga barcin nan,wallahi zamu makara school indan baka tashi daga wannan baccin naka ba,kuma kasani bana jure bulalar madam Fati"
Haka wannan Mai kwankwasa kofar keta nanatawa....
Baya murya tayi shiru kuwa sai karan *alarm* 🔔 ta soma tashi...so noisy.

" *Ohhh*!! wayyo ni,wai wacce iri makwabtane way'annan duk sunbi sun dami mutum awannan sanyi safiyar...."
......Karashe maganar yayi da tsaki

Cikin fushi ya d'ago daga kwanciyar da yake....sa'annan ya Yaye barkon dake kan kugunsa hade da yunkurawa ya wuce toilet,nan ya watsa ruwa sa'annan yayi brush....
Bai wani bata lokaci ba ya nufi hanyar fita,yayinda ya daura *tawal* a kugunsa,Cikin sanyin jiki da kwanciyar hankali yake taku har ya kaiga kofar yasa hannu ya bude ta,ganin kansa cikin uwar dakin ne yasakashi fisge wannan tawal dake kugunsa yayi jifa da ita cen gefe,But then yayi kara Aaaa!! hade da rugawa kan tawal din....da zuwansa gurin ya dauko cikin sauri ya maida a kugunsa.

"Azahirance banga komi ba"

"What the heck are you doing here,how did you get in *Muzaffar* ?".
Abinda ya fara fitowa daga bakin wannan santalelen saurayin kenan,mai kakkaurar gira da mulmulellen link ga kuma manyan idanu wacce take fara tas gashin kansa ko baki ne sid'ik

#Muzzaffar dai ya kasance Zaune yake a bakin katifa yayinda yake rike da *Coffee cup* a hannu....

"Oh actually I met your sister downstairs,ita ta sanar dani cewa kana ciki....."
Haka muzzafar ya basa ansa shiko yayi furucin" *Oh God* damn it"

"So mayya hana ka jirani a downstairs din?"

"Came on ai ba laifi danna shigo dakin ka na zauna Sabida ni friend nake,but I'm not sure banga komi ba"
Hakan ya mayar masa da martani yayinda ya karashe maganar nasa da dariya hade da kyakyatawa.

Dajiyo haka kuwa yasa hannu ya dauko filo,ya bugawa muzzaffar aka......

Haka dai muzzaffar yayi ta zuba yayin da wannan kyakyawan saurayi ke kokarin canza kaya,haka zalika kan Danny teble....yayin da yake karin kumallo,Mituna talatin ne ta dauke sa hakan ta sanadiyar saurin da yake,bayan ya kammala komi suka yunkura suka nufi hanyar fita,Bayyana sukayi a farfajiyar gidan inda ya kasance yayi shiga ta kananun kaya,sa'anan hannun sa rataye da wata yar jaka....taku suke ciki salon burgewa inda muzzaffar ke cewa.

"Kamata yayi ace ka godemin,bawai ka cikani da korafi ba, domin kuwa ni nayi su mufyda suka zauna a wajen if not da dukkannin su sai sunga halin da kake ciki"

"You fool"
Haka saurayin nan ya furta yayinda fuskarsa ke cike da annashuwa....
Fashewa sukayi da dariya dukkan ninsu biyu sa'annan suka cigaba da firar su har saida suka kai wajen wata gabjejiyar mota,shigewa ciki sukayi.....
Da shigarsu ko wata dake zaune cikin wannan motan a kujerar baya tace dasu......

KOFAR AJALI 2021Where stories live. Discover now