CHAPTER 2

165 10 0
                                    

Ni da siyama muna tafiya zamuje makaranta Muna ta labari,Kamar kullum dai itace ke Rabin surutun,Nima inayi Amma surutun ta yafi karfin nawa Dan itafa Bata gajiya,and ita she needs attention sosai in ma Bata samu ba fushi takeyi,tafe muke Ina Allah Allah muzo wurin da na ganshi jiya,hankalina ya tafi chan Ina tunanin ya ban ganshi a wurin ba,haka muka wuce kofar gidan inata sa ke sa ke a raina ga haushi ya isheni,siyama ce tadawo dani daga tunanin da nakeyi tana cewa ke Yaya Asiya Sai ayita Miki magana kiyi shiru hakuri na bata,mun Isa makaranta akan lokaci,ni Ina jss 3 sanawiyya, siyama na aji 6,kowa ya nufi ajinsu,a islamiyya kawata daya ce sunan ta fatima,saboda yawancin Yan ajinmu matan aure ne,bamu fi mu biyar bane Yaran ajin,hakan ya sa min Kara Zama matured Kuma Muna samun karatu sosai ba wasa.
    Lokacin tashi yayi min kamo hanyan gida nida siyama,saidai yanzu siyama ta lura akwai abinda nake son ingani a daidai wurin nan,haka yasa ta tambayeni ko menene nakeso ingani,nace Mata Babu komai badan nayi convincing dinta ba tayarda,haka muka wuce inata Jin haushi ban ganshi ba,gashi Kuma Thursday and friday babu islamiyya har Sai Saturday.Ranan Thursday munyi waya da baba yace zaidawo                Friday,murna mukeyi sosai saboda it's been long baba baya nan,dama Thursdays we are always at home da rana,lokacin muke samu muyi dan abubuwan mu a gida,Ina son painting,reading novels da Kuma girki,haka kusan ko wani alhamis da jumma yake kasan cewa,wannan alhamis din Sai nace umma tabarni in girka mana dinner,na girka tuwon semovita miyan kubewa,Yaya khalifa nafara zuba ma yaci yanata Santi,nikam murna ya isheni a dole na iya girki,siyama dai ance beyi Dadi ba ko ita zata iya kalanshi,well daga Baya ta fada gaskiya tace yayi dadi,mama ma taga kokarina duk da dai inayi tana fada min wasu abubuwan,na iya girki Amma rashin practice ne,mama tace daga yanzu zata dinga Bari na inayi time to time,hakan zaisa in kware.haka Thursday ya Kare,duk da I have been busy but inata tunanin shi araina Ina fatan Allah yasa in Kara ganinshi.
Friday muntashi nayi Shirin makaranta,nayi kyau Kamar kullum,Raina fari saboda murnan baba zaidawo yau nashirya natafi makaranta,yau ma Kamar kullum Yaya khalifa ya kaimu nida siyama,Yana sauke mu Sai ga mariya harda gaishe da Yayah shikam ya amsa ta,nan dai muka shiga schoo tare  da ita,mariya Yar science class ce ss3 Amma ko magana be taba hadani da ita ba,Amma yau saboda taga Yaya na Sai tayita manne min,su hafsa da hadiza abun mamaki yayita basu,Saida mukaje aji suke tambaya na Wai lafiya yau mukaga mariya ta Zama kawarki Kuma,dariya nafara musu saboda yanda suka hada Baki a tare suna tambaya ta,nan nace musu ku maida wukar ai Yaya khalifa tagani shiyasa ta ke shige min,dariya mukayi duka,sukace gaskiya bamu yarda ba mariya ta cika iyayi,gashi Yaya khalifa babu ruwanshi min fi so ya samu gentle Kamar sa.
   Mun dawo gida min taradda mama tana ta gyare gyaren Shirin dawowan baba,nan na tayata ta karasa girki sannan naje na watsa ruwa,na fito na saka Riga da skirt din lace nayi kyau Abu na,itama siyama ansha kyau Yar autar baba yau Baki yaki rufewa Dan murna,Yaya khalifa Kuma yatafi sallar jummaa,mama ma nan ta kammala komai tayi kyau itama abinta Muna jiran isowar baba.Mun zauna falo munata fira mukaji horn din mota da gudu muka tashi muna zuwa mukaga Ashe ba baba bane Yaya batool ce tazo itama,yau dai gidan dadi Kan kace me fira ya Kara yawa kowa a murna Dan ta kwana biyu batazo ba itama,wuraren laasar baba ya iso yayi murna sosai ganin iyalanshi cikin koshin lafiya,kamar kullum baba baya tsayawa Yana dawowa yake ba kowa tsarabanshi,siyama ya Fara dakko ma tsarabanta, iPad ce sabuwa a kwalinta,nikuma waya ce aka siya min murna nakeyi sosai,mama Kuma atampa ce da lace,ga wani jaka da purse irin ta hajjajun nan masu tsada,Yaya batool ma baa barta a baya ba,baba ya siya Mata agogo,Yaya khalifa Kuma earpods da smartwatch ne baba ya bashi yace adinga Jin karatu ba wakoki ba,dariya duk mukayi,daki natafi inata murnan wayata harda sim Abba ya siya min.yaya khalifa na ba yayi min setting komai sannan yayi min downloading apps yabani,nan da nan nakira su hafsa da hadiza dama su already sunada waya.
   Saturday mun shirya islamiyya,haka yau ma muka wuce ban gansa ba,sunday kam bansa tunanin ganin shi ba hakan kuwa akayi zuwa da komawa babu shi,hakan yasa na cire Rai da ganin shi,na maida kaina ga harkoki na Kamar yanda na Saba,ga jarabawan mock munyi min Gama,waec da neco ake Shirin Yi yanzu munata shiri.
   Yau Friday,hafsa da hadiza sunzo gidan mu,fira mukeyi a daki na tare da su har firan samari yatashi,kowa nata bada labarin nashi nikam Dariya naketa binsu dashi, mostly samarin su a online suka hadu,nafada musu Ni Banda ko daya,dariya suka hau min sukace kowa yanada shi saidai ince dai bana kula su,hafsa harda amsan wayata ta Fara duba min messages tace gasunan suna Miki magana kidunga amsa su,a hakan har tayita replying messages din da aka turomin ban amsa ba,har dadin replying chats din nawa takeyi inata dariya,Ashe aiki taje duk ta jawomin ban sani ba,hadiza ma firan mukeyi tana ban labarin saurayinta bello,a layin su yake,tana ban labarin Ina tunanin na hanyar islamiyya,soyayyar tasu gwanin shaawa gashi har iyayen su sun sani,
saida su hafsa suka tafi gida na amsa wayata Naga duk ga messages din mutane,abinka da introvert na rasa me zanyi Sai naji chat din da Dadi Ashe,nayita amsa duk masu min magana,akwana atashi kam Abu ya Zama jikina,Banda abinyi Sai in dau wayata inta danne danne after school,duk da hakan bana taba Bari ya Hana Ni concentrating akan karatuna Kuma mama tana kula tana min waazi akan mahimmancin karatuna.
  Yaya khalifa nata neman aiki abin shiru,Dan kasar ta lalace,hakan yasa yace Bari ya gwada applying short service,dama tun farko Yana so yazama pilot Sai Kuma Bai samu hakan ba,yanzu Sai yace Bari ya gwada Airforce ya gani,hakan kuwa akayi Dan Yaya khalifa yayi applying  short service Kuma yasamu yatafi,kullum Muna kewarshi a gida saidai Kuma badaman mukirashi,yawanci siyama ta fi shiri da Yaya khalifa,Dan Ni in Ina chan daki toh siyama na falo da Yaya khalifa suna fira,tafiyan Yaya khalifa yasa siyama ta Dan rage walwala,Sai dai tazo daki wurina,and nikuma ban cika surutu ba a hakan har siyama taja baya da Ni,ban kawo komai a Kaina ba a tunani na kawai dai tasamu wani abin yi ne,duk da mama tana kokarin sauraren matsalolin mu indai akwai Amma itama Kamar Ni ta ke Bata cika surutu ba,duk da ta lura siyama ta rage surutun nata itama Bata sa komai ba a ranta,she just assumed siyama has found something to keep her busy ne.
  Cikin Dan chat Dina da nakeyi a haka na hadu da wani sunan shi abubaka r,Muna fira sosai dashi gashi har mun Fara Zama close,rannan yace Yana so na,ba Dan Ina Jinshi ba a zuciya ta Nima na amsa Masa,haka muketa tafiya,saidai gaskiya nidai banjin shi a zuciya ta kamar yarda nataba ji ma wannan na hanyar islamiyya.Har yau Inna tuna shi inaji inama inama in ganshi ko sau daya ne.

NI DA YAN GIDAN MUDonde viven las historias. Descúbrelo ahora