CHAPTER 16

62 7 0
                                    

Parlor mama tayi Mana girkin dare,tare muka ci abincin gaba daya Amma hankali na Yana Kan Inga tanimu Inga halin da yake ciki.wayyo Yaya khalifa duk yabi yadamu tunani yakeyi ko Dan abinda nagani dazu ke sani tunani,message na tura Masa nace Yaya khalifa Ni fa na amince kayi soyayya da hafsa,tanimu ne beda lafiya na kosa yazo ingansa Inga halin da yake ciki,ya karanta message din yamin reply yace "zamuyi magana".
     Kirar tanimu nagani,na daga yace min Yana kofar gida,Saida na Dan sata kallon mama na Mike ,hijab na sako sannan nadawo falon  nace mama zanga tanimu a waje,cewa tayi adawo lafiya Kar a dade.
  A mota yazo nashiga motar na sameshi duk yayi zurum zurum kaman ya Dade Yana ciwo,da damuwa na zauna Ina tambayan lafiya,meke damunka Haka,Maimakon yayi magana kawai sai ya rungumeni Yana wani irin kuka Mai tsuma zuciya,sosai yake kukan gaba daya hankali na yatashi,bansan sanda Nima kawai nafara kukan ba,tunda nake bantaba ganinshi Yana cikin damuwa ba,ko da Abu ya Bata Mai Rai shi bazaka gani a fuskan shi ba,Sai dai inshi yafada ma da bakinsa,Amma gashi yau harda kuka Haka sosai,nasan lallai wannan ba karamin Abu bane ke damunsa.
   Sai dai Kuma nayi tunanin am supposed to be strong ai kukan shi ya kawomin,hakan yasa na dage na Kori kukan tare da bubbuga Masa bayansa alaman yayi hakuri,Sai a lokacin ya tuna yanayin da muke ciki Bai kamata ba,da sauri Kuma ya sakeni Yana fadin kiyi hakuri nayi abinda Allah baya so,Saida hankalin shi ya kwanta sosai sannan nace toh yanzu kafada min meke faruwa haka,Dan Allah kafada min ko menene.
    Cikin muryar kuka yace Asiya mutuwa zanyi,nakusa mutuwa saura kwanaki kadan in mutu,Ido na cike da kwalla nake kallon sa Ina rike da hannunsa,duk da natsorata da abin da ya fada Amma Sai na matso jarumta nace wace irin magana kake fada,ai dama muma duk mutuwa zamuyi tanimu,kallo na yayi cikin muryar Mai rawa yace Asiya cancer nake da shi,anyi confirming a asibiti Kuma ance ko anyi min magani I have few years to live,inajin tsoro sosai Asiya gashi gaba daya jikina kaman Ana bubbuga min Abu,yanzu kam kuka nakeyi Nima Ina fadin bazaka mutu ba tanimu,in Allah ya yarda maganin zeyi aiki Kuma Zakaji sauki,kuka mukeyi a tare gaba dayan mu,makogwaro na a bushe yake gashi bansan ma me zanyi ba😭😭,kukan kawai dai mukeyi muna sanar da ubangiji.
   Cire abinda ke wuyan sa yayi yace min Kinga abinda nake boyewa,cancer daga hanci shi yasa min muran da naketa fama dashi,daga hanci ya sakko wuya yanzu shi ne yasa wuya na ya ke kumbura gashi Kuma ance in baayi treating fast ba it will affect my entire face Sai Kuma mutuwa,innalillahi wa Inna ilaihi rajiun na fada,meyasa tuntuni baa duba ba har aka Bari ya Kai Haka?tambayan da nayi Masa kenan,Sai Kuma na ba kaina amsa nace nasan kana tunanin zaka damemu ne in ka fada ma mutane ko likita abinda ke damunka kamar yanda ka saba,yakamata kasan ko yaushe akwai ciwo duniya ba ko yaushe bane ake farin ciki,you cannot always make everyone happy,yanda kake sharing happiness da kowa ya kamata bakin cikin in ya sameka ma ka fada mana,Kuma yanada kyau mutum ya dinga sanar ma family dinshi damuwan shi,ba ko yaushe kayita kokarin faranta ma kowa Rai ba alhalin kana da damuwa,boyewa be kamata ba babe.
  Nagane illar yin shirun,su mama Basu taba sanin abin ya Kai Haka ba Kamar yanda kema Baki taba sani ba,Ni kawai Ina ganin Kamar Zan dameku ne Inna fada muku,kuyi hakuri ku yafe min,hannu na sa Masa na kulle Masa Baki,nace kadaina bani hakuri,yanzu babban abinda yakamata shi ne maganin,Allah yace kowani cuta nada magani kuma insha Allah zaka samu sauki tanimu na,ka kwantar da hankalinka duk da nasan hakan Abu ne Mai wuya,Amma kayi kokari,Ina maganan Ina sha re hawayen da ke fuskan sa,shima Sha re min nawa hawayen yakeyi Yana fadin kiyi hakuri Asiya ta,komai zai wuce ,kiyi hakuri na sa Miki damuwan nan,Bata Rai nayi alaman naji haushin maganar daya fada,nace kadaina cemin ka samin damuwa Dan  girman Allah,in bazaka fadamin damuwan ka ba babu amfanin fadamin farin cikin ka,so please kadaina cemin ka samin damuwa,kacigaba da addua da Neman gafarar Allah,kadauka wannan jarabawan Allah,Kuma Allah na jarabta bayinsa da yafi so ne,insha Allahu you will get over this, I love you so much baby.
  Sai da na tabbata hankalinsa ya kwanta sosai sannan na tambayesa ko su mama sun San duk wannan maganan,cemin yayi sun sani,Kuma sannan zaa Fara zuwa asibiti ayi sauran gwaje gwaje sannan chemotherapy,tausayin sa nakeji sosai a zuciya ta,Amma dole in Zama strong,kaman yasan abinda ke zuciya ta yace Kinga yanda Kika Zama strong , da wasan sa Kamar yanda ya Saba boye damuwan sa ya fada,ce Masa nayi Wai ya kakeyi?da sauri ya kalleni yace ya nakeyin mene?nace ya kakeyi ka boye damuwa a fuskan ka bayan akwai damuwan a ranka,cikin dariya yace baiwa ne Allah ya bani,ko kina kishi ne?aah nace Masa,nace toh ko zaka boye ma duniya damuwanka nidai karka boyemin.Duk da bayajin dadi Amma Saida ya tabbata mood Dina yadawo Dan daidai sannan ya barni in tafi,tanimu mutum ne me son Wasa sosai ,cewa yayi inyi Masa alkawarin ba Wanda zai sani,saidai ko mama Amma Kar in fada ma friends Dina saboda bayaso azo anata Masa sannu,in Ana Masa sannu zai Kara karaya sosai cewa nayi nayarda sannan nafita a mota na wuce gida.
Gida na shiga jikina a sanyaye,wurin mama naje na kwanta kan kafarta sannan nafara Bata labarin tanimu,mama taji tsoro sosai sannan tadinga lallashena tana fadin ciwo ba mutuwa bane,siyama ma tana gefe hakurin ta ke bani itama,sallah mama ta tashi zatayi hakan yasa natashi Nima natafi inyi sallah,cin Karo nayi da Yaya khalifa ya Yi alwala zai fito ya wuce masallaci,Yana gani na yace madam make I go pray and come back,we will talk,cewa nayi toh saika dawo kazo kayimin bayani,Kara kallona yayi yace Naga Kuma duk kinyi kuka ne meke faruwa ne,ce Masa nayi nidai je kayi sallah kadawo.

Please vote and comment ooo,motivate me to write

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now